18/08/2021
Kungiyar "Arewa Media Writers" Reshen Jihar Katsina Ta Gabatar Da Ta'aziyya Ga Shugaban Kungiyar Reshen Jihar
Daga Kungiyar "Arewa Media Writers"
Kungiyar Marubutan Arewa a Kafofin Sadarwar Zamani "Arewa Media Writers" reshen jihar Katsina ta gabatar da ta'aziyya ga shugaban Kungiyar reshan jihar Comr Nura Siniya, bisa ga rasuwar abokiyar zaman mahaifiyarshi, wadda Allah yayi mata rasuwa, a ranar juma'ar da ta gabata.
Ziyarar ta'aziyyar ta gudana ne, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban Kungiyar na jihar Comr Ibrahim Bello, inda s**a gabatar da ta'aziyya ga dukkan iyalai da 'yan uwan marigayiyar, amadadin shuwagabanni da membobin Kungiyar na kasa baki daya.
A karshe sakataren tsare tsare na kungiyar Amb. Ibrahim Adam Dan sarauta, shine ya gabatar da addu'a ta musanman a madadin kungiyar, domin nemawa marigayiyar rahamar Ubangiji, inda ya roki Allah ya jikanta da rahama yayi mata sakamako da gidan Aljanna tare da sauran musulmi baki daya.
Rubutawa✍️✍️✍️
Amb. Ibrahim Adam Dan sarauta,
Organising Secretary "Arewa Media Writers" Katsina State Chapter.