23/03/2025
KAWANAKIN RAMADAN RAGUWA SUKEYI.
Abun zai baka mamaki, kamar yau ne muka fara wannan azumin, amma yau gashi cikin iko da amincewar Allah ta'ala har munyi nisa a cikinsa"
Da yawa an fara azumin nan dasu amma baza a kai ƙarshensa dasu ba, wato kai da kake raye har zuwa yau ɗinnan wane kalar ƙoƙari kayi wajen ganin ka kyautata imaninka a cikin wannan watan, ka bawa kanka amsa da kanka"
Ibnu Rajab R.A yace: Haƙiƙa kusan rabin watan nan mai albarka ya shuɗe, yanzu fa watan nan naku raguwa yake yi, ku ƙara yawan aiyukanku, zai zamo babu ku babu shi, domin kowane wata akan sami wani ya biye bayansa, amma shi ramadana taya za ku sami wanda zai biye muku bayansa"?. Ladaa'iful... 262.