06/08/2025
Innahlillahi Wainnah Ilaihirraji'un !!!
Yanzu nake samun rahotan Daren jiya ma lamarin dai babu daɗi waɗan nan miyagun mutane sunyi ta addanci mai muni a gidan shawai dake wajen Tsamiyar Dukumi cikin ƙaramar hukumar Malumfashi.
Daren jiya da misalin karfe 12:30 ƴan ta'adda sun shiga gidan shawai dake kusa da ɗanƙuro, sun kwashi mutane 14 sun kuma kashe wani babban magidanci Dauda Yellow da ya ki ya bisu.
Akwai gidan da sun dauki magidancin tare da diyarshi da kuma matanshi dukka biyu tsohon Head master ne a makarantar unguwar Gambo sunan shi malam tsalha a bara yayi ritaya.
Wasu bayanan kuma daga wasu mazauna garin sunce “Cikin mutane 14 da s**a ɗauka Allah yaba ɗaya nasarar kubutowa ta dawo yanzu kenan sauran mutum 13 ne s**ayi aron gaba dasu zuwa daji.
Sannan mutanen garin na gidan Shawai sun bayyana na miƙa godiyar su ga al,ummar garin Tura, da sune s**ai saurin kawo musu ɗauki, inda s**ai ta musayar wuta da barayin.
Sunce “bacin wannan taimakon ɗauki da mutanan garin Tura s**ai saurin kawo musu da manyan mak**ansu, da ta'addancin da ƴan bindigar zasuyi ma ba asan iyakar shi ba.
Daga| K**ala Bala K**alancy
06| Aug| 2025