
06/09/2025
SADDAM HUSSEIN
Baturen da ya halarci kisan Shugaban Iraki Saddam Hussein (Allah ya jiƙan sa)
Wani ɗan Amurka da ya halarci kisan shugaba Saddam Hussein (rahimahullah) ya bayyana cewa har yanzu yana cikin ruɗani kan abin da ya faru. Yakan tambayi kansa sau da dama: Mece ce fahimtar Musulunci game da mutuwa?
Ya ce: Saddam mutum ne da ya cancanci girmamawa. Lokacin da aka buɗe ƙofar kurkukun sa da ƙarfe 2 na dare agogon GMT, shugaban tawagar da za su kula da kisan ya umurci jami'an tsaron Amurka su fice. Sai ya sanar da Saddam cewa za a kashe shi cikin awa guda.
Amma Saddam bai nuna firgici ba. Ya nemi shinkafa da naman kaza da aka dafa – abincin da ya saba ci da dare. Ya kuma sha kofuna da yawa na ruwan zafi da zuma, abin sha da ya saba tun yana ƙarami.
Bayan cin abincin, an nemi ya je bayan gida amma ya ƙi. Da ƙarfe 2:30, ya yi alwala – ya wanke hannunsa, fuskarsa, da ƙafafunsa – ya zauna gefen gadon ƙarfe yana karanta Alƙur'ani da matarsa ta ba shi kyauta. A wannan lokaci ne aka fara gwajin igiyar rataya da dandalin kisa.
Da ƙarfe 2:45, mutanen asibiti biyu s**a kawo akwati na katako, s**a ajiye kusa da dandalin rataya.
Da ƙarfe 2:50 aka kawo Saddam zuwa ɗakin kisa. Shaidu sun tsaya a gaban bango: alkalai, malamai, wakilan gwamnati, da likita.
Da ƙarfe 3:01 na safe ne aka fara aiwatar da hukuncin, kuma duniya ta kalla ta cikin kyamara. Aka karanta masa hukuncin.
Saddam yana duban dandalin kisa ba tare da wata fargaba ba, yayin da masu ratayarsa s**a rude, wasu suna rawar jiki, wasu kuma sun ɓoye fuskokinsu da masks, suna cikin firgici da tsoro.
Wannan Baturen ya ce:
"Na kusa guduwa daga ɗakin kisa lokacin da na ga Saddam yana murmushi bayan ya furta shahada:
(لا إله إلا الله محمد رسول الله)."
Na ce a raina: Wannan wurin cike yake da bama-bamai? Ko wani tarko aka yi mana? Domin abin mamaki ne mutum ya yi dariya da ƴan sakan kafin a kashe shi.
Da ba a ɗauki bidiyon ba, da duka abokan aikina na sojojin Amurka za su ce na yi ƙarya.