22/04/2025
Da farko za su ce maka ka samu aiki a “International Company”. Idan ka je, sai ka ga kowa a hargitse, ka ga office a birkice ba tsari, ka ga komai ana ta yin nuƙu-nuƙu.
Daga sun karɓi kuɗinka, sai su ce ma ba aiki ba ne, “Multi-Level Marketing” – bi-ma’ana sai ka kawo wani ya saka kuɗi cikin sana’ar za a fara biyanka.
Wadannan mayaudara su na wanke ƙwaƙwalwar matasa su zama k**ar tumakai (herd behaviour). Da zarar ka shiga tsarin, sai ka ga ka kasa fita, saboda sun daure ka da igiyar zato, kullum tunaninka idan ka jawo mutane s**a saka kudi, za ka zama mai arziki. Haka za ka ga matasa sun sha tsohuwar kwat da lakatayin sun kawo kujejjen kanbas sun ƙwama, sun tafi “office” tun safe sai yamma ana koya musu dabarun damfara.
Shin me su ke siyarwa ne? Su na fakewa da siyar da wasu tarkacen abubuwa ne da ba ka taɓa jin sunansu ba, amma a zahiri damfara ce kawai.
Wannan hoton sarkar “Chi-Pendant” ne da Qnet ke siyarwa N600,000. Ita dai wannan sarƙa ba gwal ba ce ko azurfa ko tagulla, amma sai azabar tsada. A ƙaryar su, ita wannan sarƙa tana ƙara ƙarfin jiki da garkuwar jiki da rage kasala.
An ce wa matasa online business ne, amma matasan sun kasa tambayar me yasa ba a ba su damar amfani da internet ko computer? Hatta layin waya ƙwace wa su ke yi saboda kada ka yi magana da wani (bad influence) daga waje, sai dai in wanda za ka janyo su damfara ne.
Ka tambayi kanka tsakani da Allah, waye zai shigo harkar Qnet in ya san tallar wannan sarƙa ko “biodisc” zai yi? A je ma tallar sarƙar ne, shin ina sarƙar take ne kuma waye mai siyan?
Sashe na ɗari huɗu da tara na kundin “Criminal Code Act” ya ce duk wanda ya karbi kuɗi ko kadarar mutum bisa yaudara ko ƙarya ko damfara, to ya aikata lafin da za a ɗaure shi shekara uku a gidan yari. In dai ka yi wa mutum ƙarya ya shiga Qnet, to in ya kai ka ƙara za ka iya shekara uku a gidan yari.
Matasa ku guji yan damfara. Ku k**a sana’a.