29/08/2022
Zuwa ga Maigirma Wazirin Adamawa, Alhaji Atiku Abubakar,
Tare da girmamawa da maraba da zuwa jahar Kano a yinkurinka na kara samun magoya baya domin tunkarar zaben da ke zuwa na 2023. Na kasance mai cike da fatan ku hada kai da Sen. Rabiu Kwankwaso domin yin aiki tare, kuma har gobe ban sauka daga kan wannan tunanin nawa ba tunda dai a siyasar Najeriya komai mai yiwuwa ne. Na san ka fi ni sanin tasirin Kwankwaso a siyasar Najeriya tunda kuwa ko babu komai kasan kun yi takarar neman tikitin jam'iyar APC domin zaben 2015, inda shugaba Buhari ya zo na daya, Kwankwaso ya zo na biyu, Allah Ya taimaki Waziri, kai kuma ka zo na uku. Gaskiyar ita ce ka na bukatar Kwankwaso, shi ma Kwankwaso ya na bukatarka. Kash! Sai dai wadanda ke kewaye da kai musamman wandanda su ke daga arewa ba za su bari alakarka da Kwankwaso ta yi tasiri ba domin yadda su ke jin haushinshi sabo da farinjinin magoyabaya da Allah ya yi mishi fiye da na su. Ina nan, zan ci gaba da addu'ar Allah Ya hada kanku da Kwankwaso kafin zaben 2023.
Haka kuma, na samu labarin cewar zuwanka Kano na da alaka da karbar Malam Shekarau domin dawowa PDP. Toh, shima wannan wani cigabane a wannan takara ta ka, sai dai kada ko da wasa ka yi tunanin Shakarau zai iya yi maka wani tasiri da al'umar Kano ba za su yi maka ba ko babushi domin Shekarau fa ya tsaya zaben shugabankasa a 2011 a tutar ANPP amma kaso 19% na kuri'ar Kano ya samu, kai kuma da ka tsaya zaben 2019 ka samu kaso 21% na kuri'ar da aka kada ta shugabankasa a Kano.
Haka kuma kar mu manta cewar idan ana batun farinjini da magoya baya a Kano, Arewa da Najeriya, ko kusa ba za a hada Rabiu Kwankwaso da Shekarau ba duk kuwa da cewa su na da abubuwa da su ka yi k**a da juna kasancewarsu tsoffin gwamnoni har karo biyu a Kano, tsoffin ministicin Najeriya kuma kowannansu ya yi sanata. Misali, Shekarau ya zama sanata a 2019 da kuri'a 506,271 amma Kwankwaso ya zama sanata da kuri'a 758, 383 a 2015. Wannan kuri'ar ta Kwankwaso ta ma zarta zarta kuri'a 526,310.