13/07/2025
Kotun Minna ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga yarinya mai shekara 16 saboda kisan malama a FUT Minna yayin wani fashi da makami – lokacin tana da shekara 14.
Wata yarinya mai shekara 16 mai suna Joy Afekafe ta samu hukuncin daurin rai da rai bayan kotu ta same ta da laifin kisan kai wanda ake hukunta shi bisa sashe na 221 na dokar hukunta laifuka (Penal Code).
An yanke mata wannan hukunci ne saboda kashe Dr. Mrs Funmilayo Sherifat Adefolalu, malamar jami’a a Jami’ar Fasaha ta Tarayya Minna (FUT Minna), a ranar 28 ga Oktoba, 2023 a gidanta dake Gbaiko, Minna, Jihar Neja.
Mai shari’a Mohammed Adishetu Mohammed na Kotun Babban Birni Minna mai lamba 4 ne ya jagoranci shari’ar, inda ya bayyana cewa masu gabatar da kara sun tabbatar da laifin fashi da makami da kuma kisan kai da gangan a kan Joy.
A cewar Lauya mai gabatar da kara daga ofishin Antoni Janar na jihar Neja, laifuffukan guda biyu – fashi da makami da kisan kai – suna karkashin sashe na 221 da 298 na dokar Penal Code.
Joy Afekafe ta fara aiki a matsayin yar aikin gida ga marigayiya Dr. Adefolalu daga ranar 2 ga Oktoba, 2023, bayan Pastor Ojo Peters daga coci mai suna Voice of Mercy Church a Minna ya gabatar da ita. Wannan coci ce su Joy da mahaifiyarta da marigayiyar ke halarta.
Bayan ta koma gidan, Joy ta fara sata wasu kadarori da kudin kasashen waje, wanda hakan yasa Dr. Adefolalu ta kore ta daga aiki.
Bayan kora, Joy ta hada kai da wasu abokanta guda biyu – DJ Wallex da DJ Smart – domin daukar fansa. A cikin bayaninta ga 'yan sandan SCIID (Sashin bincike na musamman a Neja), Joy ta bayyana yadda abokanta s**a yi wa malamar yankan wuka sau da dama.
Yayin da Dr. Adefolalu ke kokarin kare kanta da tabarma, s**a karbe tabarmar s**a doke kanta da ita, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta. Daga nan s**a kwashe wayoyi biyu, kwamfuta da kudi na waje daga dakinta.
Mai shari’a Mohammed ya bayyana cewa bayan duba hujjoji da shaidu, an tabbatar da cewa Joy da abokanta (wanda s**a gudu har yanzu) su s**a kashe Dr. Adefolalu da gangan.
Sai dai saboda Joy tana da shekara 14 a lokacin kisan, dokar ta haramta hukuncin kisa ga duk wanda bai kai shekara 18 ba a lokacin aikata laifi. Don haka kotun ta yanke mata hukuncin daurin rai da rai a cibiyar gyara halin yara saboda kisan kai, sannan kuma shekara 10 saboda fashi da makami.
Lura: Wannan hukunci na daga cikin matakan hana aikata laifi da kare rayuwar al’umma musamman na masu rauni kamar mata da yara.