09/05/2024
Ke Duniya
Ya yi garkuwa da Abokinsa na kutan, Maikacin Kedco sannan ya yi masa kisan gilla tare da arcewa da motarsa da wayarsa.
Ke Duniya, Allah ka tsare mu, k**ar ba zai aikata ba.ππππ
Sadiq Zubairu ke nan, dan unguwar Hotoron Arewa, mai shekara 35 a duniya, wanda ya hada baki tare da wasu mutane biyu, inda ya yaudari Abokinsa na kutan Bello Bukar Adam mazaunin Zawachiki dan shekara 45 a duniya, zuwa gidansa.ππ.
Bayan yaje gidan nasa da motarsa kirar Toyota Corolla, sai kawai s**a daure shi, sanann ya rinka dukansa da Muciya, ya rika kuma dora masa dutsen Guga akansa har sai da ya ce ga garinku nanππ
Ganin haka tasa ya saka gawarsa cikin bayan motar Marigayin ya tafi can T**in bypass na Hotoro ya jefar da ita.
A sak**akon rahoton rashin ganin Marigayin da yayansa ya kai ofishin yansanda hakan tasa aka fara zurfafa bincike, kuma daga bisani aka samu labarin ganin gawar Marigayin ya she a gefen T**i, aka garzaya da ita Asibiti aka tabbatar da mutuwarsa.
Bayan k**a Sadiq Zubairu ya tabbatar da aikata danyen aikinπ Kuma ya ce abunda ya sashi aikata wannan ta'asa shi ne, ganin ya yaudari Marigayin tare da karbar naira milyan 3 a hannun marigayin da sunan zai samo masa wani aiki, amma da ya fahimci ba zai iya mayar masa da kudin ba, kawai sai ya dauko wadannan mutane yan ina da kisa, s**a yi ta'adin tareππ
Yanzu haka yana komar rundunar yansandan Kano, k**ar yadda kakakin su Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Jama'a Allah ka raba mu da mugun ji da mugun gani, Ka tsare mu da yin mu'ammala da bata gari.