
25/06/2025
Al'ummar Iraniyawa mutane ne masu nagarta da sanin Yakamata -Ronald Trump's
Karon farko Donald Trump, ya yabi Al'ummar Iran da hali na nagarta.
Ɗan jarida ya tambayi Trump: Kana so a samu sauyin gwamnati a Iran?
Trump: "A'a, bana so. Ina fatan komai zai lafa cikin gaggawa. Sauyin gwamnati na haifar da rudani."
"A maimakon haka, muna so mu guje wa rikice-rikice da yawa. Don haka za mu ga yadda abubuwa za su kaya."
"Ka sani, ’yan Iran ’yan kasuwa ne nagari, suna da ƙwarewa sosai wajen kasuwanci. Kuma suna da mai da yawa."
"Ya kamata su kasance lafiya. Ya kamata su samu damar sake gina ƙasarsu kuma su yi abin kirki. Amma ba za su taɓa mallakar makaman nukiliya ba. Amma banda haka, ya kamata su yi abin kirki sosai."