09/02/2023
Allah yana jarrabtarmu saboda ayyukanmu. Muna bukatar gyara da kyautatawa junanmu da kuma son junanmu. Bautar Ubangiji ba wai kawai sallah, azumi, zakkah, hajji da kuma lazumi bane.
Ita bauta ta hada da mu'amalarmu ta yau da kullum da kuma kyautata aiki da kyautatawa juna da mutunta juna da zaman lafiya da mutane da taimako da kawarda kyashi, da cin zarafin mutune, da cutar da mutane da zalumci-kowane iri da makamantansu.
Idan bamu gyaraba, hakika abubuwan da muke gani a wasu kasashen da suke faruwa na azaba da tashin hankali zasu samemu.
Yanzu irin girgizar kasa data faru a Turkey da Syria, ba karamin izna bane garemu.
Mu gyara sai Allah ya gyara mana!
Huzaifa Sani Ilyas