07/06/2025
Kano fa tana da damar cigaba sosai
Daga Dr. Fahad Ibrahim Danladi
Komai da jihar Kano take buƙata ta haɓaka tattalin arziƙinta, an yi ko an kafa ɗanba. Kawai abin da ake buƙata a yanzu shi ne haɗin kan gwamnatin Kano, da wakilan federal a Kano k**ar su Ganduje, Barau da sauransu.
Akwai cargo train, jirgin ƙasa mai ɗauko kwantena daga Lagos zuwa tashar Dala Inland Dry Port Kano, har ya fara kawo kaya amma kaɗan, kuma na ji shiru kwana biyu. Idan su Barau s**a mayar da hankali, hakan na nufin idan na siyo kaya a China ko US, sai na zo Kano sannan za a buɗe container. Mutane dubu nawa ne za su yi arziƙi idan wannan aiki ya ɗauki saiti?
Uwa uba manomanmu. Idanfa kwantena ta zo daga Lagos, ba fa haka za ta koma ba, lodin kayan gona za a yi mata zuwa kudu da ƙasashen waje. Babu maganar kayan miya sun ruɓe a hanya ko wasu marasa mutunci sun ƙona su. Harkar noma za ta yi haɓakar da ba ta taɓa yi ba.
AKK pipeline, bututun gas ne da zai zo har Kano, tuni aikinsa ya yi nisa. Idan wannan aiki ya kammala, gwamnatin jiha ita ma ta shigo wajen kai connection ɗinsa industrial zone, hakan na nufin kamfanoninmu za su farfaɗo, sabbi kuma za su shigo. Dubbunan matasa ne za su samu ayyuka masu tsoka.
Ana titunan mota da jirgin ƙasa a Kano ta yadda masu siyayya za su samu sauƙin zuwa Kano hada-hada. Ita kuma gwamnatin Kano k**ata ya yi a ce ta mayar da hankali wajen tsaftace t**i da zirga-zirga a Kano, ta yadda ƴan kasuwa za su shigo su fita salin alin.
Waɗannan da ma wasu ɗinbun ayyukan na haɓaka tattalin arziƙi ba za su yiwu ba, sai ƴan siyasarmu na Kano sun ajiye baƙar siyasar cibaya da ke tsakaninsu zuwa zaɓe, sun mayar da hankali wajen cigaban jihar. Amma dai sam bai k**ata a ce ana irin wannan talaucin ba, alhalin muna kwance a kan tarin dukiya.