26/10/2025
Dalilin da ya sa mu ka soke batun auren Mai Wushirya da Ƴarguda - Hisbah
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa ta soke batun auren jarumin Tiktok din nan Ashiru Idris Mai Wushirya da Abashiyya Yarguda bayan sun tabbatar da cewa babu soyayya a tsakanin su.
Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne, wata kotun Majistiri ta umarci hukumar Hisbah ta shirya kan auren jaruman biyu bayan an same su da laifin wallafa hotuna da bidiyoyi na badala.
Sai dai, a wata sanarwa da mataimakin Babban Kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Dakta Mujahideen Aminudeen ya aiko wa jaridar Daily Nigerian Hausa ya bayyana cewa bayan an gudanar da gwaje-gwaje, Mai Wushirya da 'Yar Guda sun tabbatar wa da hukumar cewa "Content Creation" kawai suke yi ba wai soyayya ba.
Acewar Dakta Mujahideen, daman sharadi ne a addini cewa sai Amarya da Ango sun amince da junansu kafin a kai ga daura aure.
"Tun kafin a zo maganar Sadaki ma, s**a nuna gaskiya baza su iya ba, mai girma babban kwamanda ya yi la'akari da cewa, a Musulunci Shari'a ake karewa , kuma a shari'a ba a auren dole".
Ya kara da cewa tunda ba soyayya tsakanin Haruna Tiktok din kuma na akwai bambancin halitta tsakanin su, to ta tabbata cewa za a iya rasa wannan batu na aure domin za a iya samun matsaloli bayan auren.
"Mu kuma a Hisbah, so mu ke yi aure ya zama mutu-ka-raba, ba wai a rika samun matsaloli har ta kai ga cin zarafi ba," innji Dakta Mujahideen
Haka kuma, ya ce Hisbah za ta mayar da su gaban kotu domin daukar mataki na gaba.