Islamic Online TV

  • Home
  • Islamic Online TV

Islamic Online TV Wannan shafi an kirkiro shine saboda yada addinin Allah musulunci, bamu da wani aiki daya wuce wannan Media/News/Publishing
(1)

MUYI  SALATI GA ANNABI (SAW) Domin yaye damuwa a duniya da samun gafara a lahira. Yin salati  yana jawo wa mai yi darajo...
22/08/2025

MUYI SALATI GA ANNABI (SAW)
Domin yaye damuwa a duniya da samun gafara a lahira.

Yin salati yana jawo wa mai yi darajoji 40

Kamar yadda Ibnul Qayyim ya kawo a cikin littafin sa, da ya wallafa akan salati ga Annabi saw, mai suna Jila'ul afham.
Na 1. Yin salati Bin umarnin Allah ne.
Na 2. Koyi da Allah swt, shima yana yiwa Annabi saw. salati
Na 3. koyi da Mala'iku, suma suna salati ga Annabi saw .
Na 4. Samun lada goma.
Na 5. Samun daraja goma.
Na 6. yafe laifi goma.
Na 7. Amsa adduar wanda ya fara da salati.
Na 8. samun ceton Annabi saw .
Na 9. Gafarta zunubin mai yawan salati .
Na 10. Allah zai yaye, masa abinda yake damunsa.
Na 11. Zaiyi kusa da Annabi saw. Ranar Alkiyama
Na 12. Wanda yayi salati ya sami ladan Sadaka.
Na 13. Salati sababi ne na biyan bukata.
Na 14. Allah taala Zaiyi salati ga wanda ya yiwa Annabi saw, salati.
Na 15. Salati ga Annabi saw, yana tsarkake mai yawan yinsa.
Na 16 . Zai sami bushara da Aljannah.
Na 17 . Tsira daga tsananin kiyama
Na 18 . yiwa Annabi saw salati yana tuno maka abinda ka manta
Na 19. salati yana cikin hakkokin Annabi saw.
Na 20. Salati yana kamsasa majalisi.
Na 21. Salati yana korar talauci.
Na 22. Salati ga Annabi saw yana kore rowa .
Na 23. Bazaa durmaza hancin mai salati ba.
Na 24. Mai salati ya k**a hanyar Aljannah.
Na 25. Idan akayi taro aka tashi babu salati, zaayi warin mushen jiki.
Na 26. A fara magana da yabo ga Allah da salati ga Annabi saw.
Na 27. samun haske akan siradi ranar Alkiyama
Na 28. fita daga Jafa'i, na laifi, idan anyi salati.
Na 29. Mai yawan salati ga Annabi saw, yana samun yabo da girma.
Na 30. samun Rahma
Na 31. soyayyar Annabi saw, ga mai salati .
Na 32. Annabi saw ya Nuna yana son mai masa salati.
Na 33. Samun shiriya da rayuwar zuciya .
Na 34. Duk mai yiwa Annabi saw salati, ana gayawa Annabi saw, sunan sa.
Na 35. Tabbata akan siradi ranar Alkiyama
Na 36. Yiwa Annabi saw, salati, rokon Allah, kuma ibada ne.
Na 37. Salati ga Annabi saw godiya ne ga Allah.
Na 38. salati ga Annabi saw zakka ne da tsarki ga mai yawan yi.
Na 39. Salati ga Annabi saw yana sa albarka ne ga jikin mai yi.
Na 40. Salati ga Annabi saw, bushara da Aljannah kafin mutuwa.

Sheikh Aminu Ibrahim daurawa ✍️

An tabbatar da rasuwar jaririya Ghadeer Brika, mai watanni biyar kacal a duniya, sak**akon matsanancin rashin abinci da ...
22/08/2025

An tabbatar da rasuwar jaririya Ghadeer Brika, mai watanni biyar kacal a duniya, sak**akon matsanancin rashin abinci da kuma rashin samun kulawar lafiya da ta dace da halin da take ciki tun bayan haihuwarta.

Rahoton ya nuna cewa wannan lamari ya faru ne saboda tsananin kulle da ake yi wa Gaza, tare da ci gaba da yaƙin hallaka al’umma, wanda ya hana samun abinci da magungunan da ake bukata domin ceto rayukan jarirai da marasa lafiya.

Wannan karin misali ne daga jerin daruruwan rayuka da ke salwanta kullum a Gaza sak**akon yunwa, cututtuka, da kuma rashin kulawa ta likitoci saboda kuncin da ake ciki.

Dr. Zakir Naik acikin kariyar AllahDaga Abubakar Umar Rigasa. Dr. Zakir Naik mashahorin Malamin Addinin Musulunci ne, da...
22/08/2025

Dr. Zakir Naik acikin kariyar Allah

Daga Abubakar Umar Rigasa.

Dr. Zakir Naik mashahorin Malamin Addinin Musulunci ne, dan asalin kasar India, ya shiga harkar da'awa da muhawara da ma'abota Addinai k**ar Nasara, Yahudu, Hindu, Sikh dama Mulhidai wadanda aka fi sani da (Atheist) a wannan zamani, bayan kammala karatunsa na likitanci a kasar ta India, ya kuma tasirantu ne da marigayi Sheikh Ahmad Deedat wanda shine ya bude kofar muhawara da Nasara a wannan karni 20 zuwa 21.

Ya samu nasarori masu yawan gaske kuma dubun-dubatar mutane ne s**a shiga Addinin Musulunci ta sababinsa, bayan al'amarinsa ya daukaka ya bude cibiyar bita da nazarin Addinin Islama a kasar ta India (Islamic Research Foundation ie IRF), daga bisani ya bude tashar PeaceTV a shekarar 2012 wacce itace mafi girman tashar Addinin Musulunci da ake kallo a satellite a yankin Turai da Asia dama Africa ana kiyasta masu kallonta da million 200 ko sama da haka.

Zakir Naik ya fara fuskantar kalubale daga cikin gida India yayinda yan siyasa s**a fara wasa da tunanin yan kasa akansa domin samun kaiwa ga gacci ta hanyar yi masa yarfe da kage, sun zargeshi da tsattsauran ra'ayin Addinin Islama abinda suke kira (Islamic extremists ko Islamic terrorists), daga bisani s**a yi yunkurin k**a shi.

Dr. Naik yayi gudun Hijira zuwa kasar Saudi acikin kafalar sarkin Salman bin AbdulAziz, sai dai bai jima ba ya bar kasar saboda a Saudia ba zai samu nishadin da'awar tasa ba kasancewar ba komai ne yake faduwa a kasar ba musanman saboda sauye-sauye siyasa da yarima me jiran gado (MBS) ya kawo kasar.

A yanzu haka Dr. Zakir Naik yana kasar Malaysia kuma ya samu jinsiyar kasar, wanda hakan yake nuna ya zama cikakken Dan kasar Malaysia a hukumance, sai dai kuma acikin wannan watan Dr. Zakir Naik yayi Lecture a kasar ta Malaysia akan abinde yake faruwa a yankin Kashmir na zaluncin India karkashin shugaban kasar dan jam'iyyar BJP masu tsattsauran ra'ayin kyamar Addinin Musulunci, wanda daga bisani aka samu wasu daga cikin ministocin kasar Malaysia s**a nemi ya janye wasu Maganganu da yayi da s**a fassara da tsattsauran ra'ayi.

Abin takaici shine sai ga Alarabiya jaridar Saudia tana bayyana Zakir Naik a matsayin dan Ta'adda me tsattsauran ra'ayin Addinin Islama.

Lallai idan al'ummar Musulmai s**a yadda s**a halasta jinin wannan bawan Allah daya sadaukar da rayuwarsa saboda Addinin Allah ya samu gata to lallai sunyi babban kuskuren da zasu jima suna ganin kaskaci a duniya.

Abubakar Umar..✍️

Makasan bayin Allah a cikin Ibada Ba Su Cancanci Rangwame Ba!Muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalan waɗanda aka kashe a masal...
22/08/2025

Makasan bayin Allah a cikin Ibada Ba Su Cancanci Rangwame Ba!

Muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalan waɗanda aka kashe a masallaci yayin sallar asuba (fajr), ga al’ummar Unguwan Mantau cikin Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina, da kuma mutanen Jihar Katsina baki ɗaya. Wannan mummunan lamarin ya auku ne jiya, Talata.

Kamar yadda gidan talabijin ɗin Aljazeera da wasu majiyoyi s**a ruwaito, akalla masallata 27 ne aka kashe kuma da dama s**a jikkata lokacin da wasu ‘yan fashi da makami s**a mamaye masallaci a Malumfashi, jihar Katsina, yayin sallar asuba, k**ar yadda dagacin garin da jami’an asibiti s**a sanar.

Wannan kisan gilla ya afku ne yayin da musulmi ke yin sallar jam'i mafi wahala a wajen munafukai. Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu wata sallah da ta fi nauyi (wahala) a kan munafukai fiye da Sallar Asubah da ta Isha. Idan sun san ladan da ke cikinsu, da sun halarta ko da da rarrafe ne...” (Bukhari ya rawaito, Hadisi na 657).

Dalilin da yasa aka ambaci sallar asuba a nan shi ne saboda ƙalubalen da take da shi, yin ta a kan lokaci da cikin jam'i yana nuna gaskiya da imani na mutum. Waɗanda suke kashe mutane marasa laifi ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba, suna cin amanar ɗan adam a duniya.

Muna ƙira tare da ƙarfafa gwiwar hukumomin tsaro su tabbatar da k**a waɗannan masu laifin da kawo ƙarshen wannan ta’addanci da mafi girman laifi a rayuwar ɗan adam. Masu kashe talakawa (marasa ƙarfi) ba su da tausayi, sharrinsu ya fi na dabbobi muni.

Hukumomin tsaro na iya amfani da fasahar 'geospatial analysis', wanda zai taimaka wajen gano wurin da wayoyin salula suke a lokacin aikata laifin. Za a iya amfani da shi wajen samun sahihan bayanan wayoyin salula (cell tower data) da kuma bayanan GPS, k**ar yadda na ke ba da shawara tsawon shekaru shida da s**a gabata, a sirrance da kuma bayyane.

Allah Ya karɓi waɗanda s**a rasu a matsayin shahidai, Ya ba iyalansu da danginsu haƙuri da juriyar wannan babban rashi, Ya wulaƙanta waɗanda s**a aikata wannan mummunan laifi, Ya bawa Najeriya dauwamanmen zaman lafiya. Allah Ya ba Najeriya da ‘yan Najeriya zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Professor Isa Ali Pantami, CON
(Majidadin Daular Usmaniyya)
Co-Chairman na Majalisar Manufofin Sauyi Zuwa Sabbin Hanyoyin Masana’antu ta 4 a Tarayyar Afirka (ASRIC).

Fassarawa daga Turanci zuwa Hausa: Muhammad Umar Danmasani

21/08/2025
An Ceto Saja Hamad daga ƙarƙashin tarkacen gine-gine a Gaza, bayan shafe kwanaki. 😭A ranar Talata, 20 ga Agusta 2025, ru...
21/08/2025

An Ceto Saja Hamad daga ƙarƙashin tarkacen gine-gine a Gaza, bayan shafe kwanaki. 😭

A ranar Talata, 20 ga Agusta 2025, rundunar ceto ta gano Saja Hamad daga cikin tarkacen wani gida da Isra’ila ta kai hari a Nuseirat, Zirin Gaza.

Bayan sa’o’i da dama ana hako tarkace, an samu nasarar zakulo ta tana raye – ɗaya daga cikin ƙalilan da s**a tsira daga wannan mummunan hari.

Sai dai har yanzu ana cikin tashin hankali, domin ba a san halin da kimanin Falasɗinawa 10,000 suke ciki ba. Masu ceto na hasashen cewa da yawa daga cikinsu na iya kasancewa a binne ƙarƙashin gine-ginen da s**a rushe, tun bayan da Isra’ila ta fara yaƙin da ta ayyana na ƙare dangi a watan Oktoba 2023.

Wannan al’amari ya ƙara fayyace irin mawuyacin halin da al’ummar Gaza ke ciki, tare da kira daga kungiyoyin jin kai na duniya da a ɗauki matakin gaggawa domin kare rayukan fararen hula.

Bincike Ya Nuna Cewa Ba'a Taba Samun Malamin Adddini Bahaushe Wanda Rubuce- Rubucen sa Ya Zagaya Duniyar Musulunci Ba. K...
21/08/2025

Bincike Ya Nuna Cewa Ba'a Taba Samun Malamin Adddini Bahaushe Wanda Rubuce- Rubucen sa Ya Zagaya Duniyar Musulunci Ba. Kamar Sheikhul Islam Prof. Muhd Sani Umar R/Lemo.

Allah ya karawa malam tsayuwa da tabbatuwa kan daidai, ya kiyashe shi sharrin muna fukan cikinmu azzalumai.

21/08/2025
Duk MAI HANKALI yana kiyaye abu biyar (5)(1) MAI HANKALI Yana baya baya da duniya kafin ta barshi(2) MAI HANKALI Duk mai...
21/08/2025

Duk MAI HANKALI yana kiyaye abu biyar (5)

(1) MAI HANKALI Yana baya baya da duniya kafin ta barshi

(2) MAI HANKALI Duk mai hankali yana kokarin gyara kabari kafin ya shiga

(3) MAI HANKALI Yana kokarin ya samu yardar Allah kafin haɗuwa da Allah

(4) MAI HANKALI Yana yawaita Sallah kafin ayi masa Sallah akan shi

(5) MAI HANKALI Baya yarda ya bar duniya da hakkin wani akan shi

Shaykh Muhammad Bin Uthman Hafizahullah

21/08/2025

Lacca mai taken:
Tauhidi Jigon Farko na Musulunci
Daga Biu LGA Borno state.

Mai gabatarwa prof. Muhammad sani umar Rijiyar lemo

Hisbah za ta aurar da tubabbun ƴandaba a Kano Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta duba yiwuwar baiwa tubabbun ƴanda...
21/08/2025

Hisbah za ta aurar da tubabbun ƴandaba a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce za ta duba yiwuwar baiwa tubabbun ƴandaba da gwamnati ta yafewa gurabe a shirin ta na auren gata.

Kwamandan Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Daurawa ne ya faɗi hakan yayin taron yaye tubabbun ƴandaba 718 da gwamnati ta yafewa, ƙarƙashin shirin “Safe Corridor”, wanda ya gudana a shelkwatar ƴansanda ta Kano a jiya Laraba.

Ya ce idan su ka tabbatar da shiryuwar su, a shirye Hisbah ta ke ta baiwa mai buƙata gurbin auren gata din don ƙara samun mutuwa da kintsuwa a rayuwar su.

Daurawa, ya roƙi waɗanda s**a amfana da su ƙarfafa sauran waɗanda har yanzu ba su miƙa wuya ba da su yi hakan.

Ya ƙara da cewa, ya k**ata waɗanda s**a amfana da shirin na yafiya da su rika bayar da sahihan bayanai ga hukumomin tsaro waɗanda za su kai ga cafke masu fataucin miyagun ƙwayoyi a cikin jihar.

Address


Telephone

+2348038723868

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Islamic Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Islamic Online TV:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share