22/09/2025
TARON GANGAMI NA ƘASA ZABE NA SHEKARA TA 2025
Kwamitin Shirya Taron Gangami Na Ƙasa (NCOC), a madadin Kwamitin Zartarwa Na Ƙasa (NEC) na babbar jam’iyyar mu, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya fitar da sunayen mambobin kwamitocin rassa daban-daban da aka amince da su domin shirya Taron Gangamin Na Ƙasa Zabe na Shekara ta 2025 na jam’iyyar mu.
Wannan taro na musamman zai gudana ne domin zaɓen sabbin jami’an jam’iyyar na ƙasa, a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, daga ranar Asabar 15 zuwa Lahadi 16 ga watan Nuwamba, 2025.
kwamitocin shirya taron gangami naƙasa
Duba jerin sunayen a ƙasa.