Muhammad Auwal

  • Home
  • Muhammad Auwal

Muhammad Auwal 🙌💚

11/12/2025

Kai Tsaye cikin Daren Nan , Maulidin Sayyada Fatima Zahra (S) . Baitocin yabon sayyada tare da Sulaiman S Uziri.

Jagora (H) Ya Tura Da Wakilai Don Ta'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru BauchiA yau Alhamis, 13 ga Jimadal Thani 1447 (4/12/20...
04/12/2025

Jagora (H) Ya Tura Da Wakilai Don Ta'aziyyar Rasuwar Shehu Dahiru Bauchi

A yau Alhamis, 13 ga Jimadal Thani 1447 (4/12/2025), wanda ya dace da kwanaki bakwai da rasuwar Shaikh Dahiru Usman Bauchi, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya tura da tagawar musamman don yin ta'aziyya ga iyalai da almajiransa.

Sayyid Badamasi Yaqoub, wanda yake ƙani shaƙiƙi ga Jagora, ya bayyana ta'aziyyar Jagora (H) ga iyalan Shehin, tare da bayyana rashinsa a matsayin wani bango ga duniya, a matsayinsa na mahaddacin Alkur'ani, kuma mai hidima ga Alkur'ani a tsawon rayuwarsa.

Ta bangaren iyalan mamacin, Khalifa Shaikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya nuna godiyarsu ga ta'aziyyar, tare da bayyana rashin Shehin a matsayin abin yi ta'aziyya wa juna gabadaya. Ya bayyana irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky da marigayi Shaikh Dahiru Bauchi, inda ya bada misali da irin lokutan da Shaikh Zakzaky ya rika ziyartan Shehi a baya, har Shehi kan gabatar da shi ya ja su Sallah.

Tawagar ta hada da babban ɗan Jagora (H), Sayyid Muhammad Zakzaky, da 'yan uwan Jagora na jini, tare da ba'adin wakilan 'yan uwa daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

An gabatar da addu'o'i na musamman ga Shehin, dafatan Allah Ta'ala Ya jaddada masa rahama da jinkai.






13/Jimada Ath-Thaniyah/1447
04/12/2025

AN SAMU WANI HOTEL MAI SUNAN ZARIA  A KASAR RWANDA  TAFIYA MABUDIN ILIMICiroman Dawakin Zazzau, Alhaji Musa Tijjani, wan...
03/12/2025

AN SAMU WANI HOTEL MAI SUNAN ZARIA A KASAR RWANDA

TAFIYA MABUDIN ILIMI

Ciroman Dawakin Zazzau, Alhaji Musa Tijjani, wanda ke halin yanzu a kasar Rwanda (Kigali) domin gudanar da wasu ayyuka, cikin mamaki da farin ciki, an saukar da shi a wani Otel da ke ɗauke da sunan ZARIA”.

Bayan ya gudanar da bincike, sai ya gano cewa mamallakin otel ɗin ya bayyana masa cewa ya yi karatunsa ne a birnin Zariya, kuma ya ƙaunaci rayuwa da zaman lafiya da mutanen garin s**a nuna masa a lokacin. Wannan kyakkyawar gogewa ce ta sa ya yanke shawarar sanya wa otel ɗinsa suna “ZARIA” a matsayin tunawa da girmamawa ga garin da ya ba shi ilimi da soyayya.

BURIN MAHAIFINA YA CIKA DUK DA BAYA DUNIYA: INJI FATIMA ISHAQ IBRAHIM Fatima (Iman) tana daya daga cikin daliban da s**a...
01/12/2025

BURIN MAHAIFINA YA CIKA DUK DA BAYA DUNIYA: INJI FATIMA ISHAQ IBRAHIM

Fatima (Iman) tana daya daga cikin daliban da s**ai haddar littafin Allah Al-kur'ani mai tsarki a jiya, ta fashe da kuka jim kadan bayan tashi daga saukar yayanta Muazzam ya dauketa s**a wuce makabarta inda mahaifinta ke kwance tsawon shekara hudu.

Babana bashi da wani buri face in zama Likita kuma mahaddaciyar alkur'ani cikin ikon Allah yayin da ya kwanta ciwon ajali sai nasami Admission na karatun aikin likita a Jamiar Northwest University, Kano. yayi matukar farinciki yana kwance a asibiti nake gaya masa idan na kammala karatu zan nemi kwarewa akan fanni ciwon koda (Kidney) domin cigaba da kula dakai ashe ciwon bana tashi bane, ko semester daya bamuyi ba Allah yakarbi ranshi. Mhmm.

Kafin rasuwar shi nayi sauka amma sabida na cika masa burinshi duk da baya raye kuma shine yasan dalilin dayasa yake so na haddace Al'kurani duk da nima ina da sha'awa matuka sai na koma makaranta domin yin hadda Alhamdulillah Alhamdulillah yau gashi nayi hadda kuma gashi yau ce rana ta farko danaga kabarin mahaifina Allah don darajar wannan littafi da ka saukar awatan da yafi kowanne wata falala da daren dake cikin watan albarkacin mafificin hallita sayyidina Muhammad jikan mahaifina kasa Jannatul firdausi itace makomar mu baki daya. Hakika ina cikin farin ciki amma rashin ganin mahaifina a yau hankali na ya tashi fiye da ranar daya bar duniya.

Mahaifiyata Maryam Ibrahim Wada Allah yayi miki albarka bisa jure duk wata tangarda ta rayuwa da hana kanki jindadi don kiga munyi rayuwa mai kyau da inganci burin ki da yarage akaina na tafiya dakin miji da yardar Allah bazan baki kunya ba, cikin wani lokaci bada jimawa ba zakiji ni. Allah ya sakawa malaman mu da s**ai hidima akan mu Allah yajikan Khalifa Ishaq Rabiu bisa alkhairi daya dasa muka taso muke kwankwada.

Fatima Ishaq Ibrahim
Dalibar Karutun Aikin Likita

Hotuna :wakilin yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky  na garin Bauchi , Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ya ziyarci Farfesa Ibrahim ...
01/12/2025

Hotuna :

wakilin yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky na garin Bauchi , Sheikh Ahmad Yusuf Yashi ya ziyarci Farfesa Ibrahim Maƙari yau Litinin a garin Bauchi.

ziyarar ta Ta'aziyyar rashin Sheikh Dahiru Usman Bauchi , dakuma ƙarin kusantar juna don haɗin kan Musulmai.

Anyi addu'a na musamman ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

'' Sheikh Sharif Sale ne zai jagoranci jana'izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Gobe juma'a.  kamar yadda ɗaya ci...
27/11/2025

'' Sheikh Sharif Sale ne zai jagoranci jana'izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi a Gobe juma'a.

kamar yadda ɗaya cikin iyalan Marigayin Surunbai ya furta wa manima Labarai .

Allah yajiƙan Shehu tasadashi da Annabi Muhammad (S).

Haƙiƙa yau an wayi gari da rashi mai girma.Allah Ta'ala Ya jikan Shehi da rahamarSa, Ya yafe kurakuransa, Ya karbi uzuri...
27/11/2025

Haƙiƙa yau an wayi gari da rashi mai girma.

Allah Ta'ala Ya jikan Shehi da rahamarSa, Ya yafe kurakuransa, Ya karbi uzurinsa, ya albarkaci bayansa, Albarkacin hidimarsa ga Alkur'ani, Allah Ta'ala Ya sada shi da ceton masoyinsa Manzo Rahma (S).

Allah Ya ba iyalai, dangi, almajirai da masoya hakurin rashinsa. Ilahi Ameen Ya Allah 🤲

Anyi Jana'izar Dr Aliyu Sani Muhammad ƙaura.Da misalin ƙarfe 11 na safiyar yau Alhamis , 20 gawatan Nuwamba 2025 , aka g...
20/11/2025

Anyi Jana'izar Dr Aliyu Sani Muhammad ƙaura.

Da misalin ƙarfe 11 na safiyar yau Alhamis , 20 gawatan Nuwamba 2025 , aka gabatar da jana'izar Dr Aliyu Sani Muhammad ƙaura (Alharazimy Bin Sani) . wanda Allah yayiwa rasuwa jiya Laraba , sanadin haɗarin mota. Hanyar dawowar su gida Zariya daga Bauchi.

Dubban al' umma daga sassa , s**a halarci jana'izar , wanda babban limamin ƙasa Farfesa Ibrahim Maƙari ya jagoranta.
Bayan kammala jana'izar an raka Marigayin makwancin sa maƙabartan musulmai dake Unguwar Bishar cikin birnin Zariya.

Muna addu'an Allah yajiƙan shi yasa ya huta.

Wasu daga cikin hotunan hicking duk Cikin birthday din Shahid Ahmad Zakzaky...
20/11/2025

Wasu daga cikin hotunan hicking duk Cikin birthday din Shahid Ahmad Zakzaky...

Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un 😭 Yanzu muke samun labarin rasuwar Malam Abdullahi Mai Batula.  wanda yake bakin kasu...
20/11/2025

Innalillahi Wa'inna ilaihi Raji'un 😭

Yanzu muke samun labarin rasuwar Malam Abdullahi Mai Batula. wanda yake bakin kasuwa (karauka ) Zariya City.

Marigayin Sha'iri ne. mai yabon Annabi Muhammad (S) . kuma yana cikin Muridan Sheikh Usman kusfa (Rigi Rigi).

Za'ayi gabatar da Jana'iza 2:30pm .

A Karauka Cediya Biyu Bakin Kasuwan Zaria

Allah Yajikansa Da Rahama yasa ya huta Amin 🤲.

Wasu daga cikin hotunan Katman taron tunawa da ranar Haihuwar Shahid Ahmad Zakzaky wanda jasaz s**a shirya na Tsawon kwa...
19/11/2025

Wasu daga cikin hotunan Katman taron tunawa da ranar Haihuwar Shahid Ahmad Zakzaky wanda jasaz s**a shirya na Tsawon kwana uku a garin Zaria........

Rundunar sojin ƙasar nan ta gina wa alʼummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna makarantar firamare.Indai za'a tuna  Tu...
19/11/2025

Rundunar sojin ƙasar nan ta gina wa alʼummar garin Tudun Biri da ke jihar Kaduna makarantar firamare.

Indai za'a tuna Tudun Biri shi ne garin da jirgin soji ya jefa Bomb bisa kuskure yayin da ake bikin Mauludi kusan shekaru biyu baya .
dinbin jama'a s**a rigamu gidan gaskiya , wasu kuma s**a jikkata.

Hotuna daga Maʼaikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna.

19/11/2025

Address


Telephone

+2347032541235

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muhammad Auwal posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muhammad Auwal:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share