Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur

  • Home
  • Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur

Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur Personal Organization

Malamai s**a ce"Halittun Allah wajen biyayya da saɓa wa Allah sun kasu kashi uku (3):1.Wadanda alkhairi ne a tare dasu b...
27/10/2022

Malamai s**a ce"Halittun Allah wajen biyayya da saɓa wa Allah sun kasu kashi uku (3):

1.Wadanda alkhairi ne a tare dasu babu sharri (Manzanni, Annabawa da Mala'iku).
2.Wadanda sharri ne a tare dasu babu alkhairi (Shaidan da Shaidanu).
3.Wadanda s**a haɗa alkhairi da sharri (Mutane)".

Note:
Don haka idan alkharin mutum ya rinjayi sharrin sa to mutumin kirki ne, idan kuwa sharrin sa ya rinjayi alkharin sa to ba mutumin kirki bane.

Allah yasa alkhairan mu su rinjayi sharrin mu.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
27/10/2022M

Korafi (الهلع)da Koke-koke (الجزع)Malamai s**a ce"Idan kaga mutum yana yawan korafi da koke-koke to sallan sa da wasu ab...
26/10/2022

Korafi (الهلع)da Koke-koke (الجزع)

Malamai s**a ce"Idan kaga mutum yana yawan korafi da koke-koke to sallan sa da wasu abubuwa takwas (8)suna da matsala;
"Wato idan yana kiyaye wadannan abubuwa tara(9)zai kubuta daga ɗabi'an korafi da koke-koke,gasu kamar haka:
1.Tsaida Sallah
2.Bayar da hakkin dukiya
3.Gaskata ranan sakamako
4.Tsoron azaban Allah
5.Nisantan Zina
6.Kiyaye Amana
7.Cika alƙawari
8.Tsayuwa akan shaidan gaskiya
9.Kiyaye rukunnai da kuma lokutan Sallah.
"Allah (S.W.T)ya kawo wannan mafita ne a cikin suratul Ma'arij Aya ta (23-34).

Allah yasa mu dace.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
26th October,2022M

Sayyiduna Aliyu (R.A)yana cewa"Duk wanda halaye shida(6)s**a kasance cikin ɗabi'unsa to be bar wani hali da ake neman Al...
25/10/2022

Sayyiduna Aliyu (R.A)yana cewa"Duk wanda halaye shida(6)s**a kasance cikin ɗabi'unsa to be bar wani hali da ake neman Aljanna dashi ba:-
1.Wanda yasan Allah kuma ya bishi.
2.Yasan shaidan kuma ya saɓa masa.
3.Kuma yasan gaskiya ya bishi.
4.Yasan karya ya kiyaye shi.
5.Yasan duniya kuma yayi watsi da ita.
6.Yasan lahira kuma ya neme ta.

Allah yasa mu dace duniya da lahira.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
25th October,2022M

Kofofin Shaiɗan guda Sha Bakwai (17):1.Jahilci2.Fushi3.Son duniya4.Dogon buri5.kwadayi6.Rowa7.Girman kai8.Son yabo9.Riya...
24/10/2022

Kofofin Shaiɗan guda Sha Bakwai (17):

1.Jahilci
2.Fushi
3.Son duniya
4.Dogon buri
5.kwadayi
6.Rowa
7.Girman kai
8.Son yabo
9.Riya
10.Jiji-dakai
11.korafi da koke-koke
12.Bin son zuciya
13.Mummunan zato
14.Wulakanta Musulmi
15.Raina zunubbai
16.Amince wa talalan Ubangiji
17.Debe tsammani daga Rahman Allah.
Waɗan nan sune hanyoyin da shaidan yake amfani dasu wajen lalata zuciyan ɗan Adam.

Allah yakare mu daga sharrin shaidan da shaidanu.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
24th October,2022M

Imam Sufyan bin Uyainah (R.H) yana cewa"Ba a samun ilmi sai ta hanyar Ibada,domin ilmi yana gayyatan aiki ,idan ya amsa ...
21/10/2022

Imam Sufyan bin Uyainah (R.H) yana cewa"Ba a samun ilmi sai ta hanyar Ibada,domin ilmi yana gayyatan aiki ,idan ya amsa masa to, amma idan bai amsa masa ba sai ilmi ya tafi abinsa, domin babu alkhairi cikin bishiyan da babu ganye babu 'ya'ya sannan bazai yiwu a samu 'ya'yan itace ba bishiya ba".

(واتقوا الله ويعلمكم الله).

Allah yasa mu dace.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
025/03/1444H
021/10/2022M

Imam ash-shafi'eey (R.H) Yana cewa"Neman ilmi yafi sallan nafila falala". Shi yasa Imam as-suyudeey (R.H)Yayi Nazmi akan...
20/10/2022

Imam ash-shafi'eey (R.H) Yana cewa"Neman ilmi yafi sallan nafila falala". Shi yasa Imam as-suyudeey (R.H)Yayi Nazmi akan haka:

والعلم خير من صلاة نافلة # فقد غدالله برزق كانافلة.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
24/03/1444H
20/10/2022M

Allah yasa mu dace.

Tsakanin Musiba da Shirka;Sheikh Muhammad bn Abdilwahhab at-Tamimi (R.H)Yana cewa"Duk girman musiba bata kai shirka hats...
19/10/2022

Tsakanin Musiba da Shirka;

Sheikh Muhammad bn Abdilwahhab at-Tamimi (R.H)Yana cewa"Duk girman musiba bata kai shirka hatsari ba"
(Ya faɗi haka ne a ranar da yake cewa almajiran sa zai rubuta littafi na musamman akan tauhidul ibada).
(كتاب التوحيد)

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
023/03/1444H
019/10/2022M

(WAHHABIYYAH)Makircin yahudawa:1."Abdulwahab Rastum"*Aqeedah (Khawarij),*Zamani (Farko-farkon qarni na ɗaya)*Daula (Rust...
18/10/2022

(WAHHABIYYAH)

Makircin yahudawa:

1."Abdulwahab Rastum"
*Aqeedah (Khawarij),
*Zamani (Farko-farkon
qarni na ɗaya)
*Daula (Rustamiyyah)
*Helkwata(Tunis)
*Lakabi (Wahhabiyyah).
2.Sheikh Muhammad bn Abdilwahhab at-Tamimi(R.H)
Aqeedah (Ahlussunnah wal-Jama'ah)
Zamani (Farko-farkon qarni na 12).
Abin lura;
Sai Yahudawa s**a dauko rigan Abdulwahhab Rastum (Wahhabiyyah) s**a sanya wa Mutumin kirki"Muhammad bn Abdilwahhab at-Tamimi (R.H),domin su rusa da'awar sa na tsarkake Imani da Tauhidi.

Allah yasa mu dace.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
022/03/1444H
018/10/2022M

Wurare(12)da bai halalta ayi sallah a wajen ba:1.Bola/Juji/Bingi/Goya2.Mayankan dabbobi (abatoir)3.Tsakiyan hanya(saidai...
17/10/2022

Wurare(12)da bai halalta ayi sallah a wajen ba:
1.Bola/Juji/Bingi/Goya
2.Mayankan dabbobi (abatoir)
3.Tsakiyan hanya(saidai idan akwai lalura)
4.Makwantan raƙumi
5.Cikin Makabarta
6.Dakin wanka (Bathroom)
7.Masjid addiraar
8.Filin da aka kwace akan zalunci aka gina masallaci
8.Wajen fasadi da makamantan su (Club etc)
9.Wajen da ake bautan wanin Allah (Church e.t.c)
10.Tsakanin gimshiqi da gimshiqi a masallaci (b/w 2 pillars)
11.Saman dakin ka'bah
12.Wajen da aka hallaka wasu al'ummai(Adawa/samudawa).

Allah ya datar damu.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
020/03/1444H
017/10/2022M

Wani bawan Allah ya tambayi sayyiduna ( Abubakar R.A),cewa shin ba kowa yana cin rabon da Allah ya ƙaddara masa bane a d...
14/10/2022

Wani bawan Allah ya tambayi sayyiduna ( Abubakar R.A),cewa shin ba kowa yana cin rabon da Allah ya ƙaddara masa bane a duniya?sai sayyiduna Abubakar yace "Eh", sai Mutumin yace"to ashe barawo idan yayi sata rabon sa da Allah ya kaddara masa yaci kenan?,sai sayyiduna Abubakar yace"Eh, rabon sane, da yayi haquri da Allah ya bashi ita ta hanyar halal, amma sai yayi gaggawa".

Allah ka azurta mu da Halal.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
18/03/1444H
14/10/2022M

13/10/2022

An tambayi (ibnl Mubarak R.H),Su waye mutane?,sai yace"Masana addini",su waye masu mulki?,sai yace"Masu gudun duniya",su waye makaskanta?,sai yace"Masu neman duniya da addini".

Rabbi sallim-sallim.

Allah yasa mu dace.

✍️ Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
17/03/1444H
13/10/2022M

Rashin Sani(Tushen Hauragiya da Shirme).An tambayi Imam Malik(R.H)"Mutumin da aka zo zantar masa da hukuncin kisa, ɗan l...
12/10/2022

Rashin Sani
(Tushen Hauragiya da Shirme).

An tambayi Imam Malik(R.H)"Mutumin da aka zo zantar masa da hukuncin kisa, ɗan lokacin da ya rage a rayuwarsa wani aikin Ibada zai yi? sai yace"Neman ilmi",sai aka ce masa"ai bazai samu daman aiki dashi ba",sai yace"Neman ilmi yafi aikin falala".

Allah yasa mu dace.

Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
12/10/2022M

Malamai s**a ce"Ilimi yana da matakai guda uku (3):Wanda ya hau mataki na ɗaya (1) zai ringa girman kai,Wanda ya hau mat...
11/10/2022

Malamai s**a ce"
Ilimi yana da matakai guda uku (3):
Wanda ya hau mataki na ɗaya (1) zai ringa girman kai,
Wanda ya hau mataki na biyu (2) zai ringa kankan dakai,
Wanda ya hau mataki na uku (3) zai fahimci bai ma san komai ba".

(...وما أوتيتم من العلم إلا قليلا)

Allah yasa mu dace.

Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur (abu-fatima)
15/03/1444H
11/10/2022M

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ustaz Fa'izu Inuwa Tukur:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share