Amaan Multimedia

  • Home
  • Amaan Multimedia

Amaan Multimedia Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Amaan Multimedia, Media/News Company, .

22/07/2024

"Baza Muyi Zanga-Zanga Ba Zamu Nemi Dauki Wajen Allaah"

-Kamar Yadda Annabi Musa Da Mutanensa Sukayi (Lokacin Zaluncin Fir'auna)-

Shugabanci ko 'Jagoranci yana nufin shugabantar al'ummah ko mulki ko samun madafan iko ko jagorancin al’umma. Haka kuma ...
17/06/2024

Shugabanci ko 'Jagoranci yana nufin shugabantar al'ummah ko mulki ko samun madafan iko ko jagorancin al’umma. Haka kuma shugaba shi ke tabbatar da cewa an bin doka da oda kamar yadda aka tsara. Kuma shi ne mai bayar da umarni wajen tafiyar da ayyukkan yau da kullum wadanda mabiyansa ne sukeyi. Shi ko wucewa gaban al’ummarsa na biye da shi. Kowa ya zura masa ido don daukan umarni da biyayya ga abin da ake so ya yi a bisa tsarin doka. Duk da cewa shugaba idan ya taka doka za'a iya hukuntashi

Abin lura a nan shi ne shugaba bawa ne wajen hidimta wa al’ummarsa, ta hanyar jagorantar su a cikin al’amauran da ya shafi cigaban su da Kuma Abubuwan bukatunsu. Jagoranci muhimmin aiki ne na gudanarwa wanda ke taimakawa wajen haɓaka aiki da kuma cimma burin Al'umma

Toh amma hakan yayu a Najeriya kuwa yayi Shugaban ci ba musan inda ya dosa ba kalli fanni tsaro abun kullum sai addu,a gashi fannin kayan Abinci kuwa sai mu ce Allah ya kyauta ameen

Matsalar Najeriya bata Karin albashi bane a yanzu gwamnati tayi control price shine ina hankalin ka yake an baka dubu sittin 60 masara dubu tamanin 80 gaskiya mu farka talaka

Taken wannan Sharhi shine

Mun waye amma bamu da wayo ko mai amfani dimokuradiyya a gun mu ????

Kasan ce da AMAAN MULTIMEDIA

ABBA NUHU ABUBAKAR

Assalamu alaikum ya al’amurar musulmi Ina maku fatan alkairi,da fatan Allah ya sada mu da rahamar sa. Allah ya kawo mana...
06/06/2024

Assalamu alaikum ya al’amurar musulmi Ina maku fatan alkairi,da fatan Allah ya sada mu da rahamar sa. Allah ya kawo mana dauwamamnen zaman lafiya a Nijeriya, musamman yankin Arewa da sauran sassan kasa baki daya ameen.
Amincin Allah, Taimakon Allah, Rahmar Allah, Gafarar Allah, Alherin Allah, Tsantsar Soyayyar Manzon Allah, Tarin Ilimi da aiki dashi, koshin Lafia, yalwar Arziki, Dauwamammen rufin Asiri, Cikawa da Imani duk su tabbata agareku, iyalanku da mahaifanku amin. Barka da Juma’a

03/05/2024

Ranar ƴan jarida ta duniya: Aikin jarida a yanayi na ƙalubale iri-iri

A kowacce ranar 3 ga watan Mayu ne Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan Jarida ta Duniya, bikin da ke gudana da nufin samar da cikakken ‘yancin tofa albarkacin baki a aikin na jarida, sai dai a wannan karon ranar na zuwa a dai dai lokacin da tarin ‘yan jarida ke fuskantar tarnaki a ayyukansu.

ranar: 03/05/2024 -

Bisa al’ada hukumar UNESCO ke jagorantar gudnar da bikin ranar a kowace shekara tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da fara gudanar da bikin ranar a shekarar 1993 da nufin bai wa ‘yan jarida cikakkiyar damar samun bayanai da kuma yaɗa su, baya ga samun damar iya sharhi ko tofa albarkacin baki kan dukkanin lamurra ba tare da nuna musu tsangwama ko ƙyara ba baya ga bai wa ma’aikatan na jarida cikakkiyar kariya daga dukkan barazana ko hare-hare.
Kamar kowacce shekara a wannan karon ma hukumar ta UNESCO ita ke gudanar da bikin ranar da hadin gwiwar gwamnatin Chile a birnin Santiago, yayin da gangamin bikin ranar ke gudana a fiye da kasashe 100.
Taken ranar a bana shi ne halin da aikin jarida ke ciki a wani yanayi da Duniya ke fuskantar tarnaki ta fuskar yaki da dumamar yanayi, lamarin da ya sanya hukumar ta UNESCO nanata kiran ganin ‘yan jaridan sun jajirce wajen isar da sakwannin don magance matsalolin da s**a dabaibaye duniya.
A nata bangaren kungiyar tarayyar Turai ya bayyana bikin ranar ‘yancin ‘yan jaridan ta bana a matsayin mai cike da tarnaki, lura da yadda kasashe fiye da 60 ke gudanar da zabuka wanda ya sanya aikin jarida a tsaka mai wuya.
Sanarwar da UNESCO ta fitar game da ranar, ta ce wajibi ne gwamnatocin kasashe su bayar da cikakkiyar kariya ga ‘yan jarida don kauce wa kai musu hare-hare musamman a bakin aiki tare da basu damar gudanar da ayyukansu a lumana, yayin da hukumar ta yi tir da kai hare-hare kan ‘yan jaridar wadanda da dama kan rasa rayukansu a bakin aiki.

15/04/2024

Ƙungiyar NATO Ta Yi Allah-Wadai Harin Ramuwar Gayyar da Iran ta kai A Kan Isra’ila.

Ƙungiyar Tsaro ta NATO ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, tare da yin kira na ganin an kiyayi kai ire-iren hare-haren domin guje wa zubar da jini.

NATO ta soki harin da Iran ta kai cikin dare, inda ta ce tana sanya ido kan abubuwan da ke faruwa domin ɗaukar matakan da s**a dace.
Mai magana da yawun NATO, Farah Dakhlallah, ya ce yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye domin rikicin na iya dagula lamura a Gabas ta Tsakiya wanda hakan na barazana ga zaman lafiyar duniya.

Sai dai Iran ta yi barazanar duk ƙasar da taɓa sararin samaniyarta wajen kai mata hari to za ta ɗanɗana kuɗarta.

Iran dai ta kai harin ne, a matsayin wani martani kan harin da Isra’ila ta kai wa ofishin Jakadancinta da ke birnin Damascus.

27/03/2024

Ranar 17 Ga Ramadan Aka Yi Yakin Badar

A ranar 17 ga watan Ramadan, aka yi Yakin Badar Tsakanin Musulmi da kafiran Makkah a zamanin Manzon Allah (SAW).

Sahabban Manzon Allah 14 ne s**a yi shahada a shahararren yakin, wanda aka gwabza tsakaninsu da kafiran Makkah a wani wuri da ake kira da suna Badar a kusa da Madina

ALLAH don sirrin nasara da ke cikin ranar Allah ka ya yewa dukkan Musulmi damuwa ameen
Sunayen Shahidan Yakin Badar

Umair bin Abi Wakkas

Safwan bin Wahb

Dhu-shamalain bn Abd Amr

Muhji’ bn Salih

Akil bn Albakir

Ubaidah bn Alharith

Sa’ad bn Khaithuma

Mubasshir bn Abdulmundhir

Haritha bn Suraka

Rafi’ bn Almu’alla

Umair bn Alhammam

Yazid bn Alharith

Mu’awwadh bn Alharith

Auf bn Alharith.

Yau ranar Musulmi ta duniya Allah ya daga Musulmi da musulunci ameen albarkacin Annabi

Am proud to be a Muslim

09/02/2024
05/02/2024

Arewa mu

A gaskiya mu yan arewa muna cikin damuwa da kunchin rayuwa ya kamata shugaban nin mu ku farka idan bacci kukeyi halin da muke cikin wallahi ya kazanta muna kwana da kunchi da hahhawan farashi kayan masarufi komai yayi tsada idan muka dauko fanni tsaro matsala rashin tsaro Arewa ne bara ce bara ce Arewa ne mutuwar Aure yayi yawa yankin mu ina matsalar take kuma laifin wane Laifin Mayan Arewa ne koh Sarakunan mu koh masu hannun da shuni ne koh matasan Arewa ne koh kuma laifin malaman namu ne yakamata koh ceto mu domin ruwa zai cimma na
Ku taimaka mana akan wannan lamarin Nigeria daya ce amma kowa yasan gidan mahaifinsa Allah ya kawo mana sauki albarkacin sayyaduna Rasulullah s a W

03/02/2024

*Wonderful!!!* This is very rare in the history of the holy land Mecca. The whole world jointly and in unism praying for Nigeria in one voice in Kaabah, to overcome its challenges of Boko Haram,kidnappings and other social problems. Wow! Isn't this rare and wonderful? Nigeria will surely take it's rightful place and position in the committee of great countries of the world. Nigeria is destined for greatness. God bless Nigeria.🙏🏼

Address


Telephone

+2347087995957

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Amaan Multimedia posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share