
09/09/2025
Ƙunshi, Bijimi kuma Tudu na Siyasar Kaduna Tsakiya: Yerima Usman Shettima – Zakaran Siyasa Da Ba Shi Da Kasala a Ƙarni na 21
A cikin fagen siyasar da kullum ke motsi da sauyi a Kaduna Tsakiya, shugabanni kan tashi su kuma faɗi, amma kaɗan ne suke rubuta sunayen su a cikin tunanin al’umma. Yau, fagen siyasa na shaida fitowar wani mutum wanda ƙarfin sa, juriya da tasiri s**a sake fasalta siyasa a wannan yanki, Ambasada Yerima Usman Shettima, ana bayyana shi da “Ƙunshi (Bale)”, “Bijimi (Bull)”, da kuma “Tudu (Hill)” na Kaduna Tsakiya, amma a zahiri, Shettima ya tabbatar da kan sa a matsayin Zakaran siyasa marar kasala na karni na 21.
Kamar ƙunshi (Bale), Shettima yana wakiltar haɗin kai da cigaba a wuri na taro inda mutane ke haɗuwa don samun mafita da damar ci gaba. Ya zama ginshiƙin ga matasa, mata da al’ummomin da aka tauye ke taruwa a kewayen sa, ba wai don alƙawari marasa amfani ba, amma don wakilci na gaskiya da kuma ƙarfafa gwiwa.
Kamar “Bijimi (Bull),” yana nuna ƙarfi, jajircewa da ƙarfin zuciya. Siyasar Kaduna Tsakiya ba ta taɓa zama ta masu rauni ba, amma Shettima ya riƙa nuna ƙarfin jure matsin lamba, fuskantar ƙalubale kai tsaye, kuma ya kasance ba ya girgiza da guguwar makirce-makirce na siyasa. Muryar sa ta zazzafar kira ga adalci, daidaito da kare talakawa ta bambanta shi daga sauran ’yan siyasa na yau.
Kamar “Tudu (Hill),” yana tsaye da ƙarfi, ba ya motsi, kuma kowa na iya ganin sa. Shettima ya zama misali a tattaunawar siyasar Kaduna, ƙasa mai tudu daga inda hangen nesan sa na ci gaba, haɗin kai, da sauya al’umma ya ke haskawa. Kamar dutse, ba za a iya yi masa watsi ba; kasancewar sa tana jawo hankalin kowa, kuma tasirin sa ya zarce Kaduna Tsakiya.
Amma wataƙila mafi dacewa wajen bayyana Yerima Shettima shi ne matsayin Zaki sarkin dajin siyasa. Jarumtar sa wajen faɗar gaskiya ga masu mulki, ikon sa na ba talakawa ƙarfin gwiwa, da kuma tsayuwar sa tsayin daka wajen ingantacciyar mulki sun sanya shi ɗan siyasa na musamman a wannan zamani. Ba wai kawai ya shiga siyasa ba ne da molon ka, ya mamaye ta da tunani, dabaru, da shugabanci da zai mayar da hankali ga al’umma.
Yayin da Kaduna Tsakiya ke shirye-shiryen sake shiga wani muhimmin mataki a tarihin siyasar ta, yana ƙara bayyana cewa Shettima ba kawai ɗan takara ba ne, shi ne motsi, shi ne murya, shi ne kuma zaɓin da ba za a iya kaucewa ba na al’ummar da ke neman wakilci na gaskiya.
Lallai, Ƙunshi, Bijimi da Tudu na Siyasar Kaduna Tsakiya shi ne Yerima Usman Shettima, Zakaran siyasa marar kasala na karni na 21.
Allah ya tabbatar da alkhairin Yerima Usman Shettima, amin.