02/07/2025
Wanda Yaci Amanarka Ko Kuma Ya Ha'inceka, Ya Koya Maka Darasi Ne Akan "Yarda", Wanda Kuwa Ya Barka Lokacin Da Kake Buƙatarsa, Ya Koya Maka Darasi Ne Akan "Dogaro" Dan Haka Ciro Wayarka Ka Tura Masa Saƙon "Nagode Da Darasin Da Ka Koya Mini"
Ka Daina Baƙin Ciki Dan Wani Ya Fita A Rayuwarka, Da Sannu Shima Wani Zai Fita A Rayuwarsa Yaji Abinda Kaji.
Wanda Ya Cutar Dakai Haka Siddan, Koda Ya Tuba Karka Yafe Masa, Domin Kai Ai Ba Ubangiji Bane Mai Yafe Dukkan Laifuka.
Mun Wayi Gari, Yafiya Sabuwar Dama Ce Ta Maimaita Kuskure, Wanda Ya Soke Ka Da Tsini Tun Farko, Sallameshi Tun Daga Bakin Ƙofar Rayuwarka! Ya Juya, Sake Bayar Da Dama Ga Wanda Ya Cutar Dakai A Karon Farko, Kamar Kyautar Harsashi Ne Ga Wanda Yayi Nufin Kasheka Ya Saɓa Saiti.☹️
Sai Dai Fa Shi Wanda Ka Tabbatar Yana Sonka Da Gaskiya Duk Saɓaninku Karka Barshi Ya Fita A Rayuwarka, In Kuwa Ka Barshi Haƙiƙa Zai Karya Maka Wannan Abin Da Yake Cikin Ƙirjinka Karayar Da Babu Lallai Ta Ɗoru Ba!