17/08/2025
SHIN MACE ZATA IYA DAUKAR CIKI KO BATAYI RELEASING BA?
Tambaya: Idan ma’aurata sunayun six, mace bata kawowa, shin hakan na iya hana samun ciki?
Amsa: A’a, mace na iya samun ciki ko da bata kawo sha’awa ba yayin jima’i. Samun ciki yana faruwa ne idan maniyyin namiji ya hadu da kwai na mace a lokacin ovulation (lokacin da mace ke da damar daukar ciki).
Me yasa ake ganin cewa mace ba za ta haihu ba idan ba ta kawowa?
👉🏼 Rashin jin daɗi da bushewar gaba – Idan mace ba ta kawo sha’awa ba, za ta iya fuskantar bushewa yayin jima’i, wanda zai iya rage motsin maniyyi zuwa mahaifa.
👉🏼 Ƙarancin ruwan sha’awa – Ruwan sha’awa na mace na taimakawa wajen sauƙaƙa tafiyar maniyyi zuwa mahaifa. Idan ya yi ƙaranci, yana iya rage damar haihuwa, amma ba yana nufin ba zai yiwu ba.
👉🏼 Matsalolin Hormones – Idan mace bata kawo ba sosai, yana iya nuna cewa tana da matsala a hormone, wanda zai iya shafar haihuwa.
Menene mafita?
✅ Kasance cikin natsuwa yayin jima’i – Damuwa na iya hana mace jin daɗi da kawo sha’awa.
✅ Yin wasa kafin jima’i – Yin wasa da juna kafin jima’i na iya ƙara jin daɗi da taimakawa mace ta kawo.
✅ Shan ruwa mai yawa – Yana taimakawa wajen kara yawan ruwan sha’awa da saukaka jima’i.
✅ Amfani da lubricants (man shafe-shafe) – Idan mace na fama da bushewa, za a iya amfani da man shafe don sauƙaƙa jima’i.
✅ Ziyartar likita – Idan ana fama da matsala ta rashin kawo sha’awa ko rashin haihuwa, yana da kyau a je asibiti don a duba.
A takaice: Idan mace ba ta kawo sha’awa ba, ba yana nufin ba za ta iya samun ciki ba. Amma yana iya rage damar ciki saboda bushewa da ƙarancin ruwan jiki. Mafi muhimmanci shine a tabbatar da lafiyar jiki da natsuwa yayin jima’i.
Ayi sharing pls