WM Hausa

WM Hausa News and Media Company

Hukumar EFCC ta cafke sale Mamman da aka yanke wa hukuncin shekaru 75 a gidan yariRohotanni sun nuna cewa an k**a tsohon...
19/05/2026

Hukumar EFCC ta cafke sale Mamman da aka yanke wa hukuncin shekaru 75 a gidan yari

Rohotanni sun nuna cewa an k**a tsohon Ministan na wutar lantarki ne a yankin Rigasa da ke jihar Kaduna

KARKA KAINI BANGO: Gwamna Abba ya gargadin Kwankwaso.Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani ga tsohon...
18/05/2026

KARKA KAINI BANGO: Gwamna Abba ya gargadin Kwankwaso.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani ga tsohon jagoransa kuma wanda ya dauke nauyinshi a baya, Rabiu Musa Kwankwaso, kan “yawan s**ar da yake yi masa,” inda ya ce kada ya dauki shirunsa a matsayin tsoro ya kuma ja masa kumne da cewa kada kwankwaso ya kaishi bango

Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi State ta bayyana goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar, Adamu Aliero, a matsayin dan takarar...
18/05/2026

Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi State ta bayyana goyon bayanta ga tsohon gwamnan jihar, Adamu Aliero, a matsayin dan takarar hadin kai (consensus candidate) na kujerar Sanatan Kebbi Central.

Jam’iyyar ta tabbatar da hakan ne bayan gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana, inda mambobi da shugabannin jam’iyyar s**a amince da Aliero a matsayin wanda zai wakilci APC a zaben Sanatan da ke tafe.

APC ta ce an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali da fahimtar juna, tare da jaddada kudurinta na hadin kai da tabbatar da nasara a babban zaben mai zuwa.

APC TAYI AMAI TA LASHEJam’iyyar APC ta soke sak**akon zaɓen fidda gwani na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a Plateau State,...
18/05/2026

APC TAYI AMAI TA LASHE

Jam’iyyar APC ta soke sak**akon zaɓen fidda gwani na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a Plateau State, inda ta ayyana ɗan majalisar mai ci a yanzu, Yusuf Gagdi, a matsayin sahihin wanda ya yi nasara.

APC ta sauya sak**akon zaɓen fidda gwani na mazabar Pankshin/Kanke/Kanam a Jihar Plateau, tare da tabbatar da cewa Hon. Yusuf Gagdi ne ya lashe zaɓen.

Rundunar Sojin Najeriya da Amurka sun kashe sama da ‘yan I£IS 20 a sabon farmaki a BornoHedikwatar Tsaro ta Najeriya (DH...
18/05/2026

Rundunar Sojin Najeriya da Amurka sun kashe sama da ‘yan I£IS 20 a sabon farmaki a Borno

Hedikwatar Tsaro ta Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa an kashe fiye da ‘yan ta’addan I$IS/I$WAP guda 20 a wasu hare-haren sama da aka kai tare da haɗin gwiwar sojojin Amurka a yankin Metele, jihar Borno.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai na Tsaro, Samaila Uba, ya fitar a ranar Litinin, ya ce farmakin ya biyo bayan gano taruwar da kuma motsin ‘yan ta’adda a yankin.

Sanarwar ta bayyana cewa: “Ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa sun biyo bayan kawar da kwamandan I$IS, Abu-Bilal al-Minuki, kuma wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi na daƙile hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda, tare da kore su daga fagen yaƙi da hana su samun mafaka a cikin Najeriya.”

A cewar sanarwar, wannan farmaki na cikin matakan da ake ɗauka domin ci gaba da raunana ƙungiyoyin ta’addanci a arewa maso gabashin ƙasar.

Labari da Dumi-Dumi  Sojojin Najeriya da na Amurka sun kai sabbin hare-haren sama kan mayaƙan IS.
18/05/2026

Labari da Dumi-Dumi

Sojojin Najeriya da na Amurka sun kai sabbin hare-haren sama kan mayaƙan IS.

Kotu a Abuja ta ba tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Belin akan Naira Miliyan 100Wata babbar kotu da ke Abuja ta ba...
18/05/2026

Kotu a Abuja ta ba tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, Belin akan Naira Miliyan 100

Wata babbar kotu da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a kan kuɗin Naira miliyan 100, bisa zargin da ake yi masa na karya tsaron ƙasa.

Alƙalin kotun, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta bayyana cewa an amince da belin ne tare da sharaɗin cewa wanda zai tsaya masa dole ne ya kasance mazaunin yankin Maitama ko Asokoro da ke birnin Abuja.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa 18 ga Mayu, 2026 ita ce farkon watan Dhul-Hijjah, yayin da za a gudanar da Ba...
17/05/2026

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana cewa 18 ga Mayu, 2026 ita ce farkon watan Dhul-Hijjah, yayin da za a gudanar da Babbar Sallah a Najeriya a ranar 27 ga Mayu, 2026.

Dan majalisar wakilai na tsawon shekaru 16 ya rasa tikitin sa, a Jigawa A jihar Jigawa, wani sauyi mai girma ya faru a s...
17/05/2026

Dan majalisar wakilai na tsawon shekaru 16 ya rasa tikitin sa, a Jigawa

A jihar Jigawa, wani sauyi mai girma ya faru a siyasar jam’iyyar APC, inda Hon. Sa’idu Yusuf Miga, wanda ya shafe wa’adi hudu a Majalisar Wakilai, ya rasa tikitin sake tsayawa takara gabanin zaɓen 2027.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na zuwa ne yayin shirye-shiryen jam’iyyar na tunkarar zaɓe mai zuwa.

Atiku ya  soki sabon yunkurin Gwamnati na neman rancen Dala Biliyan 1.25 daga Bankin DuniyaTsohon Mataimakin Shugaban Ƙa...
17/05/2026

Atiku ya soki sabon yunkurin Gwamnati na neman rancen Dala Biliyan 1.25 daga Bankin Duniya

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan rahotannin cewa Gwamnatin Tarayya na tattaunawa da Bankin Duniya domin samun sabon rancen dala biliyan 1.25. Idan aka kammala, zai kasance ɗaya daga cikin manyan bashin da gwamnati mai ci ta karɓa.

Atiku ya bayyana cewa yana ganin ya k**ata a fi mayar da hankali kan cimma nasarori maimakon ƙara yawan basuss**a.

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da dakatar da jarumi Adam Garba (Raba Gardama) da jaruma Amina Uba (Rani)...
17/05/2026

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da dakatar da jarumi Adam Garba (Raba Gardama) da jaruma Amina Uba (Rani) daga harkokin fim har na tsawon shekara guda.

Ko wannan matakin yayi dai dai?

Address

No. 2 Mechanic Village Road

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when WM Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share