29/03/2026
SAKON DA MUTANEN TIKTOK S**A KASA FAHIMTA A WANNAN BIDIYON NA CIN MUTUNCI.
Yanzu ina scrolling a TikTok sai na ci karo da wani bidiyo mai tayar da hankali. Mace ce dauke da karamin yaro a hannunta tana bara a t**i da Hijab dinta tana magana da Hausa. Sai wata mota ta tsaya, a cikin motar naji muryar mutane biyu (mace da namiji) suna turanci.
Abin takaici da cin mutunci, sai s**a dauko Co*d*m s**a bata. Ita kuma bata san menene ba amma ta karba. Abin da yafi sosa min rai shine; tana karba, yaron hannunta ya kawo hannu yana ja yana kaiwa bakinsa da niyyar a zaton sa wani abin ci ne 😭 Abin bakin ciki, mutanen motar suna ce mata ta kai wa mijinta ya rika amfani da shi.
Na shiga comment section naga mutanenmu suna ta zagin mutanen motar, amma duk bincikena babu mutum daya da ya fahimci danyen sakon da suke son isarwa ta hanyar wannan cin mutuncin, Ga abubuwan da na dauka kuma haka abin yake:
1. Bautar Da Yara Wajen Neman Kudi: Yaga yaro karami a hannunta amma tana bara da shi a cikin rana, ina baban yaron yake? Shin bai shirya daukar dawainiyar yara ba ne yayi aure? Shin muna haifar yara ne domin su zama Engine din buga kudi a kan t**i? Bara haramun ce a Musulunci, shin menene amfanin irin wannan auren?
2. Mu Muke Zubarwa Kanmu Mutunci: Mutanenmu har yanzu da sauranmu. Lokuta da yawa mu da kanmu muke zubar da mutuncinmu a idon duniya, sannan idan an yi mana rashin da'a mu ji haushi.
3. Kariyar Gida: Idan da bata fita tana bara ba, wallahi bai isa ya je har gidanta ya yi mata wannan rashin mutuncin ba. T**i gidan wulakanci ne, duk wanda ya ajiye kimarsa a t**i, kowa yana da damar taka ta.
4. Wane Irin Miji Ne A Gida? Namijin da zai kwanta a gida, ya turo matarsa da jininsa suna tura kofaton neman abinci a t**i, wallahi ya rasa kwarjini da matsayinsa na jagora a Musulunci.
5. Kisan Makomar Yaro: Wancan yaron da yake kai Co*d*m bakinsa yana zaton abinci ne, an riga an kashe masa kwakwalwa. Ya taso ya ga mahaifiyarsa tana mika hannu, don haka gobe shi ma mika hannun zai yi.
Bana goyon bayan ko wane irin rashin mutunci, amma dole mutum shi ma ya kare mutuncin kansa, kafin ya nemi Allah Ya kare masa.
A fada tsakaninmu da Allah, shin laifin mazan da suke yi musu ciki ne su watsar, ko kuma laifin matan ne da suke amincewa da irin wannan rayuwar?
Allah yasa mudace.
Daga:-
UMAR ALIYU DAHIRU