Ofishin Shugaban Maaikata na jihar Kano ya tabbatar da nadin Hajiya Habiba Abubakar Balarabe a matsayin darakatar sashin kula da shirye shirye na nan gidan Radio Kano.
Da yake mika mata takardar nadin a ofishinsa shugaban gidan radio Alhaji Adamu Abubakar Rano ya bayyana nadin nata da cewar abune da ya dace bisa la’akari da kokarinta wajen gudanar da aikinta.
Alhaji Adamu Abubakar Rano ya taya ta murna tare da jan hankalinta da ta kara kokari wajen gudanar da aiyukanta.
Da take jawabinta jimkadan bayan karbar takardar sabuwar daraktar sashin shirye shiryen ta nan Gidan Radio Kano Hajiya Habiba Abubakar Balarabe ta godewa Allah bisa wannan dama da ya bata tare dayin alkawarin yin iyakar kokarinta domin ganin ta baiwa marada kunya.
Hajiya Habiba Abubakar Balarabe ta maye gurbin tsohon daraktan sashin ne Malam Nuhu Gudaji wanda yayi ritaya bayan kammala wa’adin shekaru talatin da biyar yana aikin gwamnati.
23/08/2024
Jawabin tsohon daraktan shirye shirye kenan Malam Nuhu gudaji lokacin da yake jawabin bankwana bayan da ya kammala aiki da Hukumar gidan Radio Kano a Ranar TALATA 21/8/2024
08/06/2024
SHIRIN Tambayoyin Masu Sauraronmu - Radio Kano NA F.M.YAKOMA DUK RANAR LAHADI DA KARFE 9:00 NASAFE
28/04/2024
ZAKU IYA AIKOMANA DA TAMBAYOYINKU AKAN MA'AIKATANMU DA YADDA AKE GUDANAR DA AIKI A RADIO KANO TA WANNAN SHAFIN
02/06/2023
Auwalu dandarman din matawallen hadejia - yayinda yake gabatarrda shirin zabisonka
14/05/2023
Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un
ALLAH yayiwa daya daga cikin ma'aikatan gidan radio Kano Hajiya fatima babagana rasuwa a yau lahadi 14/5/2023
Za''ayi jana'izarta a gidansu dake sharada kusada unity bank da karfe 4:00pm
Be the first to know and let us send you an email when Tambayoyin Masu Sauraronmu - Radio Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.
Contact The Business
Send a message to Tambayoyin Masu Sauraronmu - Radio Kano: