30/07/2023
A WANNE MATAKI KAKE A "THE SIX WEALTH ARCHETYPES"?
Shahararren masani Dan Lok ya nuna ɓangarorin da neman arziƙin mutum yake tafiya wanda ya yi wa laƙabi da "The Six Wealth Archetypes" a cikin littafinsa mai suna Unlock It.
Ga su kamar haka:
1. THE CAGED LION
Kana da ƙarfi, ilimi da basira, amma sai aka kulle ka a wani yanki ana bautar da kai tare da ba ka ɗan wani abu da ake ƙira albashi wanda kwata-kwata ba ya isarka, amma saboda kana tsoro ka bar aikin ka nemi na kanka, sai ka zauna don dole aka ci gaba da bautar da kai.
Wannan shi ne abun da aka yi wa zaki. An kamo shi daga daji an kulle shi a wani keji ana ba shi nama kaɗan-kaɗan duk da cewa yana da ƙarfi da izza. A maimakon ya yi kukan kura ya fita ya nemi na kansa wanda zai ishe shi, amma sai yake tsoro idan ya fita a nan bai san inda zai je ba. Ya bari an kulle shi a keji ana amfani da shi ana samun kuɗi.
2. THE CHAINED MAGICIAN
Kana da basira da fiƙira sosai, amma sai ake daƙile duk wani ƙoƙarin da kake yi don ganin ka ƙirƙiri abubuwan zamani. Mutanen garinku suna cewa ka fiye nuna cewa kai me basira ne, ta yaya za ka ce za ka iya ƙera jirgin sama, ko wayar hannu, ko manhajar na'ura da sauransu. Ai kawai ka daina nuna cewa kana da basira, ka manta da mafarkin da kake yi na zama wani abu a rayuwa.
Haka ake yi wa matasa masu fiƙira. Ana sare musu gwiwa cewa ba za su iya komai ba tunda su ba Turawa ba ne. Ana ƙaryata fiƙirar da Allah Ya ba su ana sare musu gwiwa tare da daƙile duk wani bincike na ilimi da za su yi. Sai ka ji an ce, "Kai har ka isa ka ce za ka iya ƙirƙira abun da Turawa suke ƙerawa?" Idan kuma ka yi sai a ce, "Ai wahalar banza kake sha, wannan ɓata lokaci ne kawai, ka bari ka koma aikinmu na gargajiya." Suna ci gaba da sare maka gwiwa cewa ba za ka iya kawo wani canji a yankinku ko duniya ba.
3. THE HUSTLING TREASURE HUNTER
Kai ne ka kutsa cikin duniya neman kuɗi, neman abun da za ka rufa wa kanka asiri. Duk da ka ƙira kanka ɗan fafutuka, amma kana yawan sarewa da zaran ka ji ƴar wahala ko kuma ka ga kamar ba za ka iya yin wani abu ba. Kana yawan sarewa da zaran ka fara nema, kana yawan kawo ƙorafe-ƙorafe da excuses a matsayin dalilan da ya sa kake faduwa.
Idan aka ba ka wata idea sai ka ce ai ba ka da lokaci ko kuɗi. Idan aka ce ka nemi ilimin wani abu sai ka fake da cewa ya yi tsauri ko kuma babu lokaci. Kana yawan ƙorafi amma ba ka amfani da wata dama don kai ma dama, kai dai kullum kana ikirarin cewa fafutuka kake amma ba da gaske kake ba.
4. THE INNOCENT PRISONER
Ka gama karatu ka samu aiki a lokacin da kake matashi, amma bayan shekaru sun ja kuma nauyi ya ƙaru, sai abubuwa s**a fara tafiya a baibai. Ga shi nan dai kana samu ba laifi amma ba ya isar ka, kuma ba ka iya wata sana'a ba da albashi kawai ka dogara. Shi ke nan, sai ka fara ganin abubuwa suna tafiya a baibai.
5. THE SUCCESSFUL CASTAWAY
Kana ji a ranka duniya ta yi watsi da kai don ba ka da wani "value", amma duk da haka kana gwagwarmayar neman na kai wa bakin salati. Zaman kaɗaici ya dame ka domin kullum a cikinsa kake. Ba ka da wani farin ciki saboda keɓanta da ka yi daga cikin mutane, ko kuma dai rashin "value" ɗin ne ya janyo maka keɓanta daga mutane, ƴan'uwa da sauran abokai.
6. THE UNFULFILLED KING
Duk da kasancewarka sarki wanda ya mallaki tarin dukiya da kayan alatun duniya, amma har yanzu kana ji ba ka ƙoshi ba. Kullum kana cikin tunanin yadda za ka ƙara yawan mamaye wasu yankuna, ninka yawan arziƙinka, da faɗaɗa hanyar da za ka ƙara tara dukiyoyi. Duk da cewa ba ka rasa komai ba, amma kullum kana jin ƙishi.
——————————————————
Idan ka nutsu ka karanta wannan abun da kyau kuma ka nazarce shi da kyau tare da faɗaɗa tunaninka, za ka gano cewa haƙiƙa kai ma ka taɓa faɗawa cikin ɗaya daga cikin waɗannan matakan ko kuma yanzu kana kai.
Idan duk ba haka ba ne, ka tsaya ka yi nazarin amfani da rashin amfanin kasancewa a cikinsu, sannan ka yi wa kanka karatun-ta-nutsu don gujewa faɗawa.
Allah Ya fishshe mu, amin.
✍ Muhammad Auwal Ahmad ( )
CEO, Flowdiary
30th July, 2023