
09/07/2025
NEMAN ILIMI: Kullum sai ta shafe tsawon kilomita 3 zuwa 4 a kasa kafin take isa Makarantar Firamarensu, kuma duk da haka ita take riga kowa zuwa Makarantar
An gano dalibar da take riga kowa zuwa makarantar firamaren Irshadul Ibadi Sani Mashall dake karamar hukumar Kura a jihar Kano.
Tana isa makaranta tun kafin karfe bakwai na safe.
Wannann Malamin mai suna Mai Unguwa Sunusi Sikifa Malami Makarantar Firamare ne kuma shugaban makaranta ne a karamar hukumar Garun-Malam, ya fito kan hanyar zuwa tasa makarantar sai ya riske ta a kofar makarantar Firamaren su yarinyar waro Irshadul Ibadi Sani tana dakon a zo a bude kofar shiga makarantar ta su domin daukar darasi.
Daga Dantala Uba Nuhu Kura