Sirrin zuciya

Sirrin zuciya wannan "page" zairinka kawo muku kalaman soyayya da labarin littafi

04/10/2024

Kaso wani aikine
Aqaunaceka rabone ko dacene
Aqaunaceka ruhinka yakarbi wannan qaunan aljannan duniya kenan

Sirrin zuciyar mace.......Kalamai na daga cikin abu mafi sauƙi dake saurin narkar da zuciyar mace. Da kalamai za ka iya ...
14/09/2023

Sirrin zuciyar mace.......

Kalamai na daga cikin abu mafi sauƙi dake saurin narkar da zuciyar mace.

Da kalamai za ka iya kalallaɓe zuciyar mace har ka yi dabaibayi ma rayuwarta.

Domin ita mace kunnuwanta na daga cikin abu mafi sauri da sauqin isar da saqo ma zuciyarta, shi yasa cikin sauqi da kalamai zata aminta da kai, zata iya mallaka maka kanta, dukiyarta ko a yaudareta.

Daga cikin sirrin zaman lafiyarka da mace shi ne ko da bayan kunyi aure, ka kasance mai yawan furta mata kyawawan kalamai na soyayya, yabo ( ga hali, sura, etc), gwaɗi, lallaɓi, godiya, kirari etc.

Ƙarancin wadannan kalaman na sa zuciyar mace shiga damuwa, yakan sa ta nisanci miji, dan a gani da tunaninta tunda kabar furta kalamai irin haka baka sonta ko kabar sonta ne.

✍️ Fatimah Chikaire

Tayaya kuke tsammanin samun yadda kuke so alhali bakwa abunda ya dace ? Mata na son mazaje su basu kulawa yadda musulunc...
23/08/2023

Tayaya kuke tsammanin samun yadda kuke so alhali bakwa abunda ya dace ?

Mata na son mazaje su basu kulawa yadda musulunci ya tanadar, sai dai kuma su matan ba sa son bi da yin yadda musulunci yace suyi ma mazajen.

A yayin da su kuma mazajen ke son matan kula da su, su girmama su, su musu biyayya alhali sun kasa bama matan kulawa irin yadda musulunci ya umurce su da yi.

Kowa yasan matsalar sa kuma yasan abunda ya rataya akan sa, mai zai hana bazaku gyara kuyi abunda ya dace ba dan samun zaman lafiyar ku ?

✍️ Fatimah Chikaire@@@

05/05/2023

اللهم صلي وسلم على نبينا محمد

03/09/2022
KOWA YA DIBA DA ZAFI // 24⭐ Ya ambata miki cewa yana ƙaunarki? Wannan fari ne don wata maganar soyayya da duk wasu kyaut...
14/08/2022

KOWA YA DIBA DA ZAFI // 24

⭐ Ya ambata miki cewa yana ƙaunarki? Wannan fari ne don wata maganar soyayya da duk wasu kyaututtuka da yake ba ki kar ki taɓa tsammanin cewa kin same shi a hannu.

⭐ Ba zai taɓa zama a hannunki ba matuƙar babu wata magana a tsakaninsa da mahaifanki, in dai ya ce yana son ki to haɗa shi da mahaifanki tun farko, in ba haka ba za ki yi nadama ba ƙarama ba.

Zamu cigaba insha Allahu.

Rubutawa:- Baban Manar.
Gabatarwa:- Isah Abdullahi Isah

07/08/2022

KOWA YA DIBA DA ZAFI // 30

⭐ Soyayyar da kuke faɗi kafin aure daban ce, don ita ta faranta rai ce da baki ko da zuciya, ta aure kuwa aiki ake yi ba ƙarami ba, komai a aikace ake yinsa, in kika sa rai da samun wadancan maganganun na kafin aure ba tare da kin zage dantse ba, to za ki ɓata wa kanki ne lokaci.

⭐ Ki sani, komai ya canza yanzu, muguwar sha'awar saduwa ta gushe, saura fuskantar ƙalu bale na rayuwa, yi ƙoƙari ki san abin da yake so da wanda ba ya so.

Zamuci gaba insha Allah

Rubutawa:- Baban Manar.
Gabatarwa:- Isah Abdullahi Isah

29/07/2022
Wannan shine group dinmu na Whatsapp
28/02/2022

Wannan shine group dinmu na Whatsapp

WhatsApp Group Invite

Address

Kaduna

Telephone

+2349086213111

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sirrin zuciya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sirrin zuciya:

Share