29/10/2025
                                            Take: Asibitoci Marasa Lasisi Sun Yawaita a Kaduna – Rahoto
Daga Nana Bashir Saleh
Kaduna, Najeriya – Wani tsohon jami’in da ya taɓa shiga aikin tantance asibitoci a fadin jihar Kaduna ya bayyana cewa akwai yawaitar asibitoci da cibiyoyin lafiya marasa lasisi da ke aiki ba bisa ƙa’ida ba a fadin jihar.
A cewar sa, a shekarar 2011/2012, sun sami cikakken jerin sunayen asibitocin masu zaman kansu da ke aiki a gundumomi 255 na kananan hukumomi 23 a jihar. Sai dai yayin da s**a fita domin tabbatar da ingancin wannan jerin sunaye, sun gano cewa jerin da gwamnati ke da shi bai kai kashi 15 cikin 100 na adadin ainihin cibiyoyin lafiya da ke aiki ba.
“Yawancin asibitocin da muka gani suna aiki ba tare da lasisi ko ƙwararrun ma’aikata ba,” in ji shi.
A cewar sa, abin da ya fi ba su mamaki shi ne abin da ya faru a wani ƙauye da ke cikin karamar hukumar Birnin Gwari, inda s**a gano wani asibiti da wasu maza biyu daga Kudu maso Gabas ke gudanarwa.
“Da muka isa wurin, ɗaya daga cikinsu ya gudu, muka k**a ɗaya. Abin mamaki, mutumin bai iya magana da Turanci yadda ya k**ata ba, kuma bai san sunan allurar da yake riƙe da ita ba. Daga baya muka gano cewa bai taɓa halartar makaranta ba,” in ji shi.
Rahoton ya nuna cewa irin wannan yawaitar asibitoci marasa lasisi na faruwa ne sak**akon raguwar ingancin asibitocin gwamnati, raunin hukumomin da ke sa ido, da kuma rashin tsarin daidaito a harkar lafiya a jihar.