
21/09/2025
AL'UMMAH RAHAMA NE
A wannan rayuwan idan kaga mutane na tururuwa zuwa gareka, mutane na son zuwa kusa da kai, mutane na son mannuwa dakai toh tabbas Allah ya azurtaka da wata ni'ima ko dai ta dukiya, Ilimi, Mulki ko Sarauta, koma Allah ya hada maka gaba daya.
Ya kai dan'uwa idan Allah yayi maka daya daga cikin ni'imominsa a rayuwa toh ka gode masa ta hanyar anfani da wannan ni'imar da ya maka wurin kyautatawa Al'ummah ko yin abinda Allah yakeso kuma ya aminta dashi.
Kada kayi anfani da ni'imar ko wata dama da Allah ya baka anan duniya ka wulaqanta Al'ummah da kake rayuwa tare dasu, saboda cikin qanqanin lokaci Allah yana iya karbe ni'imar ko damar ya baiwa wani wanda baka taba tunanin zai iya samu ba, dama kai dinma ba wayonka ko dabararka ko qarfinka ne yaba ka.
NI'IMAH TA DUKIYA
Dukiya tana daya daga cikin ni'imomin da Allah ke yiwa wasu daga cikin bayinsa anan duniya kuma daya ce daga cikin ni'imomin da idan Allah yayi maka toh mutane zasuyi tururuwa zuwa gareka musamman ma idan ka kasance mai budadden hannu.
Idan Allah yayi maka ni'ima ta dukiya kayi iyakan qoqarinka ka kyautatawa Al'umma da wannan dukiyar sannan kayi iyakan qoqarinka ganin ka aikata abinda Allah yakeso da wannan dukiyar.
Kada kabi zugin shaidan da shaidanu wadanda zasu riqa fada maka cewa: ''mutanen nan sunzo su qarar maka da abinda ka tara'' ko ''suna daura maka nauyinsu'' ko "kaifa ba Gomnati bane" ko "Mutanen nan basu tayaka tara dukiyar ba'' dss...
Kasani ko kayi abinda ya dace da dukiyar ko karkayi dayan biyu sai ya faru: kodai dukiyar ta qare ta barka ko kuma kai Ka mutu ka bar dukiyar kuma sai Allah ya tambayeka akai gaba daya.
NI'IMAH TA ILIMI
Ilimi shima daya daga cikin ni'imomin da Allah yake yiwa wasu daga cikin bayinsa ne inma na addini ko na wani fanni na rayuwa wanda kuma kesa Al'umma suyi tururuwa zuwa garesu musamman ma idan Ilimin ya zama na addini ne ko na dukka biyu.
Idan Allah ya baka dimbin Ilimi na Addini ko na wani fanni na rayuwa toh kayi iyakan qoqarinka wurin anfanarda al'umma da wannan Ilimin kuma kayi iyakan qoqarinka wurin aiki da wannan Ilimin ta hanyar da Allah yakeso.
Kada Ka yarda iliminka ya samar maka da daya daga cikin wadannan abubuwan acikin rayuwarka
1. Girman Kai
2. Raina kowa
3. Kowa Jahili ne
4. Kaine kadai Masani
5. Too Harsh
6. kowa batacce ne
7. Kowa dan wuta ne, dss...
Ilimin da Allah ya baka abin tambaya ne a gareka a ranar Hisabi, Allah yasa mudace da abinda yake dai dai kuma ya yarda dashi.
Bari mudan kurbi koku mu hadu a Rubutu na gaba .....
✍️: Muhammad Khalid Hussaini
(De GENERAL)
21/09/2025