
13/07/2025
Na rubuta Sheikh Mal. Tijjani Usman Zangon Bare-bari shi ne farkon wanda ya fara tara jama'a yana karantar da tafsirin Alkur'ani mai girma a garin Kano. Akwai daga wasu sashen ƴan uwa Ƙadirawa, suna cewa mu kara bibiyar tarihi. Domin suna ganin Malam Nasiru Kabara shi ne ya fara tafsirin a gidan Ciroma Muhammadu Sunusi I sarkin Kano na goma sha ɗaya a jerin Fulani.
Gaskiya babu tabbacin tafsirin ana tara mutane domin sauraro irin yanda ake yi yanzu. Malam Nasiru Kabara, shi ya fara gabatar da tafsirin Alkur'ani na tara mutane suna sauraro a irin wanda a ke yi yanzu a cikin shekarar 1954, a gidan masarautar Kano.
Shi Sheikh Malam Tijjani Usman Zangon Bare-bari ya fara gabatar da tafsirin Alkur'ani na tara mutane suna sauraro irin wannan na da ke yi a yanzu a cikin shekarar 1950, shekaru 75 kenan .
✍️