Hausa24

Hausa24 HAUSA24, Za Ta Kasance Wata Kafar Yada Labarai Da Za Take Kawo Muku Labarai Da Dumi-Dumin Su, Cikin Harshen Hausa!

Fagen harkar yada labarai fage ne mai fadin gaske, da dama sun zo sun tafi bayan sunyi abinda s**a yi, wasu ma sun zo basu yi komai ba sun tafi ba tare da ko labarinsu an ji ba. Mun sani kuma mun aminta igiya biyu ce kadai za ta iya rike mu, har mu ma muyi abinda muka yi. Wadannan igiyoyi su ne: GASKIYA da GOYON BAYANKU, za mu rayuwa idan har akwai wadannan igiyoyi. H24 za ta zamo wata takar yakin

Hausawa ‘yan Nijeriya, domin yakar karya da kare gaskiya a kodayaushe, koda kuwa a hannu masu mulki ne. Ta haka ne kadai za mu cimma burinmu da naku baki daya.

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Gyaran Alau Dam Akan Kuɗi Naira Biliyan 80 Nan Da 2027, Don Inganta Noman Rani Da Samar ...
08/08/2025

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kammala Gyaran Alau Dam Akan Kuɗi Naira Biliyan 80 Nan Da 2027, Don Inganta Noman Rani Da Samar Da Wutar Lantarki

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa aikin gyare-gyare da fadada Alau Dam da ke jihar Borno, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 80, zai kammala nan da shekarar 2027. Ministan Ruwa da Tsabtace Muhalli, Farfesa Joseph Utsev, ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar aiki da ya kai wurin aikin a garin Alau, kusa da Maiduguri. Ya ce an fara aikin ne da amincewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu karkashin shirin Renewed Hope Agenda, domin Dan din ya zama mai amfanarwa sosai, ciki har da ban ruwa don bunkasa noman rani da kuma shirin samar da wutar lantarki a nan gaba.

Ministan ya bayyana cewa aikin ya kasu kashi biyu, inda kashi na farko zai kare a watan Satumba na wannan shekara, domin rage hadarin ambaliyar ruwa a wannan damina. Kashi na biyu kuma zai fara a watan Oktoba kuma ya kammala a watan Maris 2027, wanda zai kai ga kammala sake ginawa da fadada Dam din. Ya ce, bayan kammala aikin, Dam din zai kara inganta samar da ruwan sha ga Maiduguri da kewaye, ya tallafa wa noman rani, tare da bai wa yankin damar samar da wutar lantarki ta hanyar ruwa.

Farfesa Utsev ya gode wa Shugaba Tinubu da Gwamna Babagana Umara Zulum bisa jajircewa wajen ganin aikin ya tabbata, yana kuma kira ga manoma a yankin su daina shuka amfanin gona a gefen Dam din domin kauce wa matsaloli yayin aikin. Ya kuma shawarci mazauna yankin da su kwantar da hankalinsu kan yiwuwar ambaliya, yana mai bayyana cewa aikin na da matuƙar muhimmanci wajen magance matsalolin ruwa da inganta harkokin noma a Borno da ma kasa baki daya.

Shugaba Tinubu Ya Taya Dalibai Uku ‘Yan Arewa Murna Bisa Nasarar Da S**a Samu a Gasar Duniya Ta TeenEagleShugaban Ƙasa B...
06/08/2025

Shugaba Tinubu Ya Taya Dalibai Uku ‘Yan Arewa Murna Bisa Nasarar Da S**a Samu a Gasar Duniya Ta TeenEagle

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu mai shekaru 17, Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15, da Hadiza Kashim Kalli murna bisa nasarar da s**a samu a gasar TeenEagle ta duniya da aka gudanar a birnin London, Ƙasar Ingila. Nafisa ce ta lashe kyautar gwarzon daliba a fannin ƙwarewar harshen Turanci, yayin da Rukayya ta zama ta farko a muhawara, Hadiza kuma ta samu kyautar zinariya a matsayin mai hazaka.

Shugaba Tinubu ya jinjinawa waɗannan matasa na Najeriya da s**a ɗaga tutar ƙasa a idon duniya, yana mai cewa wannan nasara alama ce ta hasken makomar ƙasar. Ya kuma yaba da irin gudunmawar cibiyoyin ilimi da gwamnatocin jihohi wajen haɓaka ƙwarewar ɗalibai, yana mai cewa hakan na nuna ingancin tsarin ilimi da ƙasar ke da shi wajen haifar da matasa masu ƙwarewa da basira.

Shugaban ya ƙara jaddada cewa ilimi ginshiƙi ne na ci gaban ƙasa, wanda ya sa gwamnatinsa ke zuba jari a fannin tare da cire ƙalubalen kuɗi ga talakawa masu neman ilimi ta hanyar NELFUND. Ya yi kira ga Nafisa, Rukayya da Hadiza da su ci gaba da jajircewa a karatunsu, yana musu fatan samun karin nasarori a gaba.

29/07/2025

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana irin cigaba da aka samu a fannin tsaro, duba da yadda matsalar take a da a Arewa.

Ya yi wannan bayani ne a firar sa da manema labarai, a wajen taron kwanaki biyu na tattaunawa tsakanin gwamnati da ’yan ƙasa da aka shirya a jihar Kaduna, mai taken: Duba Alkawuran Zaɓe: Haɓaka Hulɗar Gwamnati da ‘Yan Ƙasa Domin Ƙarfafa Haɗin Kan Najeriya, wanda Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya.

Tinubu Ya Gwangwaje 'Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen SuShugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu y...
28/07/2025

Tinubu Ya Gwangwaje 'Yan Super Falcons Da Kyautar Dala 100,000 Da Kuma Gida Kowannen Su

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama 'yan rundunar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, wato Super Falcons, da kyautar karramawa ta ƙasa da kuma kyautar kuɗi da ta gidan kwana saboda nasarar su a gasar Kofin Ƙasashen Afrika na Mata (WAFCON), wanda aka gama ranar Asabar, inda s**a ciyo kofin a karo na 10.

A wurin wata babbar walima da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Dutsen A*o a ranar Litinin, Tinubu ya ba da lambar girma ta ƙasa ta Officer of the Order of the Niger (OON) ga kowace daga cikin 'yan wasan su 24.

Haka kuma ya gwangwaje kowace 'yar wasa da kyautar tsabar kuɗi Naira wadda ta yi daidai da Dalar Amurka dubu ɗari ($100,000), da kuma gida mai dakunan kwana uku.

Bugu da ƙari, kowanne daga cikin ma'aikatan kulob ɗin ƙwallon ƙafar an ba shi kyautar dala dubu hamsin ($50,000) (a naira), a matsayin godiya saboda muhimmiyar rawar da s**a taka wajen samun nasarar.

“Wannan ƙungiya ta ƙara janyo wa Nijeriya abin alfahari a duniya," inji Tinubu. “Jajircewar ku da zummar ku da wasan ku sun kasance abin koyo ba kawai ga 'yan wasa masu tasowa ba har ma ga kowane ɗan Nijeriya.

“Na karɓi wannan kofi a madadin dukkanin 'yan Nijeriya, kuma na ce maku: mun gode da sadaukarwar ku da hoɓɓasan ku, da kuma tuna mana da ƙarfin halin 'yan Nijeriya da kuka yi.

“A madadin ƙasar nan da ke cike da godiya, a nan ina bai wa dukkan 'yan wasa da ma'aikatan kulob su 11 kyautar karramawa ta ƙasa mai suna 'Officer of the Order of the Niger' (OON).

“Bugu da ƙari, ina ba da umurnin cewa a ba kowace 'yar wasa da kowane ma'aikacin kulob kyautar gida mai daki uku.

“Wani ƙari kuma shi ne, akwai kyautar tsabar kuɗi a naira wadda ta yi daidai da $100,000 ga kowacce daga cikin 'yan wasa 24, da kuɗi da ya yi daidai da $50,000 ga kowanne daga cikin ma'aikatan kulob su 11.

“Ina ƙara taya ku murna, kuma zan ci gaba da yi maku addu'a. Da wannan, ruhin Nijeriya ba zai gaza ba kuma ba zai taɓa mutuwa ba.”

Shugaban Ƙasar ya ba da labarin yadda mutane s**a riƙa ji a ran su lokacin da wasan ya zo kusan ƙarshe, yana mai nuni da yadda wasan da 'yan wasan s**a riƙa bugawa ya daga ruhin ƙasar nan tare da haɗa kan 'yan Nijeriya a duk inda suke.

Ya ce: “Nasarar ku tana wakilta abin da ya na zarce nasara a wasa. Nasara ce ta bajinta, jajircewa, ɗa'a, da kuma tsayawa kai da fata.

“A gaskiya, da farko ban so na kalli wasan. Ban so na samu hawan jini. Amma sai mutane s**a shigo s**a kamo tashar da ake wasan a talbijin ɗina. Lokacin da aka ci 2-0, sai rai na ya ɓaci , na rasa sukuni.

“Amma ina dai ta kallo da ƙarfin zuciya, da dagewa, da bajinta. To bayan an buga fanariti ɗin nan, sai na ji ƙarfi a rai na, kuma na yi amanna da cewa shi ma ran ƙasar nan ya ƙarfafa.

“Amma fa kun kusa sanya ni na yi ƙarin fushi domin mamar ku (wato Uwargidan Shugaban Ƙasa) tana cikin ɗakin girki, ta kusa mantawa da abinci na.

”Ba ta kallon gasar sai idan namu 'yan matan ne s**a buga wasa. To lokacin da aka busa usur ɗin ƙarshe, sai duk aka ɓarke da murna a duk faɗin ƙasar nan."

Shugaban Ƙasa ya tabbatar wa da kulob ɗin cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da ba su goyon baya da kuma mara wa cigaban harkokin wasanni baya, tare da alƙawarin cewa gwamnatin za ta ƙara zuba jari a harkar ƙwallon ƙafar mata da cigaban matasa a duk faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “Labarin ku labari ne na kyakkyawar fata. Don haka a wannan zamani na Sabunta Kyakkyawar Fata (Renewed Hope), muna taya ku bikin murna ba kawai a matsayin ku na zakarun Afrika ba, har ma gwarzayen mafarkin Nijeriya.”

Wani ƙarin godiya shi ne Shugaban Ƙungiyar a Gwamnonin Nijeriya (NGF), wato Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, shi ma ya bayyana kyautar naira miliyan goma (₦10m) ga kowace 'yar wasa da ma'aikatan kulob ɗin a madadin gwamnoni jihohi 36.

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana 'yan wasan Super Falcons a matsayin abin koyi kuma kyakkyawan misalin bajinta da inganci.

Ta taya su murna saboda wasa mai jan hankali da s**a yi da kuma ƙarfin ruhin su, tana mai bayyana aikin su da cewa “alama ce ta dagewa, aiki tare, da jajircewa."

Kyaftin ɗin Super Falcons, Rasheedat Ajibade, ta ce nasarar da su ta kulob ɗin su ce kuma ta kowace yarinya 'yar Nijeriya ce da ke mafarkin cimma wani gagarumin abu a rayuwa.

Ta ce: “A yau, na tsaya a gaban ku ba kawai a matsayin kyaftin ɗin Super Falcons ba, har ma a matsayin ɗiyar Nijeriya mai alfahari, ɗauke da mafarkai, jajircewa, da ruhin babbar ƙasar mu.

“A madadin ƙawayen aiki na, koci-kocin mu, da ma'aikatan mu, ina bayyana godiyar mu saboda wannan kyakkyawar tarba da aka yi mana da kuma nagartacciyar amannar da kuka nuna mana.”

Da take nanata muhimmancin cin kofin na 10 na gasar WAFCON da s**a yi, kyaftin ɗin ta ce: “Wannan nasara ba kurum a kofi take ba. Shaida ce ta rashin gazawar ruhin Nijeriya. Abin murna ne ga kowace ƙaramar yarinya da ke ƙauyukan mu, garuruwan mu, da biranen mu wadda ke da ƙoƙarin yin mafarki... Wannan cin kofin na 10 naka ne, ya mai girma Shugaban Ƙasa, na 'yan Nijeriya ne, na Nigerians, Super Falcons, Kuma na kowane ƙaramin yaro da ya yi amanna tare da mafarkin zai hau wannan dandamalin wata rana."

Zamu biya bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin Gwamnatin Tarayya tun daga 2015 —TinubuShugaban kasa Bola ...
26/07/2025

Zamu biya bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin Gwamnatin Tarayya tun daga 2015 —Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa kamfanonin samar da wutar lantarki (GENCOs) cewa gwamnatin tarayya za ta biya bashin da suke bin ta bayan kammala cikakken bincike da tantance adadin da ake ikirari. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taro da wakilan kungiyoyin GENCOs a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya ce dole ne a tabbatar da gaskiyar duk wani adadi da za a biya, domin hakan zai zama ginshiki wajen habaka masana’antu da tattalin arziki.

Mai ba Shugaban kasa shawara kan makamashi, Ms Olu Verheijen, ta bayyana cewa gwamnati ta tantance bashin da ya kai naira tiriliyan 4 daga shekarar 2015 zuwa karshen 2023, inda aka riga aka tabbatar da tiriliyan 1.8. Ta ce shugaban kasar ya amince da shirin fitar da takardar biyan bashi na naira tiriliyan 4 domin rage matsin lambar kudin da ke addabar bangaren wutar lantarki, tare da jaddada cewa bashi da aka tantance aka tabbatar ne za kaɗai a biya.

Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yabawa jagorancin Tinubu, inda ya ce a karkashin mulkinsa an samu nasarori da s**a hada da karuwar kudin shiga daga naira tiriliyan 1 a 2023 zuwa tiriliyan 1.7 a 2024, da kuma karin megawatt fiye da 700 ta hanyar shirin PPI.

Manyan ‘yan kasuwa irinsu Tony Elumelu da Kola Adesina sun bukaci gwamnatin ta hanzarta biyan bashin, domin kaucewa rufe masana’antu da durkushewar ci gaban kasa..

Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, inji Ministan Yaɗa LabaraiMinistan Yaɗa Labarai da Wayar da Ka...
23/07/2025

Tinubu Ba Zai Taɓa Tauye ’Yancin Kafafen Yaɗa Labarai Ba, inji Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana da cikakken goyon baya ga ’yancin faɗar albarkacin baki da ’yancin ’yan jarida, tare da fahimtar muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen gina ƙasa.

Da yake jawabi a taron lacca na shekara-shekara na kamfanin jaridar Blueprint wanda aka gudanar a ranar Talata a Abuja, Idris ya ce tun farkon naɗin sa, Shugaba Tinubu ya bayyana masa cewa ya ba shi dama ya yi aikin sa yadda ya ga ya dace a matsayin sa na ƙwararre.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu babban mai goyon bayan kafafen yaɗa labarai ne. Yana da masaniyar cewa kafafen yaɗa labarai suna da matuƙar muhimmanci wajen gina ƙasa, kuma ya sha gaya mini cewa in ci gaba da aiki na yadda na ga ya dace, kasancewa ta ƙwararre.”

Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai taɓa, a kowace hanya ko salo, tauye ko hana ci gaban aikace-aikacen kafafen yaɗa labarai a wannan ƙasa ba. Amma dole ne mu duka ‘yan jarida da masu aikin yaɗa labarai mu haɗa kai, mu bi wannan hanya mai sarƙaƙiya, mu tabbatar da cewa al’umma tana ci gaba da zama cikin haɗin kai, yayin da muke riƙe shugabanni da gwamnati da alhakin aikin su.”

Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen kula da tsarin dimokiraɗiyya, inda ya shawarci ’yan jarida da su kula da rawar da suke takawa domin kada su zama abin da zai jawo ruɗani ko rikici a cikin al’umma.

“A yayin da kuke yin wannan aiki, kuna da babban nauyi na riƙe gwamnati da shugabanni da alhakin aikin su. Amma ko da kuna yin hakan, dole ne ku sani cewa saboda matsayin ku na musamman da rawar da kuke takawa, za ku iya taimaka wa ƙasa matuƙa, amma idan ba a yi taka-tsantsan ba, ayyukan ku na iya cutar da al’umma,” inji shi.

Ya bayyana buƙatar sanin ya kamata da hankali wajen tantance sahihin bayani daga wanda zai iya ɓata zaman lafiya ko raba kan al’umma.

Ministan ya ce duk da ƙalubalen da ke fuskantar fannin yaɗa labarai, akwai haske a gaba domin kafafen sun ci gaba da nuna jajircewa da ɗorewa.

Ya kuma bayyana cewa ba shi ba ne Shugaban kamfanin jaridar Blueprint ba tun bayan da aka naɗa shi Minista.

“Ba ni ne shugaban jaridar Blueprint ba yanzu. Ni ma baƙo ne aka gayyata zuwa wannan taro. Na san cewa a baya ni ne ke gaba wajen shirya wannan taron na Blueprint, musamman tun lokacin da aka kafa ta shekaru 14 da s**a wuce. Dole ne in gode wa waɗanda aka gayyata su haɗu da ni a watan Mayun 2005 domin tunanin fara jaridar Blueprint: Malam Ibrahim Sheme; Manajan Darakta, Malam Salisu Umar; Shugabar Kwamitin Tace Labarai, Hajiya Zainab Okino, da dukkan ma’aikatan jaridar Blueprint.

“Na gode da cigaba da tafiyar da abin da muka faro cikin nasara. Na shekara guda ban ziyarci ofishin ba, amma ina ganin lokaci ya yi da zan yi hakan. Ina so in ga ko har yanzu kuna ci gaba da tafiyar da abin da muka faro. Ina alfahari kuma ina farin ciki da cewa abin da muka fara ya ci gaba da bunƙasa,” inji shi.

Idris ya taya waɗanda s**a samu kyaututtuka murna, inda ya bayyana cewa ba a yi masu kyautar bisa wani son zuciya ko tasiri daga wani waje ba, sai hukuncin jaridar ne kaɗai.

Cikin manyan baƙin da s**a halarci taron akwai Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume; Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin; Ministan Ma’adanai, Dakta Dele Alake; Ministan Raya Noman Dabbobi, Idi Mukhtar Maiha; Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, da babban baƙon jawabi na taron, Farfesa Attahiru Jega.

Waɗannan su ne mutanen da motarsu ta yi haɗari da ta gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa a jiya Lahadi kan hanyar Da...
21/07/2025

Waɗannan su ne mutanen da motarsu ta yi haɗari da ta gwamnan jihar Katsina Umaru Dikko Raɗɗa a jiya Lahadi kan hanyar Daura zuwa Katsina. Su suna komawa Daura daga hanyar Katsina, motar gwamnan kuma na komawa Katsina daga Daura.

📸Hamza Arma Daura

Labarin da ke Bayan Wadannan Hotuna, A Kasar Saudiyya _ Inji Bashir Ahmad Akwai wani labari mai ban sha'awa da ke bayan ...
19/07/2025

Labarin da ke Bayan Wadannan Hotuna, A Kasar Saudiyya _ Inji Bashir Ahmad

Akwai wani labari mai ban sha'awa da ke bayan waɗannan hotuna. An ɗauke su ne yayin taron Future Investment Initiative (FII) da aka gudanar a Riyadh, Saudiyya, a watan Oktoba na shekarar 2021. A gefen wannan taro ne marigayi Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shirya gudanar da wata ganawar ɓangare biyu da Yarima Mai jiran gado, Muhammad bin Salman, a fadar sa ta Al‑Yamamah.

Kamar yadda aka saba, tawagar masu shirya wa Shugaban Ƙasa gaba sun riga sun bar otal ɗin domin shirya wurin taron. Mu kuwa muna zaune cikin motar 'yan jarida, muna jiran Baba ya sauko domin mu wuce fadar. Cikin gaggawa sai aka samu wani saƙo na gaggawa cewa Yarima Mai jiran gado ya nemi a bar Baba a otal, domin shi zai zo da kansa ya same shi a nan, saboda yana ganin Baba tamkar mahaifi ne a gare shi.

Cikin ƴan mintoci kaɗan, jami’an tsaron Saudiyya s**a mamaye otal ɗin gaba ɗaya. Daraktan gudanarwa na otal ɗin tare da duka manyan jami’ansa s**a sauko da kansu domin lura da shirye-shiryen tarbar Yarima Mai jiran gado. Na tambayi ɗaya daga cikin jami’an harkokin masarautar Saudiyya game da wannan al’ada ta ban mamaki, sai ya ce: “Idan Yarima Mai jiran gado zai bar fadarsa ya zo otal domin ganawa da wani shugaba daya kawo ziyara, to hakan na nuni da girman darajar da yake ba Shugabanku.” Ma’aikatan otal ɗin ma sun tabbatar cewa ba a taɓa samun irin wannan lamari ba a tarihin otal ɗin.

Allah ya gafarta wa Baba Buhari.

An saka gawar a mota yayin da aka nufi Daura da ita. Tsohon dogarin marigayin ne wanda ke jagorantar motar da aka ɗauki ...
15/07/2025

An saka gawar a mota yayin da aka nufi Daura da ita.

Tsohon dogarin marigayin ne wanda ke jagorantar motar da aka ɗauki gawar domin yi mata rakiya zuwa inda za a yi masa sallah tare da binnewa a gidansa.

DA DUMI-DUMI: Masu zaman makoki bangaren mata ke rera karatun Al-Qurani a gidan margayi Buhari dake Daura a yayin da ake...
15/07/2025

DA DUMI-DUMI: Masu zaman makoki bangaren mata ke rera karatun Al-Qurani a gidan margayi Buhari dake Daura a yayin da ake jiran isowar gawarsa....

15/07/2025

Wata shira ta Mirgayi Buhari da TTV.

Tawagar kasar Nijar 🇳🇪 bisa jagoranci prime ministan kasar, Ali Lamine Zeine sun iso filin tashi da sauka na Umaru Musa ...
15/07/2025

Tawagar kasar Nijar 🇳🇪 bisa jagoranci prime ministan kasar, Ali Lamine Zeine sun iso filin tashi da sauka na Umaru Musa Yar'adua dake jihar Katsina domin halartar Jana'izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari wanda za'ai da misalin karfe 2:00 na wannan rana a Daura.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa24 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa24:

Share