06/02/2025
🚀 Muhimmiyar Sanarwa Kan Taron Wata-wata na Kamfanin IBIS karo na 57.
An gudanar da taron Wata-wata na Majalisar Zartarwa na kamfanin IBIS karo na 57, cikin nasara a jiya, 5 ga Fabrairu, 2025, a Shafin Kamfanin na Zamani a Manhajar Haɗuwa ta bai ɗaya. Taron ya samu halartar kashi biyu bisa uku na mambobin majalisar, inda aka tattauna muhimman batutuwa masu alaƙa da ci gaban kamfanin tare da cimma muhimman matsaya ✅.
Daga Cikin Manyan Abubuwan da Aka Tattauna a Taron Sun haɗa da:
1. Bayani Kan IBIS Master Plan📜: Shugaba kuma Babban Jami'in Gudanarwar Kamfanin, Mallam Abdulhadi Ya’u Maikawo, ya gabatar da taƙaitaccen bayani kan IBIS Master Plan, wanda ke zama tushe na abun fata ga dukkan mambobin IBIS . Tsarin yana ƙunshe da dabaru, hanyoyi da sharuɗɗa da za su taimaka wajen cimma gajere, matsakaici da dogon zango na burin kamfanin.
2. Shirin Gyara Matsalar Mambobin da Ba Su Da ƙwarin Gwiwa ko kuma suke da rauni: Maimakon cire waɗanda ba sa da kyakkyawar tsayuwa ko ince masu nuna rauni a kamfanin, majalisa ta amince a haɗe su cikin rukuni guda, inda dukkaninsu zasu zaɓi wakili guda ɗaya (1) da zai wakilce a rijistar masu Hannun-jari a kamfanin, hakan na nufin dukkanin abinda ya amince dashi to dukkanin su shine matsayar kuma kamfanin zaiyi amfani da Maganar sa ne kawai a madadin su. Waɗanda abin ya shafa majalisar ta basu adadin kwanaki 10 don kammala kowane irin tsari da kuma bayyanawa kamfani wakilin da s**a zaɓa domin ya wakilcesu.
3. Ci-gaban Kasuwancin IBIS PharmaPlus: Shugaban kamfanin ya bayyana matakan da aka cimma kan shirin buɗe IBIS PharmaPlus, wanda aka tsara za a kaddamar da shi a mako na farko na watan Oktoba na wannan shekara. Wannan shiri yana cikin tsare-tsaren gajeren zango na IBIS kamar yadda yake ƙunshe a cikin IBIS Master Plan.
4. Sabuwar Buƙatar Wani Mai Son Mallakar Hannun Jari: An karɓi buƙatar wani memba da ke son samun hannun jari a IBIS, kuma bayan tsananta tattaunawa, majalisa ta amince a ci gaba da matakai na gaba don tantance shi.
5. Korarren Memban da Aka Sallama daga Kamfanin IBIS: Bisa la’akari da cin amanar kamfani, karkatar da kudaden kamfani bayan aminta da damƙasu gareshi don a taimake shi, ba tare da wani gamsasshen bayani kowa wani ɗaukar lamuni daga gareshi ba tsawon lokaci, ƙin bin ka’idojin sulhu da rashin bin umarnin da aka ba shi don nema Mashi mafita, majalisa ta amince da cire wannlnan memba daga cikin masu hannun jari. Wannan hukunci ya dace da dokokin IBIS da kuma tanade-tanaden dokokin dake ƙunshe a cikin "Companies and Allied Matters Act 2020" ⚖️.
6. Ƙirƙirar Sabbin Kwamitoci: Majalisa ta amince da kafa sabbin kwamitoci guda biyu:
✅ IBIS Master Plan Advisory Committee: Don kula da bunƙasawa da kuma aiwatar da IBIS Master Plan cikin tsari bisa amincewar Majalisar ƙoli.
✅ IBIS Audit Committee: Don inganta saka idanu da bincike haɗi da kula da harkokin kuɗi da tabbatar da ingantaccen tsarin lissafi.
7. Ci-gaban Fasahar Kamfani: Babban Jami’in Fasaha, Jibril Ahmad Kaduna, ya gabatar da cikakken rahoto kan ci gaban sashen fasahar kamfani IBIS. Ya kuma ƙarfafa gwiwar mambobi da su goyi bayan waɗanda ke kokarin kawo sabbin dabarun ƙirƙire-ƙirƙire. Bugu da ƙari, ya sanar da shirin wani taron ilmantarwa, haɗi da bita ga manyan shugabannin IBIS wanda zai gudana ranar Tsabar karfe 8:30 zuwa 10:30 na dare a Manhajar Zoom.
8. Jawabin Rufe Taro da kuma Jan-hankali ga Mambobi: Babban Jami’in Gudanarwar Harkokin Kasuwanci na kamfanin, Shu’aibu Laba Muhammad Kano, ya ja hankulan mambobi da su ci gaba da jajircewa don tabbatar da nasarar IBIS. Ya jaddada irin fafutukar da manyan Jagororin kamfanin suke yi da yadda sukeyin aiki dare da rana don cigaban IBIS ba tare da gajiyawa ba, don haka dole ne duk wani mai hannun jari ya lizintawa kansa halartar taron wata-wata da kuma tanadar muhimman Shawarwari da kuma saka baki yayi gudanar da tattaunawa . Ya kuma kara da jan hankulan mambobi da su daina halartar taro ba tare da cikakken tsayuwa har a kammala taron ba, domin hakan yana haifar da ƙurewar sadarwa ta yadda Basu san ainihin me aka cimma matsaya akansa ba, da rarrabuwar fahimta a wani lokaci.
Daga ƙarshe dai, taron ya kasance muhimmin zama da ya haifar da sababbin tsare-tsare, matakai da sabbin manufofi. IBIS na ci gaba da jajircewa don zama babban kamfani mai tasiri a kasuwanci, kuma muna kiran dukkan mambobi da su ci gaba da aiki tare, goyon bayan shugabanci, da jajircewa don samun nasarar IBIS akan manufofin ta na Alkhairi 💪.
Da ikon Allah duk wanda ya Jajurce kuma ya daure zai Ribatu kuma zai yi alfahari da wannan kamfani. Allah Ya taimake mu, kuma ya Datar damu akan dai-dai.
✍️ Daga:
📢 Sakataren Majalisa
INTIMATE BROTHERS INTEGRATED SERVICES LIMITED