Bello Ida

Bello Ida Labarun gida da na waje

Ta wannan fuskar.
15/04/2025

Ta wannan fuskar.

08/04/2025

Labari mai taɓa zuciya, labarin Jaycee Dogard.

Yarinyar da aka sace tu tana shekara 11.

Labarin gaske ne.

EFCC ta sake k**a Sirajo Muhammad Jaja, babban accountant na Jihar Bauchi, tare da wasu biyu, Aliyu Abubakar da Sunusi I...
08/04/2025

EFCC ta sake k**a Sirajo Muhammad Jaja, babban accountant na Jihar Bauchi, tare da wasu biyu, Aliyu Abubakar da Sunusi Ibrahim Sambo, bisa zargin yin safarar kuɗi da kuma ɗaukar Naira biliyan 70 daga kuɗaɗen gwamnati.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta musanta k**a su, tana cewa wannan lamari yana da alaƙa da siyasa kuma ana ƙoƙarin lalata shugabancin Gwamna Bala Mohammed.

Kungiyoyi k**ar Bauchi Accountability and Truth Awareness Front (BATA) ma sun yi s**a ga EFCC bisa zargin cewa suna yin binciken saboda siyasa. Duk da wannan, EFCC ta ce binciken da take yi yana cikin ƙoƙarin yaƙar cin hanci da rashawa da tabbatar da gaskiya a gwamnati.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta gano wata cibiyar haihuwar jarirai ba bisa ka’ida ba a yankin Ijegun na jihar.Bayan ...
08/04/2025

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas ta gano wata cibiyar haihuwar jarirai ba bisa ka’ida ba a yankin Ijegun na jihar.

Bayan samun bayanan sirri, jami’an ‘yan sanda sun kai samame a wurin a ranar 5 ga Afrilu, 2025, inda s**a k**a mai gudanar da wajen, Mariam Vincent mai shekara 35, da wasu mataimakanta biyu: Orie Ruth mai shekara 23 da Ujunwa Ifeanyi mai shekara 18.

A yayin wannan samame, ‘yan sanda sun ceto mata bakwai da aka sace, waɗanda s**a haɗa da: Precious (24), Magdalene (25), Adaobi (23), Princess (22), Ifeanyi (25), da Amaka (26), tare da yara uku: Destiny (yaro mai shekara 7), Miracle (yarinya mai shekara 5), da Success (yarinya mai shekara 2).

Waɗanda ake zargin sun amsa laifin sace mutanen daga sassa daban-daban na Jihar Legas domin gudanar da wannan cibiya ta haihuwar jarirai.

Gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin Usman Ododo tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun mayar da...
07/04/2025

Gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin Usman Ododo tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, sun mayar da martani mai zafi kan wani iƙirari da Natasha Akpoti ta yi game da wani boyayye shiri na kashe ta.

An daɗe dai ana cacar baki tsakanin shugaban majalisa Godwill Akpabio da Sanata Natasha.

Wasu ƴan bindiga daɗi da ba a san ko su waye ba, sun kashe eani ɗan ƙasar China da ƙarin wani ɗansanda.Kisan ya faru ne ...
07/04/2025

Wasu ƴan bindiga daɗi da ba a san ko su waye ba, sun kashe eani ɗan ƙasar China da ƙarin wani ɗansanda.

Kisan ya faru ne a Jihar Abia, har yanzu dai ƴansanda na binciken maharan.

Ƴanbindiga sun yi garkuwa da da mutum Hamsin a Jihar Katsina.Al'ummar ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴan...
07/04/2025

Ƴanbindiga sun yi garkuwa da da mutum Hamsin a Jihar Katsina.

Al'ummar ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina sun ce ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyukanƙauyuka, inda s**a sace sama da mutum hamsin waɗanda s**a haɗa da mata da ƙananan yara.

Barayin sun kashe wasu ƙarin mutum shidda, bayan sun kai wani sabon hari a ƙaramar hukumar Dandume.

08/02/2025

"Na Fi Messi, Pele Da Maradona Iya Kwallon Kafa", Inji Cristiano Ronaldo

Ina gaskiyar wannan maganar?

Ku faɗi ra'ayoyinku a Comment Section.

Ra'ayoyinku
08/02/2025

Ra'ayoyinku

"Na Fi Messi, Pele Da Maradona Iya Kwallon Kafa", Inji Cristiano Ronaldo

Ina gaskiyar wannan maganar?

Ku faɗi ra'ayoyinku a Comment Section.

Address

Sokoto

Telephone

+2349075676327

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Bello Ida posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Bello Ida:

Share