Fikrah TV

Fikrah TV Don Gyaran Tunaninku
(1)

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kaddamar da Sabon Shafin Daukar Ma'aikata 10,000A wani mataki na bunkasa rayuwar al’umma da ku...
29/04/2025

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kaddamar da Sabon Shafin Daukar Ma'aikata 10,000

A wani mataki na bunkasa rayuwar al’umma da kuma karfafa ma’aikata, Gwamnatin Jihar Bauchi ta kaddamar da wani sabon shafin yanar gizo na daukar ma’aikata, wanda ke dauke da sama da ayyuka 10,000 a sassa daban-daban na Ma’aikatun Gwamnati, Hukumoji da Sashen Gudanarwa (MDAs).

A wani mataki na bunkasa rayuwar al’umma da kuma karfafa ma’aikata, Gwamnatin Jihar Bauchi ta kaddamar da wani sabon shafin yanar gizo na daukar ma’aikata, wanda ke dauke da sama da ayyuka 10,000 a sassa daban-daban na Ma’aikatun Gwamnati, Hukumoji da Sashen Gudanarwa (MDAs).

Cibiyar Kiwo Za Ta Jawo Zuba Jari Daga Cikin Gida Da Waje: Gwamnan BauchiGwabnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ...
29/04/2025

Cibiyar Kiwo Za Ta Jawo Zuba Jari Daga Cikin Gida Da Waje: Gwamnan Bauchi

Gwabnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cikakken yakini cewa Cibiyar Kiwo da ake shirin kafa wa za ta jawo masu zuba jari daga cikin gida da na ƙasashen waje idan aka kammala ta.

Gwabnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cikakken yakini cewa Cibiyar Kiwo da ake shirin kafa wa za ta jawo masu zuba jari daga cikin gida da na ƙasashen waje idan aka kammala ta.

Gwamnatin Bauchi da UNICEF Sun Kaddamar da Yunkurin Rigakafin Polio ga Yara Miliyan 2.5Gwamnatin Jihar Bauchi, tare da h...
29/04/2025

Gwamnatin Bauchi da UNICEF Sun Kaddamar da Yunkurin Rigakafin Polio ga Yara Miliyan 2.5

Gwamnatin Jihar Bauchi, tare da hadin gwiwar UNICEF, ta kaddamar da wani babban yunkuri na rigakafin polio ga yara sama da miliyan 2.5, ciki har da wadanda ke cikin yankuna masu wuya da kuma yankunan da ake fuskantar matsalolin tsaro.

Gwamnatin Jihar Bauchi, tare da hadin gwiwar UNICEF, ta kaddamar da wani babban yunkuri na rigakafin polio ga yara sama da miliyan 2.5, ciki har da wadanda ke cikin yankuna masu wuya da kuma yankunan da ake fuskantar matsalolin tsaro.

Boko Haram sun kashe mutane 7 a wajen jana’iza a BornoAkalla mutane bakwai (7) sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama...
29/04/2025

Boko Haram sun kashe mutane 7 a wajen jana’iza a Borno

Akalla mutane bakwai (7) sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama s**a jikkata sakamakon harin da ake zargin 'yan Boko Haram s**a kai wa al'umma a kauyen Kopl da ke karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

Akalla mutane bakwai (7) sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama s**a jikkata sakamakon harin da ake zargin 'yan Boko Haram s**a kai wa al'umma a kauyen Kopl da ke karamar hukumar Chibok, a jihar Borno.

Bam Ta Kashe Mutane 8 a BornoAkalla mutane takwas (8) sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku s**a jikkata, sakamakon fash...
29/04/2025

Bam Ta Kashe Mutane 8 a Borno

Akalla mutane takwas (8) sun rasa rayukansu, yayin da wasu uku s**a jikkata, sakamakon fashewar bama-bamai da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne s**a dasa a karamar hukumar Gamboru Ngala da ke jihar Borno.

https://fikrahtv.com.ng/bam-ta-kashe-mutane-8-a-borno

ISWAP Na Rike Da Kusan Kauyuka 80 a Jihohin Borno, Benue da Filato – Inji CRA #,Borno,  ,
28/04/2025

ISWAP Na Rike Da Kusan Kauyuka 80 a Jihohin Borno, Benue da Filato – Inji CRA

#,Borno, ,

Kungiyar Kare Haƙƙin Kiristoci a Najeriya (CRA) ta bayyana damuwa kan yadda kungiyar ‘yan ta'adda ta Islamic State’s West Africa Province (ISWAP) ke ci gaba da mamaye al’ummomi a Najeriya, inda ta ce kungiyar ta karbe iko da kusan kauyuka 80 a jihohin Borno, Benue da Filato.

16/04/2025

Allah ya kyauta!!!

Daga shafin: Haruna Kyawa

Don Allah mafarautan Arewa ku guji zuwa dazukan Kudu farauta. Ko a Arewa akwai dazukan da aka hana yin farauta a ciki sa...
13/04/2025

Don Allah mafarautan Arewa ku guji zuwa dazukan Kudu farauta. Ko a Arewa akwai dazukan da aka hana yin farauta a ciki saboda gwamnati ta keɓe su.

Har ila-yau akwai dazukan da saboda rashin tsaro mafarauta ba sa shiga. Tunda ba za ka je Sambisa farauta ba saboda yan BH, to ya kamata mu ƙaurace wa dajin Okumu da ke jihar Edo ko dan ‘yan bijilan.

Don Allah mu kiyaye.
Jafar jaafar

12/04/2025
Farfesa Pate Ya Cika Alƙawarin Da Ya Ɗauka Na Bawa Sakatariyar Jam'iyyar APC ta jihar Bauchi Kyauta Motoci.A cikin wata ...
12/04/2025

Farfesa Pate Ya Cika Alƙawarin Da Ya Ɗauka Na Bawa Sakatariyar Jam'iyyar APC ta jihar Bauchi Kyauta Motoci.

A cikin wata tawaga dake ƙarƙashin Alh. Bala Hadis a yau alhamis ta miƙa kyautar motocin da ministan lafiya da walwalar jama'a Farfesa Muhammad Ali Pate ya yiwa sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Bauchi.

Tawagar wacce ta sami rakiyar wasu cikin jigajigan tafiyar ministan ta miƙa motocin a hanun shugaban jam'iyyar APC na jihar Bauchi Hon. Muhammad Hassan Tilde.

An dai gabatar da jawabai a wajen wanda s**a ɗauki hankalin mahalartar taron, ciki har da jaddada yadda ministan ke cika alƙawari. Sannan shugaban jam'iyyar APC na jihar Bauchi ya yi godiya ya tabbata da cewa za ayi amfani da motocin yadda ya dace.

Sallah Janazah Babban Limamin mu Imam Dr. Idris  Bauchi (Rahimahullah)Karfe: 10:00amA Masallacin Eidi Games Village Bauc...
03/04/2025

Sallah Janazah Babban Limamin mu
Imam Dr. Idris Bauchi (Rahimahullah)
Karfe: 10:00am
A Masallacin Eidi Games Village Bauchi

Mutuwa Rigar kowa!!ALLAH Ya jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen TanshiALLAH ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakur...
03/04/2025

Mutuwa Rigar kowa!!

ALLAH Ya jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi

ALLAH ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakuransa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana ameen

Allahu Akbar shikenan fa!!

ALLAH Ya hadamu gidan Aljannah

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Fikrah TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Fikrah TV:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share