Jakadiya RTV

Jakadiya RTV Jakadiya Radio and Television is a registered internet radio and television with Corporate Affairs Commission.
(1)

Our aims is to ensure credibility of news circulating on our social network platform to help the fight against fake news.

28/10/2025

Siyasa!!!

28/10/2025

Bayanin Khadija Hamisu Wada wata mata da harshashen bindiga har guda uku ya same ta kuma take zargin jami'an tsaron C-Watch a unguwar Filin Samji.

Rahotanni sun ruwaito cewa shaidu sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan gayyato jami’an Hisba don sulhunta faɗa tsakanin wasu samari a yankin, amma lamarin ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan jami’an Hisba sun nemi taimakon jami’an C-Watch, wanda hakan ya janyo harbe-harben da dukan mutane.

Engr Suraj Yazid Abukur Ph.D A Matsayin Kwamishina: An Ɗora Kwarya a Gurbin TaJin labarin an tura sunan injiniya Suraj Y...
22/10/2025

Engr Suraj Yazid Abukur Ph.D A Matsayin Kwamishina: An Ɗora Kwarya a Gurbin Ta

Jin labarin an tura sunan injiniya Suraj Yazid Abukur a majalisar dokokin jihar Katsina domin a tantance shi a matsayin Kwamishina ya yi kowa daɗi kila sai dai...!

Hakika Malam Dikko Umar Raɗɗa ka ɗora ƙwarya a gurbin ta, domin ka zaɓo wanda yasan aiki ya iya aiki kuma zai taya ka aiki ba dare ba rana.

Lallai tarihi ba zai manta da irin gudunmawar da wannan matashi kuma jajirtaccen ɗan siyasa injiniya Suraj Yazid Ph.D ya bada wajen kafa gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa da ta shugaba Bola Ahmad Tinubu.

Sai yanzu al'ummar jihar Katsina za su ƙara yarda da gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa cewa mutum ne mai hangen nesa mai jin shawara mai san ya sauke nauyin da ya rataya akan da .

Babu shakka injiniya Surajo Yazid mutum jajirtacce wanda yasan abinda yake, wanda yake siyasa da gaske wanda ya yarda da duk abinda ya shafi mai girma gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD

Mu mutanen Rimi, mun yi imanin cewa wannan mataki da ka ɗauka zai canza siyasa ƙaramar hukumar Rimi da ta jihar Katsina baƙi ɗaya.

Mai girma gwamna, da muna daga cikin mutanen da ke yi maka kallon mutumin baya jin shawara, amma yanzu duk ka sallame mu, ka goge mana harda baƙi ɗaya, mun dawo wuri guda muna jiran sabon karatu a matsayinmu na ɗaliban siyasa.

Hakika zaɓen injiniya Suraj Yazid Abukur a matsayin Kwamishina zai taimaka wajen tabbatar da nasarar ka a ƙaramar hukumar Rimi da jihar Katsina, sannan muna baka tabbacin zai cigaba da fidda kai kunya kamar yadda ya saba.

Injiniya Suraj Yazid yana da kyakkyawar tarihi a siyasa zamantakewa da ilmi da sanin ya kamata, mutum kaifi ɗaya, duk abinda yasa gaba shi zai yi, wanda ya juyawa baya kuwa ya barshi har gaba da abada.

Kowa yasan irin ayyukan da ya gudanar KASROMA a dalilin da sunan ta ya yi shiru a Nijeriya ayyukan da ya shinfida za su cigaba da tuna shi a siyasa, yanzu kuma zai ɗora daga inda ya tsaya.

Muna da tabbacin cewa injiniya Suraj Yazid Abukur baya da zaɓin wurin da zai yi aiki duk inda aka kai shi, za a ga aiki da cikawa.

Mutane irin su injiniya Suraj Yazid tun farko gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta rasa amma yanzu ma ba a makara ba, domin muna tabbacin rawar da zai taka zata ƙara tabbatar da wanene injiniya Suraj Yazid Abukur a siyasance.

Mu mutanen ƙaramar hukumar Rimi mun yi amannar cewa ƙoƙarin da taimakon da injiniya Suraj Yazid yake yi kadai nasarar gwamnatin jihar Katsina ce, sai kuma gashi an kara masa dama.

20/10/2025

Ba zamu yi wa Mai wushirya da yar guda auren dole ba, sai mun tambaye su sun amince suna son juna - Inji Hukumar Hisbah

Cigiya!!!Iyayen wannn yaron mai suna Auwal na cigiyarsa.Sun zo daga karamar hukumar  Kankara zuwa unguwar Rahamawa cikin...
18/10/2025

Cigiya!!!

Iyayen wannn yaron mai suna Auwal na cigiyarsa.

Sun zo daga karamar hukumar Kankara zuwa unguwar Rahamawa cikin Katsina domin duba maras lafiya, suna shirin tafiya sai yaron ya fita daga gida ba a san inda ya nufa ba tun da safe.

A na rokon duk wanda ya ganshi da ya tuntubi iyayen shi ta wannan lambar da ke kasa.

09033416377

Allah ya sa a gan shi

Ambasadan zaman lafiya Sheikh  Ibrahim Yahaya Masussuka ya kai ziyarar girmamawa gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin ...
17/10/2025

Ambasadan zaman lafiya Sheikh Ibrahim Yahaya Masussuka ya kai ziyarar girmamawa gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin gaisuwa da sada zumunci tare da kara dabbaka zaman lafiya tsakanin al'umma.

14/10/2025

Kwamandan Hisbah na jihar Katsina Dr. Abu Ammar ya ce Abdullahi Umar Raɗɗa da ya bar addinin Musulunci ya koma Kirista ba ɗan Hisbah ba ne.

Tattaunawar Katsina Times

12/10/2025

Ziyarar Sheikh Masussuka a wajen taron maulidi

11/10/2025

Abinda yasa na ɓoye ina karatun lauya saboda kar mahassada su yi man Najeriya su ja a kada ni - Inji Dino Melaye.

11/10/2025

Matsalolin da ke faruwa a jami'ar Ummaru Musa ba wasu matsaloli ba ne na azo a gani - Kwamishinan ma'aikatar ilimi mai zurfi a Katsina, Hon. Isah Muhammad.

Ya ce Gwamnan Radda ya riga ya wadata makarantar da duk abinda take bukata.

Gayyatar Daurin Aure Ammadadin iyalan Alhaji Lawa Mai Iyali Dan Musa Dana Alhaji Hamza Yusuf Gafai ,na Farin Cikin Gayya...
10/10/2025

Gayyatar Daurin Aure

Ammadadin iyalan Alhaji Lawa Mai Iyali Dan Musa Dana Alhaji Hamza Yusuf Gafai ,na Farin Cikin Gayyatar Yan uwa da Abokan Arzikin Zuwa Wajan shedar Daurin auran dansu

Comrd Yusuf Lawal Mai iyali da amaryarshi Fatima Hamza Gafai

Wanda zaayi Ranar 11th October 2025 da misalin Karfe 12:00 Na ranar a Unguwar Gafai Babban Gida Opposite Wakilin Yamma Dake katsina ,Katsina state

08/10/2025

Kada Allah ya kawo ranar da za a ce sai na yi kwangila in ci abinci - Madugun adawa a jihar Katsina, Mustapha Inuwa

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jakadiya RTV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share

Jakadiya Radio and Television

Domin Samun Sahihan Labarai, da Shirye-shirye managarta.