
30/07/2025
Kudiri da hangen nesan Danfulani na cigaba da farfado da daraja da kimar hukumar NAIC, in ji kungiyar masu ruwa da tsaki kan noma
Wata kungiya mai suna Forum of Agricultural Stakeholders in Nigeria ta jinjina wa Dr. Yazid Shehu Umar Danfulani, Shugaban Hukumar Inshorar Harkokin Noma ta Nijeriya NAIC, bisa yadda ya dawo da kima da msrtabar hukumar.
Yayin wani taron manema labarai, Shugaban Kungiyar, Mr Olayinka Omolaye, ya bayyana shugabancin Dr. Danfulani a matsayin mai kawo sauyi kuma mai hangen nesa.
Ya ce hukumar NAIC, wadda a da ta sha fama da matsalolin karancin kudi da kayan aiki, a yanzu haka tana fuskantar wani cigaba na musamman karkashin jagorancin Danfulani.
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi zabin shugaban hukumar cikin hikima da ya nada Dr. Danfulani. Jagorancinsa mai cike da kwazo da jajircewa yana dawo da darajar hukumar NAIC,” in ji Omolaye.
A cewarsa, ma’aikatan hukumar NAIC da kansu sun tabbatar da canje-canje masu ma’ana da ake samu a cikin hukumar.
Kungiyar ta bayyana cewa gyare-gyaren da Danfulani ke aiwatarwa na kan tafarkin sake gina hukumar NAIC don ta zama wata muhimmiya a yaki da rashin abinci a kasa.
An bukaci manoma daga sassa daban-daban na Nijeriya da su goyi bayan hangen nesan Danfulani yayin da yake kokarin kafa sahihin yanayi mai dorewa da ke cike da sabbin dabarun inganta harkar noma.
Kungiyar ta kuma bayyana cikakken goyon bayanta ga sauye-sauyen da hukumar NAIC ke yi, tare da kira ga duk masu ruwa da tsaki a harkar noma da su mara wa hukumar baya.
Tare da Danfulani a matsayin shugaba, kungiyar ta bayyana tabbacin cewa NAIC za ta ba da gudunmuwa sosai wajen tabbatar da wadatar abinci a lungu da sako na Nijeriya.