26/03/2025
Eman Ahmed Abdul Aty mace mafi kiba a duniya
Yar Masar ce wacce ake ganin ita ce mace mafi kiba a duniya kuma mace ta biyu mafi nauyi a tarihi, bayan Carol Yager. An yi iƙirarin cewa nauyinta da farko ya kai kilogiram 500 (lb 1,100).
An haifi Abd El Aty a Masar kuma ta zauna a Alexandria. Iyalinta sun bayyana cewa tana da nauyin kilogiram 5 (11 lb) lokaci da aka haife ta. Ta yi fama da matsalar zazzabin thyroid kuma ta daina makaranta.
Abd El Aty ta rasu a ranar Litinin, 25 ga Satumba, 2017 da karfe 4:35 na yamma, kwanaki 16 bayan cikarta shekaru 37 da haihuwa, sakamakon cututtukan da s**a hada da zuciya da na koda, a Asibitin Burjeel, Abu Dhabi, UAE lokacin da aka kwantar da ita asibiti a watan Mayu na 2017.