Safar Hausa

Safar Hausa Gaskiyar Lamari

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaron Najeriy...
04/12/2025

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaron Najeriya.

Haihuwa ba kyauta bace a Asibitin Nassarawa: Inji Gwamnatin jihar Kano.Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar Kano, ta bayya...
02/12/2025

Haihuwa ba kyauta bace a Asibitin Nassarawa: Inji Gwamnatin jihar Kano.

Hukumar Kula da Asibitoci ta jihar Kano, ta bayyana cewar, Asibitin Koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase, wanda aka fi sani da Asibitin Nassarawa, yana karbar kudin haihuwa daga wajen marasa lafiya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar, Samira Suleiman ta fitar, ta ce sabanin wasu rahotanni dake yawo cewar, haihuwa kyauta ce a Asibitin, abin ba haka yake ba.

Samira Suleiman ta kuma jaddada kudirin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf wajen inganta fannin kiwon lafiya a fadin jihar Kano.

Yanzu yanzu: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaron ...
02/12/2025

Yanzu yanzu: Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon Ministan Tsaron Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasar, Bayo Onanuga ya fitar, ta ce Tinubu ya aike da sunan Christopher Musa ga Majalisar Dattijai domin tantance shi.

Christopher Musa dai haifaffan jihar Sokoto ne.

Kasashen Indonesia da Malaysia da Bangladesh da Brunei da Kuma India, sun sanar da ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 202...
29/03/2025

Kasashen Indonesia da Malaysia da Bangladesh da Brunei da Kuma India, sun sanar da ranar Litinin, 31 ga watan Maris, 2025 a matsayin ranar Idin Sallah Karama. Sak**akon rashin ganin jinjirin watan Shawwal da ba'a yi ba a Yau Asabar.

Yankarwa Ma'aikata Albashi: Gwamnan Kano ya dakatar da Mai rikon mukamin shugaban Ma'aikata.Gwamnan jihar Kano, Alh. Abb...
27/02/2025

Yankarwa Ma'aikata Albashi: Gwamnan Kano ya dakatar da Mai rikon mukamin shugaban Ma'aikata.

Gwamnan jihar Kano, Alh. Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Mai rikon mukamin shugaban Ma'aikata na jihar Salisu Mustapha nan take, biyo bayan zargin yankarwa ma'aikata albashi da kuma rashin biyan wasu Ma'aikatan albashin su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau Alhamis, ta ce Gwamnan ya kuma umarci Salisu Mustafa ya sauka daga mukamin sa na Babban Sakatare a ofishin shugaban Ma'aikatan, domin bayar da damar yin bincike yadda ya k**ata.

Sanarwar ta kara da cewar, domin tabbatar da aiyukan gwamnati basu tsaya ba, Gwamnan ya amince da nadin Malam Umar Muhammad Jalo, wanda Babban Sakatare ne a ofishin Sakataren Gwamnati, a matsayin mai rikon mukamin shugaban Ma'aikata, har zuwa lokacin da za'a kammala bincike.

Gwamna Abba Yusuf ya jaddada kudirin sa, na ganin an yaki cin hanci da rashawa, tare da gargadin cewar, duk wanda aka k**a da laifi, zai girbi abinda ya shuka.

A yau ne Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da kwamitin bincike karkashin jagorancin Abdulkadir Abdussalam, kan zargin zaftarewa ma'aikata albashi, wanda aka basu kwana 7 domin su mika rahoto.

An nada Salisu Mustapha a matsayin mai rikon mukamin shugaban Ma'aikatan ne, biyo bayan tafiya neman lafiya zuwa kasar Indiya, da shugaban Ma'aikatan, Abdullahi Musa yayi.

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila.Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta dakatar da Sanatan Kano ta kudu, S...
24/02/2025

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila.

Jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, ta dakatar da Sanatan Kano ta kudu, Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila daga cikin ta.

Shugaban Jam'iyyar a Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa ne ya bayyana hakan a yau Litinin, a yayin taron manema labarai daya gudanar.

Dungurawa ya kuma bayyana cewar an dakatar da 'Yan majalisun tarayya guda uku daga Jam'iyyar, sak**akon zagon kasa da suke aikatawa NNPP.

'Yan majalisun da dakatarwar ta shafa sun hadar da Aliyu Sani Madakin Gini mai wakiltar Dala, da Kabiru Alhassan Rurum dake wakiltar Kananan Hukumomin Rano da Kibiya da Bunkure, sai kuma Abdullahi Sani Rogo dake wakiltar Karaye da Rogo a majalisar tarayya.

Hashimu Dungurawa ya kara da cewar, Jam'iyyar ta kafa Kwamitin bincike akan Sanata Kawu Sumaila da sauran 'yan majalisar guda uku da aka dakatar.

Har ila yau ya ce, kofar Jam'iyyar a bude take ga 'yan majalisar, yana mai cewa idan s**a tuba s**a gane kuskuren su, Jam'iyyar za ta yafe musu.

“Shekarar mu 40 tare da Kwankwaso, bamu taba sa'insa ba, sai yanzu da na zama Gwamna kuma wasu suke son na butulce masa?...
07/11/2024

“Shekarar mu 40 tare da Kwankwaso, bamu taba sa'insa ba, sai yanzu da na zama Gwamna kuma wasu suke son na butulce masa? to ban samu irin wannan tarbiyyar a Gida ba"

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf

Yanzu-Yanzu: Mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aikin sa.Ngelale ya bayyan...
07/09/2024

Yanzu-Yanzu: Mai magana da yawun Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu, Ajuri Ngelale ya ajiye aikin sa.

Ngelale ya bayyana cewar ya ajiye aikin ne na wucin gadi domin yaje ya lura da rashin lafiyar iyalin sa, sai dai ya ce zai dawo aikin idan hali yayi.

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Safar Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Safar Hausa:

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share