25/11/2025
KIRA GA SHUGABAN KASA, JAGORORIN AREWA, DA SARAKUNAN GARGAJIYA – A KARE MUTUNCINMU
A cikin kwanakin nan, wani abin tada hankali yana yaduwa a kafafen sada zumunta—Netflix, TikTok, da sauran shafuka. Wani sabon fim daga Kudu ya bayyana a Netflix inda ake nuna ’yan ta’adda a matsayin Hausawa, har ma ana amfani da harshenmu wajen nuna miyagun halaye.
A lokaci guda kuma, wasu mutane daga Kudu a TikTok suna ɗaukar bidiyo suna cewa wai “’yan ta’adda Hausawa ne” sun tare su, suna yi musu dariya, suna kuma yi mana tozarci a gaban duniya. Wadannan bidiyoyi suna kara yaduwa sosai, suna ƙara ɗora wa Hausawa lakabin da bai dace ba.
Misalin Bidiyo na 1:
[https://vt.tiktok.com/ZSffkPkM5/]
Misalin Bidiyo na 2:
[https://vt.tiktok.com/ZSffkg7Ks/]
Wannan ba barkwanci bane.
Ba “content” bane.
Wannan cin mutunci ne ga kabila ɗaya gaba ɗaya, kuma barazana ce ga zaman lafiyar ƙasar nan.
Mai Girma Shugaban Kasar Nigeria, Gwamnonin Arewa, ’Yan Majalisar Dattijai da Ta Wakilai, da Sarakunanmu na Gargajiya:
Lokaci ya yi da za ku yi magana a kan wannan batu. Ba za mu yi shiru ba yayin da ake danganta mu da ta’addanci a fina-finan duniya da kuma bidiyoyin TikTok. Shiru a irin wannan lokacin yana nuna cewa mutuncinmu baya da mahimmanci a idon masu mulki.
Wannan abu ka iya tayar da rikici, ya jawo fushin matasa, ya sa su jin cewa ana tozarta su da kabilansu. Idan ba a dau mataki yanzu ba, Allah kaɗai yasan irin mummunan tasirin da hakan ka iya jawowa ga kasar nan da ma gwamnati kanta.
Muna kira da:
1. A fito da bayyana kin amincewa da irin wannan nuna wariya ga kabilar Arewa.
2. A tattauna da masu shirya fina-finai da masu dora bidiyo domin dakatar da irin wannan badakala.
3. A saka baki daga Ofishin Shugaban Kasa, a fadawa duniya cewa babu wata kabila a Nigeria da za a danganta da ta’addanci.
4. A gudanar da fadakarwa da wayar da kai domin tabbatar da hadin kan ’yan kasa.
Nigeria ta kowa ce.
Ba kabila daya za a yi wa lakabin ta’adda ba.
Ba harshenmu za a zubar wa da mutunci ba.
Ba yankinmu za a wulakanta don a samu kudi ko daukar hankali ba.
Muna goyon bayan zaman lafiya—amma zaman lafiya yana bukatar adalci, gaskiya, da jagoranci mai ƙarfi.