23/02/2025
Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasa (NASRDA) ta tabbatar cewa za a ga sabon jinjirin wata na farko a shekarar 2025 a Najeriya ranar 28 ga Fabrairu. A cewar sanarwar da Daraktan Sadarwa da Hulɗa da Jama'a na NASRDA ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa jinjirin zai bayyana ne da ƙarfe 1:45 na safe agogon Najeriya (WAT).
Wannan lokacin, da ake kira "Crescent Zero Hour," shi ne mafi ƙarancin lokacin da za a iya ganin jinjirin ƙarƙashin yanayi mafi kyau ta amfani da kayan hangen nesa kamar gilashin bincike ko na'urar hangen nesa. Duk da haka, ga waɗanda ba su da kayan binciken wata , za su iya ganin jinjirin da ido kawai da yamma ranar Juma'a, 28 ga Fabrairu, tsakanin ƙarfe 6:17 na yamma zuwa 7:35 na yamma a sassa daban-daban na ƙasar.
A Kachia, Jihar Kaduna, ana sa ran ganin jinjirin tsakanin ƙarfe 6:38 na yamma zuwa 7:12 na yamma. NASRDA ta ba da shawarar amfani da gilashin bincike ko na'urar hangen nesa idan ya zama dole, tare da tabbatar da cewa an zaɓi wurare masu faɗi ba tare da cikas ba a gabar yamma bayan faɗuwar rana. Hakanan, yanayi mai kyau na sararin samaniya yana da muhimmanci don ganin jinjirin yadda ya kamata.