31/08/2020
JARIDAR "MUSLIM NEWS NIGERIA" TA BAYYANA MINISTA DR PANTAMI A MATSAYIN GWARZON SHEKARA A SAHUN MINISTOCIN NIGERIA
Dr Isah Ali Ibrahim Pantami shine Ministan a cikin Ministocin shugaba Buhari da yake tafiya gurin aiki bisa ka'ida na karantarwan addinin Musulunci wanda ya zama abin kwatance, inji jaridar Muslim News Nigeria
Jaridar Muslim News Nigeria ta lura sosai tare da bin bahasin ayyukan majalisar zartarwa na tarayyar Nigeria wato Ministoci , inda daga bisani jaridar ta bayyana Maigirma Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani Dr Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin Minista Musulmi da yafi dukkan Ministocin shugaba Buhari aiki, kwazo, gaskiya da kuma jajircewa
Idan za'a tuna Dr Pantami tayi rantsuwar zama Minista a gwamnatin tarayyar Nigeria ranar 21-8-2019 a karon farko tare da sauran ministoci da shugaba Buhari ya zaba don su ja ragamar ma'aikatu, wa'adin mukaminsu na Minista zai kare a shekarar 2023 tare da wannan gwamnatin
Binciken jaridar Muslim News Nigeria ya gano wasu abubuwa game da Dr Isah Ali Ibrahim Pantami masu tarin yawa:
Dr Isah Ali Ibrahim Pantami kafin ya zama Minista a 2019 shine shugaban hukumar bunkasa fasahar sadarwan zamani na Nigeria ( NITDA), a yanzu hukumar ta NITDA tana karkashin kulawar ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani bisa jagorancin Minista Dr Isah Ali Ibrahim Pantami
Muslim News Nigeria ta gano cewa Dr Isah Ali Pantami Minista ne mai tsoron Allah wanda yake bin karantarwan addininsa wajen kokarin jaddada gaskiya da adalci wa kowa a ma'aikatar sadarwa, ya samu manyan nasarori a shekara daya kacal da yayi a mukamin Minista, wadannan nasarori da ya samu, ya samesu ne bayan tsaruka masu kyau da ya kawo akan yadda tattalin arzikin Nigeria zai habbaka, tare da magance manyan matsalolin da suke addabar ma'aikatar sadarwa fiye da karni guda wato sama da shekaru 10 da sula gabata
A shekara daya; Dr Pantami ya kawo sauyi mai ma'ana a ma'aikatar sadarwa kuma yana ta kokarin tabbatar da kudurorin da zaisa ma'aikatar ta tsayu da kafafunta domin tayi gogayya da sauran ma'aikatun sadarwa na kasashen duniya da s**a cigaba, kuma yana jagorancinsa ne bisa koyarwan addininsa da yayi umarni akan ayi gaskiya tare da yin adalci wa kowa, duk da kasancewarsa mai addini kuma Malamin addini bai taba nuna banbancin addini wa kowa ba a ma'aikatar sadarwa, abinda ya saka gabansa shine a yiwa kowa adalci musulmi da wanda ba musulmi ba, duka 'yan Nigeria ne suna da hakki bisa doka
Farfesa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami duk da kasancewarsa Minista wanda a kullun kowace rana sai ya fita aiki amma yana da lokaci na musamman da ya ware yake jan ragamar karantar da addinin Allah domin ya nunawa Musulmai da wanda ba Musulmai ba sahihiyar hanya ta samun tsira anan duniya da kuma lahira, jaridar Muslim News Nigeria ta bayyana cewa a lokacin Azumin watan Ramadan kullun sai Minista Dr Isah Ali Ibrahim Pantami ya gabatar da tafsirin Al-Qur'ani Maigirma a lokacin da akayi fama da yaduwar cutar Coronavirus (COVID-19), wanda yawanci darussa na addini da yake gabatarwa da Hausa yana yadawa a kafofinsa na sada zumunta
Ku tuna cewa wannan jarumin Minista mai tsananin rikonsa da addinin Musulunci sai daya zama mutum cikin mutane 5 a Nigeria da s**a fi kowa sanuwa a kafofin sada zumunta da na yada labarai a shekarar 2019, inda Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya zama na farko a cikin mutane 5, Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami baiyi kasa a gwiwa ba, ya cigaba da aiki tukuru wanda zuwa yanzu ya zarce kowa a sanuwa, ya sanu ya kuma samu lambar yabo da shaida a cikin Nigeria da wasu kasashen duniya
Wakilin jaridar Muslim News Nigeria Malam Rasheed Abubakar ya taya murna wa Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami bisa kokarin da yake yi, sannan ya shawarceshi da ya cigaba da kokari don tabbatar da shugabanci na gari a ma'aikatar sadarwa, Mallam Rasheed Abubakar yaci gaba da cewa duk da kokarin da makiya suke don ganin sunyi batanci wa Dr Pantami, hakan bai sanyaya gwiwarsa ba, ya tabbatarwa duniya cewa shi Musulmi ne na kwarai, kuma ya wanke Musulmi daga bakin fenti da makiya s**a yiwa Musulmai
Malam Rasheed Abubakar yayi kira ga sauran masu rike da madafun iko da suyi koyi da Dr Isah Ali Pantami, "..kamar yadda yake a cikin tsarin mu na Muslim News Nigeria, na yabon 'yan uwa Musulmai da s**a nuna jarunta da aiki tukuru bisa doron gaskiya da adalci, ya zama wajibi garemu muka zabi Maigirma Ministan sadarwa Dr Isah Ali Ibrahim Pantami a matsayin Ministan da yayi fice a cikin Ministocin Nigeria saboda aiki da kokarinsa a ma'aikatar sadarwa..", inji Malam Rasheed Abubakar
Yaci gaba da cewa; Ma'aikatar sadarwa da Dr Isah Ali Ibrahim Pantami yake jagoranta tana da matukar tasiri da muhimmanci da jan hankalin duniya zuwa matakin habbaka tattalin arzikin zamani a bangaren harkokin sadarwa na fasahar zamani da suke da matukar tasiri a wannan zamanin, Dr Pantami ya kawo baiwar ilmin harkokin sadarwa da Allah Ya masa yana shayar da al'ummah a zaman aji da kuma cibiyoyi na al'umma domin a samu kwarewa a ma'aikatar sadarwa, mutum ne mai saukin kai, ga kyautata mu'amala, yana da kula sosai gurin karban bayanai, sannan kullun yana cikin bincike da lalubo hanyar da za'a samu cigaba kamar yadda ake nunawa a kafofinsa na sada zumunta.., inji Malam Rasheed Abubakar
Yaci gaba da cewa; Ba kowani Ministan bane zai tsaya bata lokaci wajen mayar da amsar tambayoyin da ake masa a Twitter kamar Dr Isah Ali Ibrahim Pantami Ministan Sadarwa, zabarsa da akayi a matsayin gwarzo na wannan shekaran zai kara masa jajircewa wajen kyautata wa 'yan Nigeria a ma'aikatar sadarwa, ina tayashi murna, inji Malam Rasheed Abubakar mawallafin jaridar Muslim News Nigeria
Nan da wasu kwanaki kadan, jaridar Muslim News Nigeria zata wallafa muku manyan ayyuka da Dr Isah Ali Pantami yayi a ma'aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani a tsakanin shekara daya da yayi a mukamin Minista
Muna fatan Allah Ya masa jagoranci, Ya kara masa taimako da nasara da kuma hakuri Amin