21/06/2026
KASHE NI BA ZAI KAWO KARSHEN SHI’A BA, SAI DAI YA KARAWA KARBALA YAWAN SHAHIDAI
– Inji Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)
Na san bayan da s**a harbe mu, su kaimu nan su kaimu nan, har s**a kawo mu nan Abuja s**a kai mu asibitin jami’an tsaro. To sai s**a zozzo wajen su bakwai, kowanne ya zanzare ya zamge wuya, wai za su yi tambayoyi ne. To ba zan baku bayanin dukkan abin da ya faru ba, zan fada muku wani bangare ne na abin da nace musu.
Na ce musu, sojan da ya saka ni a mota yana ta zage-zage. Cikin abin da yace min, yau ka mutu. Sai nace masa ai kai ma za ka mutu. Sai ya yi shiru. Sai nace masa ko ba za ka mutu ba ne? Sai ya yi shiru. Sai na sake ce masa, ko ba za ka mutu bane? Sai yace, Shi’a ta kawo karshe. Ni ma sai na yi shiru. Da ya cigaba da zage-zage sai ban ce masa komai ba. Ban amsa masa cewarsa Shi’a ta kawo karshe ba, saboda na ga a lokacin shi ba yana da hankali bane, bai cancanci in ma yi magana da shi ba, tunda zage-zage yake yi.
Sai na ce ma su wadannan mutanen da s**a zo masu zanzaron nan, ku yanzu bari na fada muku, Da kashe wani mutum zai kawo karshen Shi’a, da wannan mutumin Imamu Husaini (AS) ne, wanda shi an ritsa da shi da iyalansa da sahabbansa ba su kai mutum 100 ba. Mahaya akalla dubu 30, akallan kaddarawa. Mahayi, in an ce maka rundunar mayaka, dama yana daukan akwai mahaya, akwai mayakan kafa, Faris shi ne mahayi, Rajil kuma mai yaki da kafa, to galiba idan ka ga mahaya to za ka samu Rajjal sun nunka su biyu ko uku ma. An fahimta ai. In ka samu runduna aka ce Faris dubu daya, to ka tabbata Rajjal ya kai dubu uku ko ma fiye, wato mayakan kafa.
To, abin da na fada musu, nace to akallan Taqadiri mahaya dubu 30, mafi yawan Taqadiri, da mahaya da mayakan kafa mutum dubu dari biyu, s**a far wa mutum dari daya, ba su kai ma dari daya ba, a falalen daji, s**a kashe su duk, s**a tsire kawukansu a masu. Da ainihin ana gamawa da Shi’a da karshen kenan. Amma wannan tambatsa shi ya yi, shi ne ma ya mai da Shi’ar ta kambama duk duniya.
Ina fada muku abin da na gaya wa wadannan ne, nace musu in abin ku kashe ni ne, to za ku kara wa Karbala yawan Shuhada ne, amma Shi’a karuwa ma za ta yi, don ba ni ne Shi’ar ba ballantana ku kashe ni ku ji tsit.
Su sai s**a yi shiru. Wai sun zo su yi tambayoyi ne. Nace yanzu a wannan hali, kuka tunanin za ku min tambaya? Sai na ji daya ya zunguri daya yana ce masa, ba wannan ne lokacin yi ba. To sai s**a tafi, tambayoyin da basu yi ba kenan. Sai bayan kamar shekara biyu s**a zo, s**a ji abin da s**a ji daga garemu. Wannan bazan muku bayanin dogon bayanin ba.
– Cikin Jawabin Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin ganawa da‘yan uwa kimanin 200 da gwamnatin Buhari ta tsare su lokacin Waki’ar Buhari 2015, a Abuja, ranar Lahadi 4/6/2023 (15/11/1444H)
– Sheikh Zakzaky's Library
6/Muharram/1448
21/June/2026