Arewa Web3 Labs

Arewa Web3 Labs AREWA WEB3 LABS
Empowering Arewa minds to learn, innovate, and build in Web3. Connecting crypto enthusiasts, creators, and innovators under one hub.

KWANKWASIYYA AMANA

A gaskiya wannan muhawara ta fara wuce iyaka.Idan muka kalli yadda ake tafiyar da ita yanzu, ta koma hayaniya da kai-kaw...
17/04/2026

A gaskiya wannan muhawara ta fara wuce iyaka.

Idan muka kalli yadda ake tafiyar da ita yanzu, ta koma hayaniya da kai-kawo maimakon anfanuwa ga al’umma. ya kamata ku tuna cewa mutane da yawa na kallonku a matsayin masu ilimi kuma shugabanni a wannan fanni namu na crypto musamman DEX.

Idan kun girma, ku nuna hakan a aikace ba sai komai ya zama abin gardama ba. Akwai bambancin ra’ayi, amma ba lallai bane ya zama hanyar rikici ko cin mutunci juna.

Mu daina mayar da hankali kan wanda ya yi daidai ko wanda ya yi kuskure, mu koma kan abin da zai amfani mutane: ilimi, gaskiya, da fahimta mai zurfi.

A irin wannan lokaci, mafi kyawun mataki shi ne a dakatar da wannan case cikin mutunci, abar hayaniyar haka.

Wani Malamina yace min✍️
Shiru da hikima sun fi hayaniya da gardama amfani.

Bissalam.

16/04/2026







🦅 Idan kana son samun aiki a Web3, ka fara da wannan 👇Yawancin mutane suna bina ta Dm suna cewa:“Bro ka taimaka min da j...
16/04/2026

🦅 Idan kana son samun aiki a Web3, ka fara da wannan 👇

Yawancin mutane suna bina ta Dm suna cewa:
“Bro ka taimaka min da job a Web3.”

Amma gaskiya daya ce kullum nake gaya musu 👇

Web3 ba ana baka aiki bane.
Ana ganin value dinka ne, a
nemeka🤔.

Idan kana son a nemeka fara da wadannan 👇

1️⃣ KA ZAMA MAI FAHIMTA, BA MAI BIN HYPE BA

Kada ka fara da:
“GM sir” a duk post.

Fara da:
• Karanta whitepaper
• Fahimci project tokenomics
• Fahimci problem da suke solving

Knowledge > Noise.

2️⃣ GINA PERSONAL BRAND DINKA

Kana son job?
To ka nuna kwarewarka a fili.

• Yi threads
• Yi analysis
• Yi breakdown
• Yi research

Ka bari timeline dinka ta zama CV naka.

3️⃣ ZABI SKILL DAYA KA KWARE

Web3 ba developers kadai bane suke cin moriyarta.

Akwai:
• Community management
• Content writing
• On‑chain analysis
• Moderation
• Graphics / Design
• Research

Ba sai ka iya komai ba.
Amma ka iya abu daya sosai.

4️⃣ KA SHIGA COMMUNITIES

Discord.
Telegram.
Twitter spaces.

Ka dinga bada value.
Ka daina neman a baka role.

Role zai nemeka idan ka nuna competence.

5️⃣ KA YI PROJECT NA KANKA

Ko da ba’a biyaka ba.

• Rubuta analysis
• Gina mini community
• Yi research reports

Experience > Certificate.

🎯 GASKIYA:

Web3 ba ana shiga da roko bane.
Ana shiga da proof of work ne.

Idan ka fara da wadannan, ba zaka nemi job ba, projects ne zasu fara tambayarka:

“Are you open to work?”

👇 Kana son na yi muku post akan wanne skill a Web3 dalla‑dalla?







Zasu raba $5K kuma har yanzu participants ɗin basu kai 3K ba watakila dan baiwa kasamu jari a wannan project ɗin. Kayi k...
14/02/2026

Zasu raba $5K kuma har yanzu participants ɗin basu kai 3K ba watakila dan baiwa kasamu jari a wannan project ɗin.

Kayi kokari kayi join, zaka yi connecting din X account dinka sai kaje kayi wasu task a telegram da X (twitter) shi kenan.

Sai kajira gobe zasu Lahadi zasu rufe campaign ɗin.

Karku manta da sanyi sanyin safiya ake dukan ƙarfe.

Link:👇👇👇

quests.claimr.io/royaltiz/royal…

14/02/2026

The_easiest_way_to_get_a_web3_jobs_20263_

14/02/2026

To: Sir, Naziru M. Ahmad Sarkin Waka��

Sir, for your kind information and consideration.

Akwai wani hazikin matashin mawaki M S Dan Gata Musty daga garin Wudil, ya fito da wata waka, wadda ya sadaukar domin Sarkin Waka, Naziru Ahmad.
Lallai wannan waka ta fito fess, an zuba ta da hikima, basira, da GASKIYA, waka ce da ke ɗauke da saƙo mai zurfi.

Ni kaina ba mawaki ba ne, amma a gaskiya ba zan iya boye abin da na ji ba. Wannan waka ta burge ni matuƙa, domin an yi ta ne cikin ladabi, girmamawa, da fahimtar martabar Sarkin Waka.

Yakamata a yaba wa wannan matashi, a kuma ƙarfafa ma shi gwiwa, domin irin wannan ƙoƙari shi ke ɗaga darajar waka da al’adarmu gaba ɗaya.

ina fatan za ka ga wannan bidiyo ka saurara, domin waka ce da aka yi maka da zuciya ɗaya, ba kwaikwayo ba.

Allah yakara basira, ya ƙara ɗaukaka, ya kuma buɗe wa wannan matashi ƙofofin alheri. �

Shawarwari Goma Ga Ƙaramin Crypto Trader1. Ka ririta capital ɗinka kamar jariri ko kwai✍️Capital a trading tamkar jariri...
13/02/2026

Shawarwari Goma Ga Ƙaramin Crypto Trader

1. Ka ririta capital ɗinka kamar jariri ko kwai✍️
Capital a trading tamkar jariri ne. Ana rainonsa a hankali a hankali da risk management, discipline, da haƙuri. Idan capital dinka ya ƙone, trading ɗinka dole ya tsaya. Don haka ka girmama shi kamar rayuwarka.

2. Ka guji overtrading da shiga kasuwa ba tsari✍️

Shiga trade ba tare da setup ba, ko bin motsin zuciya (FOMO), hanya ce mai saurin ƙona account. Ka san lokacin shiga trade, lokacin fita, da adadin risk din da zaka dauka kafin ka taɓa buy ko sell.

3. Ka san yadda za ka rarraba profit✍️

Idan ka samu riba:

Ka fitar da wani ɓangare (withdraw).

Ka ware na alheri da na bukatunka.

Ka bar mafi yawa a account domin ya girma. Wannan shi ne sirrin compounding a crypto.

4. Ka tsaya da ƙafarka kafin ka riƙa copying ko koyarwa✍️

Idan kai ba ka da consistency, kada ka ɗauki nauyin bada signal a groups ko koyar da mutane. Idan ka fadi, za ka ja mutane da yawa su fadi tare da kai. Ka fara gyara kanka tukuna.

5. Ka daidaita rayuwarka da yanayin kasuwa✍️

Idan kasuwa tana sideways ko drawdown, rayuwarka ma ta kasance a hankali. Kada ka gina rayuwa akan bull market kawai. Bear market shi ne lokacin gane trader na gaskiya.

6. Ka mayar da loss darasi, ba dalilin daina trading ba✍️

Loosing a crypto ba rashin basira ba ne (indai kana da ilimi a tafiyar). Yana nuna maka inda ka karya doka ne. Ka duba journal ɗinka, ka gyara kuskurenka, ka koma kasuwa da hankali.

7. Kada ka cinye profit gaba ɗaya✍️

Ka raba profit gida uku:

Reinvestment a account.

Personal use & helping others.

Reserve (stablecoins / cash). Lokacin da kasuwa ta yi muni, reserve ne ke kare ka daga liquidation da panic.

8. Ka guji gasa da whales✍️😂

Whales suna da capital masu nauyi. Idan ka shiga kasuwa kana so ka yi sauri kamar su, za ka ƙone yan dalolinka ne. Ka yi trading kamar ƙaramin yaro mai hankali, ba kamar babba marar tsoron loss ba.

9. Ka tafiyar da trading ɗinka da zamani✍️

Ka yi amfani da:

On-chain data

Market structure

Risk tools

Journal & review
Trader da bai sabunta iliminsa ba, kasuwa tana cin shi a hankali.

10. Ka gina kanka kafin ka shagaltu da hype da soyayya✍️

A farkon tafiyarka, ka rage:

Shiga hype coins

Bin influencers makafi

Damuwa da abin da wasu ke samu
Ka gina system, discipline, da patience. Idan ka tsaya da ƙafarka, kuɗi da nutsuwa za su zo da kansu.

✍️ Arewa Web3 Labs
Takuce
Code120226

26/10/2025

With Sunusi Danjuma Ali – I'm on a streak! I've been a top fan for 9 months in a row. 🎉

Address

Wudil

Telephone

+2348133686253

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Web3 Labs posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share