20/09/2026
DALILAI 10 DA YASA MATA S**A FI SON NAMIJIN DA BAYA SON SU:
Idan na fada muku gaskiyar yadda kwakwalwar mace take aiki, wasu zasu dauka tsana ce. Amma zahirin magana shi ne: Mata da yawa suna kyamatar namijin da yake durkusa musu da tsantsar kauna, su koma suna haukatar da kansu a kan wanda bai ma san da zamansu ba.
Ga dalilan da yasa hakan take faruwa:
1.
Kalubale: Mace ba ta son abin da yake zuwa mata da sauki. Namijin da baya nuna damuwa, yakan zama kamar wani babban kofi na trophy da take son lashewa don ta tabbatar da cewa kyanta yana aiki.
2.
Rashin Zakuwa: Namijin da yake nuna zakewa yana nuna rauni a idonsu. Amma wanda yake tafiyarsa yana nuna cewa rayuwarsa tana tafiya daidai koda babu ita, wannan rashin damuwar ita take tayar musu da hankali.
3.
Gasa a Tsakanin Mata: Idan mace ta ga baka damu da ita ba, lissafinta yana bata cewa akwai wasu matan da kake bawa kulawa. Wannan tunanin na gasa shi yake rura wutar son ta mallake ka.
4.
Kwarjini Da Jan Aji: Namijin da ya cika yi wa mace bayanin komai yana rasa kwarjininsa. Wanda yake yin shiru bai cika magana ba, shi ne yake sa ta raba dare tana tunanin waye shi a zahiri.
5.
Raunin Motsin Zuciya: Rayuwa da namijin da yake nuna kauna dari-bisa-dari tana basu gajiya saboda babu wani sabon abu. Suna son wanda zai sa su fargaba yau, gobe ya sa su dariya; wannan shi yake sa su ji suna raye.
5.
Karyar "Zan Iya Canza Shi": Wata irin dabi'a ce ta son nuna karfi. Mace takan so ta auri taurin kan namiji da nufin cewa ita kadai ce zata iya yin amfani da dabarunta wajen sassauta shi.
6.
Yawan Kulawa Yana Kawo Raini: Idan ka mayar da mace ita ce duniyarka ta hanyar yi mata bauta, zata fara kallonka a matsayin mara aikin yi. Amma wanda yake watsar da ita yana fuskantar abin gabansa, shi ne take kallo a matsayin namiji mai tsari.
7.
Kuskuren Fahimtar Karfi: Mata da yawa suna fassara nuna ko-in-kula a matsayin tsantsar karfin 'Da Namiji. Suna ganin wanda bai damu da zafin soyayya ba, shi zai fi basu kariya a rayuwa.