Karfin Jama’a Sabuwar Duniya

Karfin Jama’a Sabuwar Duniya Motivational speaker Student of Al-istiqama University Sumaila Kano State

17/09/2025

Duk wanda ka ji yana zagi hujja ce ta kare masa, duk wanda yasan me yake yi ba ya zagi. Ita gaskiya ɗaya ce daga kinta sai bata.

11/09/2025

FREE Nasiru Hassan Yelwa NOW!!!

11/09/2025

Innā lillāhi wa innā ilayhi rājiʿūn Yan bíndigà sun shiga karamar hukumar Raba a jihar Sokoto a cikin daren nan ku sa su a addu'a.

Me ya k**ata ɗan sanda ya yi idan Gwamna ya ba shi umarnin k**a wani a bisa zalunci?A takaice dai: Dan sandan ya ki aiwa...
09/09/2025

Me ya k**ata ɗan sanda ya yi idan Gwamna ya ba shi umarnin k**a wani a bisa zalunci?

A takaice dai: Dan sandan ya ki aiwatar da umarnin da ya sabawa doka, ya tsaya kan gaskiya, domin doka ta fi karfin kowa.

Sashe na 35(1) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (as amended) ya tabbatar da cewa kowa yana da ‘yancin ‘yanci (right to personal liberty), kuma ba za a iya k**a shi ko tsare shi ba sai bisa doka.

Sashe na 36(1) kuma ya ce kowa yana da hakkin samun shari’a adalci (fair hearing) a gaban kotu mai ikon sauraron karar sa.

Wannan yana nuna cewa:

Duk wani umurnin k**a mutum da zalunci ko ba tare da doka ba → bai da inganci.

Aikin ɗan sanda shi ne bin doka da kare jama’a, ba bin umarnin mutum ɗaya ko gwamna idan ya sabawa kundin tsarin mulki.

Don haka, abin da ya dace shi ne: ɗan sanda ya ki aiwatar da umarnin da ya sabawa doka, ya tsaya kan gaskiya, domin doka ta fi karfin kowa.
✊🏾Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

06/09/2025

Mu ‘Yan Gaskiya ba jam’iyya bane. Mu tsari ne na girgiza barayin da dole mu karya su, in sha Allahu.
✊🏾✊🏾✊🏾

✊🏾 SUN MAIDA NIGERIYA FILIN DAGGA! SUN MAIDA KASAR WAJE WURIN SHAKATAWA!Hakika, ba'a taba samun shugaban wata kasa da ya...
05/09/2025

✊🏾 SUN MAIDA NIGERIYA FILIN DAGGA! SUN MAIDA KASAR WAJE WURIN SHAKATAWA!

Hakika, ba'a taba samun shugaban wata kasa da ya taba zuwa Nigeria domin hutu ko shakatawa.

Amma shugabanninmu? Sai yawo suke yi k**ar wadanda s**a ci kafar kare! Da sunan hutu ko neman lafiya.

Nigeria ta cancanci zama developed country, saboda babu abinda muka rasa.

• Muna da albarkatun kasa
• Muna da injiniyoyi da mutane masu fasaha
• Muna da damar mallakar duk abinda kasashe suke tunkaho da shi, amma mun rasa shugabanni

Babu abinda s**a iya sai su ciwo bashi, da nufin aiki, karshe su karkatar da su a aljuhun su!

Zalūnci ne Shugaba ya tafi wata kasa neman lafiya yayin da yan kasa ke fama da rashin lafiya.

Zalūnci ne Shugaba ya tafi hutu, yayin da al'umma ke cikin tashin hankali.

Mutum ne yana da gida, sai ya koma gidan haya, har ya yiwa gidan fenti!!!
Anya mutumin nan yana da hankali kuwa?

Kamar yadda Dan Bello yace:
“Karfin kasar mu baya cikin hauka da shige-shige, yana cikin gaskiya da fasaha.

Sabuwar duniya ba za'a gina ta ba da bashi, da kuma kayan aro daga kasashen waje, amma da karfin mu'amala, ilimi, da fasahar cikin gida.”

Ya yawa duk wasu kwararru a duniya, k**a daga likitoci, injiniyoyi da sauransu zaka samu yan Nigeria ne, kawai matsalar daga shugabanni ne! Babu wanda bai son ya samar da cigaba a kasarsa.

YA KAMATA MU FARKA. HAR YANZU BA MU DA YANCI, SABODA ÂZZALUMAN SUN RIGA SUN SAIDA MU!

Ban ga dalilin da zai sa yan Nigeria su sake zaɓen Tinubus a 2027 ba!

✊🏾 Nigeria Muna Bukatar Canji, Amma Ba Irin Na APC Ba🔥
✊🏾 Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

03/09/2025

Kame-kamen da ake yi a Zariya yayi yawa. Na kula suna da wasu ‘yan siyasa masu zuciyar dabbobi. Idan muka tabbatar suna da hannu a k**a wannan matashi, to in sha Allah za su gani. FREE EL-HASSAN QAURAN-MATA NOW!!!

Matasa! Ku tuna: Azzalumai ba abinda s**a tsana irin Gaskiya. Su kan fi jin tsoron ta fiye da makami. Don haka ku rike g...
03/09/2025

Matasa! Ku tuna: Azzalumai ba abinda s**a tsana irin Gaskiya. Su kan fi jin tsoron ta fiye da makami. Don haka ku rike gaskiya a zuciyarku, ku fadi gaskiya a duk halin da kuka samu kan ku, ku tsaya akan gaskiya a dukkan aikinku.

✊🏾 Wannan shi ne ƙarfin ku.
✊🏾 Wannan shi ne makamin ku.

Duk wanda ya tsaya akan gaskiya, ya fi karfin rundunar azzalumai!
✊🏾 Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

A zamanin da kenan, kana cikin tafiya zaka iya yada zango ka gangara gefen hanya ka ci ka gyatse babu tsoro babu firgici...
02/09/2025

A zamanin da kenan, kana cikin tafiya zaka iya yada zango ka gangara gefen hanya ka ci ka gyatse babu tsoro babu firgici, amma yanzu hanyar ma tsoron binta ake yi.

Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya.

A gyara harshe don tsare mutunci, a gyara hali don samun ƙauna, a gyara zuciya don samun nutsuwa, a tsarkake niyya don i...
31/08/2025

A gyara harshe don tsare mutunci, a gyara hali don samun ƙauna, a gyara zuciya don samun nutsuwa, a tsarkake niyya don inganta aiki.
©ZancenHikima

30/08/2025

Mutanen da suke yi maka hassada lokacin da ka samu nasara, sune dai mutanen da suke yi maka dariya lokacin da kake fafutuka.

Nazari game da Mutane 30 da aka kashe suna Sallar Asuba a Gidan Mantau dake jihar Katsina!Gomna yace awa 15 before, an s...
29/08/2025

Nazari game da Mutane 30 da aka kashe suna Sallar Asuba a Gidan Mantau dake jihar Katsina!

Gomna yace awa 15 before, an san da harin, kuma an sanarwa jami'an tsaro.

Sannan intelligent unit sun tabbatar da tahowar su kasa da awa 3.

Gomna ya bayyana cewa, su aikinsu bawa Jami'an tsaro umarni ne, amma basu da hurumin tilasta musu wajen karɓar umarnin!!!

A iya tunanina tunda sun san da harín, kuma an hana Jami'an tsaro ɗaukan mataki, ai da sai su sanar da mutanen su gudu su tsiratar da rayukansu.

• Me yasa Gomnatin Katsina bata sanar da al'ummar Gidan Mantau za'a kawo musu harí ba?

• Me ya sa ba za su biya su diyyar sakacin rayukan yan uwansu da aka k@she ba?

• Dan Allah ina matsalar take???
✊🏾Karfin Jama'a Sabuwar Duniya

Address

Habuja Gorubobi
Wudil
5783

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2348108972352

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karfin Jama’a Sabuwar Duniya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Karfin Jama’a Sabuwar Duniya:

Share

Category