FBC

FBC Welcome to Fact Broadcasting Company's (FBC) page – We are "The Voice of the Voiceless"

In Pictures: How the Governor of Katsina State, Malam Dikko Umar Radda, renovated the Executive Council Chamber at the K...
13/05/2026

In Pictures: How the Governor of Katsina State, Malam Dikko Umar Radda, renovated the Executive Council Chamber at the Katsina State Government House, modernized it, and officially commissioned it today, Wednesday, 13th May, 2026.

What is your opinion on the renovation of the Executive Council Chamber?

Da Ɗumi-Ɗumi: An fara “toya wainar” siyasar Kaita da JibiaMasu amfani da kafafen sada zumunta a ƙananan hukumomin Kaita ...
11/05/2026

Da Ɗumi-Ɗumi: An fara “toya wainar” siyasar Kaita da Jibia

Masu amfani da kafafen sada zumunta a ƙananan hukumomin Kaita da Jibia na Jihar Katsina na ci gaba da bayyana ra’ayoyi da gudanar da muhawara bayan ɗan jam’iyyar adawa ta ADC, Hon. Musa Lawal, ya sayi fom domin shiga jerin masu neman takarar kujerar Majalisar Wakilan Najeriya ta mazaɓar a zaɓen 2027 mai zuwa.

ta ruwaito cewa, wannan mataki na Hon. Musa Lawal ya fara jan hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin, inda ake ci gaba da tattaunawa kan yadda fafatawar siyasar za ta kasance tsakanin jam’iyyun siyasa da masu neman takara.

Shin yaya kuke hasashen siyasar 2027 za ta kasance a yankin Kaita da Jibia na Jihar Katsina?

Gwamna Radda Ya Yi Bankwana da Maniyyata Aikin Hajji Mutane Sama Da Dubu Biyu Na Jihar KatsinaGwamnan Jihar Katsina, Dik...
10/05/2026

Gwamna Radda Ya Yi Bankwana da Maniyyata Aikin Hajji Mutane Sama Da Dubu Biyu Na Jihar Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi bankwana da maniyyata aikin Hajji kimanin mutane 2,035 daga jihar kafin tafiyarsu zuwa ƙasa mai tsarki domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Da yake jawabi yayin taron bankwana da aka gudanar a sansanin Alhazai (Hajj Camp) na Jihar Katsina, Gwamna Radda ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da gudanar da aikin Hajji cikin nasara da kwanciyar hankali ga dukkan maniyyatan jihar.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar wa maniyyatan kayan tallafin Sallah k**ar yadda aka saba yayin da suke ƙasa mai tsarki, tare da kira gare su da su kasance jakadu nagari na Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya a lokacin zamansu a Saudiyya.

Gwamnan ya kuma shawarci maniyyatan da su yi amfani da kuɗaɗen alawus ɗin tafiyarsu cikin hikima tare da dagewa wajen yi wa jihar da ƙasa addu’o’in zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa.

Gwamna Radda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin jami’ai 240 domin kula da gudanar da harkokin aikin Hajji cikin nasara. Jami’an sun haɗa da malaman addini, ma’aikatan lafiya, masu ɗaukar kaya, jami’an hukumar jin daɗin Alhazai da sauran wakilan gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin shugaban tawagar gwamnati- Amirul Hajj.

Haka kuma, Gwamnan ya umarci shugabannin tawagar da su sanya ido sosai kan yadda jami’an da aka tura aikin ke gudanar da ayyukansu tare da kai wa gwamnati rahoto kan yadda s**a gudanar da aikinsu.

Tun da farko, Amirul Hajj kuma shugaban tawagar jihar, Barrista Ahmed Usman El-Marzuk, ya gode wa gwamnatin jihar bisa amincewar da ta yi musu na jagorantar maniyyatan jihar zuwa ƙasa mai tsarki. Ya bayyana cewa an gudanar da tarurruka daban-daban domin wayar da kan jami’an aikin Hajji kan nauyin da ke kansu.

A nasa jawabin, Babban Daraktan Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina, Alhaji Yunusa Abdullahi Dank**a, ya yaba wa Gwamna Radda bisa ci gaba da ba da goyon baya dom

Gwamnan Jihar Katsina Ya Jagoranci Kaddamar da Sababbin Motocin Hukumar KASSAROTA.A Ranar Alhamis 7 ga watan Mayun 2026,...
08/05/2026

Gwamnan Jihar Katsina Ya Jagoranci Kaddamar da Sababbin Motocin Hukumar KASSAROTA.

A Ranar Alhamis 7 ga watan Mayun 2026, Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da sababbin motocin Hukumar KASSAROTA a gidan gwamnatin jihar Katsina, domin ƙara inganta ayyukan hukumar.

A cikin jawabin sa yayin ƙaddamarwar, gwamnan ya buƙaci jami’an hukumar ta KASSAROTA da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da kuma jajircewa wajen tabbatar da an yi amfani da motocin yadda ya dace domin amfanin al’umma.

Haka kuma, gwamnan ya jaddada muhimmancin kula da motocin ta hanyar yin gyare-gyare da kulawa akai-akai domin tabbatar da dorewar su da kuma ci gaba da anfani da su na tsawon lokaci.

Da yake nasa jawabin, Daraktan Hukumar ta KASSAROTA, Major Garba Yahya Rimi, ya bayyana jin daɗinsa tare da nuna godiya ga gwamnan jihar bisa wannan gagarumin tallafi da goyon baya da ya baiwa hukumar.

Ya ce a madadin hukumar baki ɗaya, suna kallon wannan a matsayin wata babbar nasara da ci gaba ga hukumar, wadda za ta ƙara musu ƙwarin guiwa wajen gudanar da ayyukansu yadda ya k**ata.

Major Garba Yahya Rimi ya kuma tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da aiki tuƙuru domin tabbatar da ingantaccen tsarin kula da zirga-zirga da kiyaye lafiyar masu amfani da hanya tare da bin dokoki da ƙa’idojin aiki domin cigaban jihar Katsina.

Former presidential candidate of the ADC party, Atiku Abubakar, met with other leaders of the ADC coalition at a major i...
02/04/2026

Former presidential candidate of the ADC party, Atiku Abubakar, met with other leaders of the ADC coalition at a major international press conference, which was led by the National Chairman, Senator David Mark.
At the event, he expressed concern that bias from the electoral commission is becoming a threat to democracy.
He emphasized that such attempts to suppress democracy will not last.
He further stated that any authoritarian rule, even if it manages to stand for a while, does not endure—it only lasts a short time before eventually collapsing

President Tinubu met with his Chadian counterpart, Mahamat Idriss Déby, at his residence in Abuja today, Thursday.
02/04/2026

President Tinubu met with his Chadian counterpart, Mahamat Idriss Déby, at his residence in Abuja today, Thursday.

Gwamnatin tarayya ta ce zata fara yin rijistar raba tallafin kudi na sama da naira biliyan daya ga masu kanana da matsak...
01/04/2026

Gwamnatin tarayya ta ce zata fara yin rijistar raba tallafin kudi na sama da naira biliyan daya ga masu kanana da matsakaitan sana'o'i, daga ranar 7 ga watan gobe.

Shin kuna ganin tallafin ze je ga waɗanda abin ya sha fa?

El-Rufai ya isa babbar kotun tarayya ta Kaduna domin ci gaba da shari’ar da ICPC ke yi da shi a safiyar yau Talata
31/03/2026

El-Rufai ya isa babbar kotun tarayya ta Kaduna domin ci gaba da shari’ar da ICPC ke yi da shi a safiyar yau Talata

Hon. Yusuf Sulaiman Jibia ya karbi ragamar k**a aiki daga tshowar kwamishinan Ilimin Firame da Sakandire Hajiya Zainab M...
30/10/2025

Hon. Yusuf Sulaiman Jibia ya karbi ragamar k**a aiki daga tshowar kwamishinan Ilimin Firame da Sakandire Hajiya Zainab Musa Musawa.

Ma’aikatar Ilimin Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta gudanar da bikin mika ragamar aiki tsakanin sabon kwamishina, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, da tsohuwar kwamishina, Hajiya Zainab Musa Musawa, a dakin taron ma’aikatar ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, 2025.

A jawabinsa, sabon kwamishinan, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya bayyana kudirinsa na yin aiki tukuru tare da hadin kan dukkan ma’aikatan ma’aikatar domin ciyar da harkar ilimi gaba. Ya kuma gode wa Gwamna Dikko Umar Radda bisa amincewa da ya nuna masa, tare da alkawarin mayar da hankali kan karfafa ilimin firamare, inganta jin dadin malamai, da kuma kyautata gine-ginen makarantu a fadin jihar.

Hon. Jibia ya bukaci Hajiya Zainab Musa Musawa da ta ci gaba da bayar da shawarwari da goyon baya domin dorewar nasarorin da aka cimma.

A nata bangaren, tsohuwar kwamishina Hajiya Zainab Musa Musawa, ta gode wa shugabanni da ma’aikatan ma’aikatar bisa hadin kai da goyon bayan da s**a nuna mata a lokacin aikinta. Ta bayyana wa’adinta a matsayin lokaci mai albarka wanda ya haifar da nasarori da dama, ciki har da sabunta manhajar karatu, gyaran makarantu, da horar da malamai. Hajiya Zainab ta yi addu’ar fatan alheri ga sabon kwamishinan tare da bayyana tabbacin cewa zai ci gaba da daga darajar ilimi a jihar Katsina.

Shi ma Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar Katsina (SUBEB), Dr. Kabir Magaji Gafia, ya yi maraba da sabon kwamishinan, inda ya bayyana kwarin gwiwa cewa kwarewarsa da jajircewarsa za su kawo sabuwar dama ga fannin ilimi. Ya tabbatar masa da cikakken goyon bayan hukumar wajen aiwatar da manufofi da za su inganta ilimi da tabbatar da samun damar koyo ga kowane yaro a jihar.

Shugaban Karamar Hukumar Jibia, Hon. Sirajo Ado, ya taya Hon. Yusuf Jibia murna bisa wannan sabon mukami, tare da yabawa Gwamna Radda bisa hangen nesansa na daga darajar Yusuf Jibia daga matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman zuwa kwamishina. Ya tabbatar da cewa babu shakka, harkar ilimi za ta samu gagarumar nasara a karkashin jagorancinsa.

Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin hukumomi, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, dangi, da magoya baya da s**a halarta domin taya sabon kwamishinan murna.

Address

Area (A) Last Road, Nyanay Abuja
Wuse
900001

Telephone

+2349128230649

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when FBC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to FBC:

Share