
07/09/2025
Allah Ubangiji Yajikan Alhaji Haruna Danja Miloniya Uban Maijidda. An yima Addini Hidima Malam. Ance Shine Ya Fara Gina Masallacin Jumma'a Na Izala a Garin Zaria. Bawan Allah
TUNAWA DA MARIGAYI ALHAJI HARUNA DANJA, YAU SHEKARU KUSAN 40 DA RASUWAR SA...
Muna tunawa da rayuwar Marigayi Alhaji Haruna Danja, wani gwarzo a cikin al’umma wanda rayuwarsa ta kasance cike da gaskiya, adalci, tausayi, sadaukarwa da kishin al’umma.
Alhaji Haruna Danja ya rayu ne cikin mutunci da kamun kai, ya kuma bayar da gudummawa mai tarin yawa wajen gina al’umma ta hanyoyi daban-daban Addini, Ilimi, da zamantakewa. Ya bar tarihin da ba za a taba mantawa da shi ba, kuma darussan rayuwarsa za su ci gaba da haskaka zukatan wadanda s**a san shi.
Muna roƙon Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta masa, ya saka masa da Aljannatul Firdausi, ya kuma ba iyalansa da duka 'yan uwa da abokan arziki haƙuri da juriya.
Allah ya jikansa da rahama. Ameen
Asalin Hoto A Comment Section 👇