YALWA NEWS HAUSA

YALWA NEWS HAUSA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from YALWA NEWS HAUSA, Media/News Company, Goron dutse yalwa, Yalwa.
(1)

Jaridar Yalwa news Hausa Jarida ce mai zaman kanta karkashin kamfanin YALWA NEWS HAUSA MULTIMEDIA AND COMMUNICATION SERVICE

Domin Isar muku da mahimmin sako ku Tuntubemu ta wannan number
07048886899

Ban Ga Laifin Ķiristoçìn Nijeriya Ba Don Sun Koka Cewa Ana Kaśhe Musù Mutanè Saboda Suna Kishin Na Su, Amma Manyan Arewa...
07/11/2025

Ban Ga Laifin Ķiristoçìn Nijeriya Ba Don Sun Koka Cewa Ana Kaśhe Musù Mutanè Saboda Suna Kishin Na Su, Amma Manyan Arewa Har Karyatawa Suke Idan Muka Fito Muka Ce Ana Kashè Mutanè, Nan Wani Malami Ma Ya Ce Ya Je Kebbi Ya Dawo Lafiya Bai Ga Matsalar Tsaro Ba, Cewar Sheik Murtala Assada

DA DUMI-DUMI: Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dr.Abdulmohsen Al-Qasim Ne Zai Jagoranci Gabatar Da Hudubar Juma...
07/11/2025

DA DUMI-DUMI: Fitaccen Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dr.
Abdulmohsen Al-Qasim Ne Zai Jagoranci Gabatar Da Hudubar Juma'a A Masallacin Harami Manzon Allah Da Ke Birnin Madinah Almunnaw Warah.

Allah Ya Kara Mana Son Manzon Allah.

DA DUMI-DUMI: Da sanyin safiyar nan zanga-zanga ta sake barkewa a Amurka, dubban mutane suke ta kiran da a sauke Donald ...
07/11/2025

DA DUMI-DUMI: Da sanyin safiyar nan zanga-zanga ta sake barkewa a Amurka, dubban mutane suke ta kiran da a sauke Donald Trump.

YANZU-YANZU: Koriya ta Arewa ta harba makami mai Linzamin da har Yanzu masana sun kasa tantance girmansa da nisansa.Kori...
07/11/2025

YANZU-YANZU: Koriya ta Arewa ta harba makami mai Linzamin da har Yanzu masana sun kasa tantance girmansa da nisansa.

Koriya ta Arewa ta harba wani makami mai linzami da ba a tantance ba: kamar yadda Rundunar Sojin Koriya ta Kudu ta bayyana.

Gwamnatin Japan ta ce ana kyautata zaton makamin da Koriya ta Arewa ta harba ya faɗi ne a tekun Yankunan.

Rundunar sojin Koriya ta Kudu ta bayyana cewa Koriya ta Arewa ta harba aƙalla wani makami mai linzami zuwa cikin ruwan gabashin ƙasarta.

Wannan lamari ya faru ne, biyo bayan rahoton da hukumar leƙen asirin Koriya ta Kudu ta bayar a ranar Laraba, inda ta ce Koriya ta Arewa ta kammala shiri don gwajin nukiliya na bakwai, kuma za ta iya gudanar da shi nan take idan shugaban ƙasar, Kim Jong-un, ya yanke shawara, a cewar rahoton kamfanin labaran Yonhap.

Kuyi following 👉 ATP WORLD don samun labarai masu Inganci

"Wai maye ma ɗan Trump ya ce zai kawo mana hari Najeriya? Mu fa dama a cikin hari muke rayuwa ta ko ina, ga Boko Haram, ...
07/11/2025

"Wai maye ma ɗan Trump ya ce zai kawo mana hari Najeriya? Mu fa dama a cikin hari muke rayuwa ta ko ina, ga Boko Haram, Kidnappers da kuma Lakurawa, kai ita kanta gwamnatin farmaki take kawo mana".

Sheikh Alƙali Abubakar Zariya, Malamin Addinin Musulunci.

07/11/2025

YANZU-YANZU A safiyar Juma'a
Kowa ya Fito mu gaida Shugaba Muhammadur Rasulullah ﷺ🥰

ALLAHU AKBAR :- Wannan shine Kabarin sayyida Nana Khadija matar manzon Allah ( S a w)  ta farkoAllah yakara mana soyayya...
06/11/2025

ALLAHU AKBAR :- Wannan shine Kabarin sayyida Nana Khadija matar manzon Allah ( S a w) ta farko

Allah yakara mana soyayyar manzon Allah (S)

Kungiyar Giginyu Ward Facebook Connect and Community Development ta shirya wani muhimmin shiri na rarraba kayan karatu g...
06/11/2025

Kungiyar Giginyu Ward Facebook Connect and Community Development ta shirya wani muhimmin shiri na rarraba kayan karatu ga ɗalibai a cikin Mazabar Giginyu.

Wannan shiri yana daga cikin manufofin kungiyar na tallafawa al’umma, musamman wajen inganta ilimi da ƙarfafa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi domin su samu damar ci gaba da karatunsu cikin kwanciyar hankali.

Wannan aiki na jin ƙai ya nuna yadda matasa ke amfani da kafafen sada zumunta don kawo canji mai kyau a cikin al’umma.

Shugaban kungiyar Ishaq Garba Kawo ya bayyana cewa, “Manufar mu ita ce mu taimaka wajen ganin yara da iyaye marasa galihu sun samu kayan karatu, domin ilimi shi ne ginshikin cigaban kowace al’umma.”

A karshe, kungiyar ta yi kira ga sauran jama’a da su mara mata baya wajen irin wannan aiki na alheri da ciyar da al’umma gaba.

Daga Comrd Yahya Garba Ado

JARUMTA: An hango Jagoran Shi'a na Najeriya Sheikh Zakzaky ya shimfiɗa tutar Amurka yana takawa.A cikin malaman Najeriya...
06/11/2025

JARUMTA: An hango Jagoran Shi'a na Najeriya Sheikh Zakzaky ya shimfiɗa tutar Amurka yana takawa.

A cikin malaman Najeriya bayan Sheikh Zakzaky wanne malami kuke ganin zai iya wannnan jarumatar???

“Alburusai da Bama-bamai basu san kabila ko addini” — Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima.Me zakuce? Leadership news
06/11/2025

“Alburusai da Bama-bamai basu san kabila ko addini” — Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima.

Me zakuce?

Leadership news

Da Dumi-Dumi:Wani babban jami’in kamfanin magunguna na kasar Amurka ya yanke jiki ya fadi yayin jawabin Shugaba Trump a ...
06/11/2025

Da Dumi-Dumi:

Wani babban jami’in kamfanin magunguna na kasar Amurka ya yanke jiki ya fadi yayin jawabin Shugaba Trump a Ofishin Oval, inda aka kori ’yan jarida daga dakin taron.

Me za ku ce?

YANZU-YANZU: Amurka ta yi Gwajin makami mai Linzami mai tafiya wata Nahiya.Karon farko bayan shafe shekaru 30, Amurka ta...
06/11/2025

YANZU-YANZU: Amurka ta yi Gwajin makami mai Linzami mai tafiya wata Nahiya.

Karon farko bayan shafe shekaru 30, Amurka ta gudanar da gwajin harba makamin roka mai linzami mai ƙetare duniya, bayan Sanarwar da Donald Trump yayi kan dawo da gwaje-gwajen makaman nukiliya.

Rahoton ya bayyana cewa an harba makamin roka mai suna Minuteman III A jihar California.

kamar yadda Lucas Tomlinson, ɗan jaridar Fox News, ya ruwaito bisa bayanin rundunar sojin saman Amurka.

HOTO📸. ATP Hausa

Address

Goron Dutse Yalwa
Yalwa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when YALWA NEWS HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to YALWA NEWS HAUSA:

Share