12/11/2025
Yadda Ministan FCT, Nyesom Wike, Ya Kira CDS Don Ya Umurci Sojan Da Ya Hana Shi Shiga cikin fili
Wani masani kan al’amuran siyasa da zamantakewa, Charles Ogbu, ya bayyana yadda Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya shiga cikin wani hali na kaskanci bayan rikicinsa da wani jami’in soja, Lt. AM Yerima, a Abuja.
A cewar Ogbu, “Cikin girman kai, Wike ya ce, ‘to bari in kira shugaban sojoji, Chief of Defence Staff (CDS), in umarce shi da ya ce wa wannan yaro ya matsa gefe.’ Sai ya kira CDS wanda shi ne babban kwamandan rundunonin sojoji, ya ba shi labarin abin da ke faruwa, sannan ya mika wayarsa ga jami’in soja Yerima, yana tsammanin zai ji irin kalmomin nan na ladabi kamar ‘barkanka da aiki ranka ya daɗe’ ko ‘mun tashi daga nan yanzu, ranka ya daɗe.’”
Amma sabanin haka, jami’in soja Yerima ya yi bayaninsa cikin natsuwa da mutunci ga CDS, wanda bayan sauraren bayanin, ya ki bayar da umarnin da Wike ke tsammani. Wannan lamari ya bar ministan cikin kunya, inda ya bar wurin a hankali cikin abin da wasu s**a kira “tafiyar kunya”.
Ogbu ya kara da cewa, “Ka ɗan yi tunani — mutum ya kira babban hafsan tsaro don ya kai kara kan soja, ya mika wayarsa ga sojan, sannan bayan tattaunawa, sai a ce ministan ne ya fice da kansa cikin kunya? Wannan ya nuna cewa, duk da hayaniyar Wike a kafafen labarai, ba shi da karfi kamar yadda yake tsammani. Kuma da yana da hikima, da ya zauna a ofishinsa, ya bi hanya ta ofis don warware rikicin, maimakon zuwa wurin da kansa da rundunar tsaro, wanda hakan ya iya jefa shi da wasu cikin hadari.”
A ƙarshe, mai sharhin ya tambaya cikin mamaki: “Shin Wike na tsammanin CDS zai karya doka ta runduna domin ya rushe umarnin tsohon hafsansa, don kawai a kwace filaye a sake rabawa ga abokansa da danginsa — ba don amfanin jama’a ba, amma don son kai?”
Tushen labari: Aster1zaman (socio-political analyst)