29/10/2025
Yadda zaka ragewa wayarka shan data
👇👇👇
1. Kashe Background Data
Wasu apps suna amfani da data ko da baka buɗe su ba.
Yadda ake yi:
🔧 Shiga Settings
🔍 Danna Network & Internet → Data usage
⚙️ Danna App data usage ka duba waɗanda ke cin data sosai
🚫 Kashe Background data a apps ɗin da ba ka yawan amfani da su
2. Yi Amfani da Lite Versions na Apps
Lite apps suna da sauƙin amfani kuma suna rage shan data.
Misalai:
Facebook → Facebook Lite
Messenger → Messenger Lite
TikTok → TikTok Lite
YouTube → YouTube Go (ko kashe autoplay)
3. Kashe Auto-Update na Apps
Play Store na iya sabunta apps da kansa – wannan yana shan data sosai.
Yadda ake yi:
🔧 Buɗe Play Store
☰ Danna icon na sama → Settings
⚙️ Danna Auto-update apps
✅ Zaɓi Don’t auto-update apps
4. Amfani da Data Saver
Data Saver yana hana apps cin data sai da izini.
Yadda ake yi:
🔧 Shiga Settings → Network & Internet
⚙️ Danna Data Saver
🔛 Kunna Data Saver
5. Kashe Auto-Download a WhatsApp & Social Media
WhatsApp, Telegram, da Facebook na sauke hotuna da bidiyo kai tsaye.
WhatsApp:
Buɗe WhatsApp → Settings
Danna Storage & Data
A When using mobile data, cire duk abubuwa
💡 Bonus:
🛑 Guji kallon Live ko streaming videos akai-akai da data.
📵 Idan baka amfani da data, kashe mobile data gaba ɗaya domin ajiye MB.