JMB Online TV

JMB Online TV JMB HAUSA na yaki da labaran boge kuma muna kokarin kawo muku sahihen labarai masu inganci. zaku iya tuntubar wannan Number dan karin bayani, 08103353719

’Yan fashi sun kai hari ɗakunan kwanan dalibai mata a Makarantar SPY dake Adamawa Tare Da sace wayoyiDaga: Dahiru B Sidd...
28/05/2026

’Yan fashi sun kai hari ɗakunan kwanan dalibai mata a Makarantar SPY dake Adamawa Tare Da sace wayoyi
Daga: Dahiru B Siddiki
Alhamis, 28/Mayu/2026 6:15 na yamma
Wasu ɓarayi dauke da bindigogi, wukake da adduna sun kutsa cikin ɗakin kwanan dalibai mata na harabar Numan ta Kwalejin Fasaha ta Jihar Adamawa, inda s**a kwace wayoyi 15 da sauran kayayyaki masu daraja daga hannun daliban.
Shaidu sun ce wasu dalibai da s**a yi ƙoƙarin hana ɓarayin sace wayoyinsu sun samu raunuka, inda har wata ta suma sak**akon firgici da tashin hankalin harin.
Jaridar DAILY POST ta tattaro da safiyar Alhamis cewa lamarin ya faru ne da sassafe ranar Laraba, 27 ga Mayu, yayin da Musulmi ke shirye-shiryen bikin Sallah.
Daliban da abin ya shafa, suna kuka da halin da s**a shiga, sun zargi hukumomin makarantar da sakaci da kuma rashin tsaro a harabar makarantar.
Harabar Numan ta Kwalejin Fasaha ta Jihar Adamawa ita ce ta biyu mafi girma bayan babbar harabar da ke cikin birnin Jimeta na Yola.
Jami’in hulɗa da jama’a na kwalejin, Mista Albert Matila, ya tabbatar da aukuwar lamarin a harabar Numan, yana mai cewa shugabannin makarantar za su ziyarci ɗakunan kwanan daliban mata da abin ya shafa domin tantance abin da ya faru

27/05/2026

Barka da babban salla zuwa ga al'umma musulmai duniya gada nan JMB Online TV

26/05/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Nuru Muhammed, Ammee Abdullahi, Tukur Muhammed

Wata babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, ya ...
13/05/2026

Wata babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da Akanta Janar na jihar Bauchi, Sirajo Muhammad Jaja, ya gabatar na neman izinin zuwa ƙasar Saudiyya aikin Hajji da duba lafiyarsa.

Mai shari’a O.A. Egwuatu ya yanke hukuncin ne bayan masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa akwai yiwuwar wanda ake tuhumar zai tsere, musamman ganin wasu da ake tuhuma tare da shi har yanzu ba a kamo su ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar EFCC na Tuhumar Jaja tare da Aliyu Abubakar, wani ɗan canji, kan zargin karkatar da kuɗaɗen Gwamnatin Jihar Bauchi da kuma wawure kuɗaɗe har Naira biliyan 1.6.

13/05/2026

Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Najeriya NHRC, ta bayyana damuwa kan yadda ake samun karuwar cin zarafin mata a Jihar Kaduna.

Hukumar ta ce kusan kashi 95 cikin 100 na korafe-korafen da ofishinta da ke Kaduna ke karɓa na da alaka da cin zarafi ko take hakkin mata.

NHRC ta jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, hukumomin tsaro da al’umma domin dakile matsalar tare da kare hakkin mata a fadin jihar.

Wata Babbar Kotun Tarayya ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, da laifuka 12 da s**a haɗa da zamba da ku...
07/05/2026

Wata Babbar Kotun Tarayya ta samu tsohon Ministan Wutar Lantarki, Sale Mamman, da laifuka 12 da s**a haɗa da zamba da kuma halasta kuɗaɗen haram da s**a kai kusan Naira biliyan 33.8.

Kotun ta bayyana cewa Hukumar EFCC ta gabatar da hujjoji da s**a nuna an karkatar da kuɗaɗen ayyukan wutar lantarki na Mambilla da Zungeru ba bisa ƙa’ida ba.

Haka kuma, an same shi da laifin amfani da kusan $655,700 wajen sayen gida a Abuja ta hanyar da ba ta dace ba.

Sai dai ba a samu tsohon ministan a kotu lokacin yanke hukunci ba, lamarin da ya sa aka dage bayyana hukuncin tare da neman sammacin k**a shi.

Rundunar sojin Najeriya a karkashin Operation Enduring Peace sun ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita, tare da kwato ...
27/04/2026

Rundunar sojin Najeriya a karkashin Operation Enduring Peace sun ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita, tare da kwato Naira miliyan 8 da iyalanta s**a biya a matsayin kudin fansa a jihar Filato.

Jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta ce bayan tattara bayanan sirri da kuma binciken wani da aka k**a, sojoji sun gano inda aka boye matar a dajin Padam da ke karamar hukumar Qua’an Pan, inda s**a kai farmaki s**a ceto

16/04/2026

Kamfanin MTN na Nigeria ya sanar da dakatar da bada bashin kuɗin kiran waya da data, wanda aka fi sani da "Xtratime" na wani ɗan lokaci.

Ga chikakken Rahoton daga nan JMB HAUSA

GWAMNATIN NAJERIYA TA CE FARASHIN FETUR DIN KASAR NA DA ARAHA IN AN KAWATANTA DA KETARE Gwamnatin tarayyar Najeriya ta c...
16/04/2026

GWAMNATIN NAJERIYA TA CE FARASHIN FETUR DIN KASAR NA DA ARAHA IN AN KAWATANTA DA KETARE



Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce duk yadda a ke kuka da tsadar farashin man fetur a cikin gida amma ya na da sauki ko araha in an kwatanta da na wasu kasashe.

Bayanai daga ofishin kula da tara haraji na nuna hatta Amurka ta fi Najeriya tsadar fetur da kashi 50% haka ma wasu kasashen na duniya.

Bayanan na nuna matsalar dama ta taso ne daga hare-haren Amurka da Isra’ila kan kasar Iran inda rufe mashigar ruwan teku ta Hormuz ta tada farashin.

Akalla dai bayanan na nuna don tace man a cikin gida wato fiye da kacokan dogara ga ketare ya taimaka wajen daidaita farashin da samun man.

Don haka kira na dawo da tallafi ba shi ne zai zama mafita ba don tsadar ruwan dare ne game duniya.

Hakika farashin wasu kayan masarufi sun tashi don nasaba da tsadar kudin sufuri. JMB HAUSA

Address

Yola Kohu

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JMB Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share